Daga Dayo Yussuf
Ali Khalid ba ya iya tuna adadin gawawwakin da ya binne, yawancinsu na mutanen da bai san sunansu ba, kuma ba ya iya tuna fuskokinsu. Amma dai har yanzu yana alhinin su.
Ali, wanda mazaunin Nairobi ne ya fada wa TRT Afrika cewa, "A Musulunci, idan mutum ya mutu, alhakin al'umma ne su gaggauta tabbatar da an masa sutura a mutunce."
"Yana da ban tsoro idan ka tuna cewa, ta yiwu akwai Musulmai cikin gawawwakin nan da ke ajiye a mutuware tsawon watanni, ga shi babu wanda zai musu wannan alfarmar."
Ali ya fita daban cikin al'ummar da bisa al'ada, suke ƙyamar magana kan mutuwa.
Yana aiki ne tare da masallacin Juma'a da ke kusa da shi a Nairobi, inda yake hada gwiwa da wasu mutane don samun bayanai game da gawawwakin Musulmai da ke ajiye a mutuwaren birnin.
Tun sanda ya fara wannan yunkuri, Ali ya ce sun binne mutane wadanda ba don wannan yunkuri ba, da ba su samu wannan sutura bayan mutuwa ba.
Mutuware ta cika makil
A watan Satumba, hukumar Birnin Nairobi City ta fitar da sanarwar neman mutane su zo su duba gawawwaki, don ganin ko akwai 'yan-uwansu da suka bace.
Sanarwar ta ce an tara gawawwaki 200 da babu masu su a mutuwaren gwamnati cikin wata daya kacal. Hakan ya sa ala dole hukumomi suke binne su, bayan wani lokaci.
A asibitin Kenyatta Hospital, wanda shi ne asibitin gwamnati mafi girma a kasar, an fitar da irin wannan sanarwar a watan da ya wuce, inda aka ba da wa'adin kwana bakwai bayan nan za a binne gawawwaki 233, da ke ajiye a mutuware, sama da watanni uku.
Ali ya ce, "Muna da jami'ai a asibitocin, har ma a mutuwaren. Idan aka samu Musulmin da ya mutu kuma babu dan-uwansu da ya zo karbar gawarsu, to su zo su same mu. Za mu taimaka".
"Muna kokarin gano 'yan-uwan mutum idan za mu iya. Idan abin ya ci tura, mukan yi aiki tare da masallacin Jamia Mosque Waqf don binne gawawwakin."
Takaitaccen tasiri
Duk da labarin kokarin Ali da sauran mutane yana kwantar da hankali, aikin nasu yana amfanar mutane ne 'yan kalilan cikin al'ummar gari.
Kasar Kenya tana da yawan Musulmai kasa da kashi 20%, kuma Ali ya ce yana yin jana'iza ne kadai ga gawawwakin Musulmai.
Rashin masaniyar kan yadda tsarin jana'izar wadanda ba Musulmai ba yake, da kuma tsoron fadawa rigimar shari'a, shi yake hana Ali taimakawa wajen kokarin yin jana'izar wasu gawawwakin.
Steven, wani Kirista mabiyin darikar Katolika, ya fada wa TRT Afrika cewa lamarin ya fi wuyar sha'ani ga Kiristoci.
Ya ce, "Abin shi ne, Kiristoci sun rabu zuwa darikoki daban-daban, kuma kowannensu yana da nasa tsarin na binne gawa."
"Haka nan, yawancin coci-coci suna da mambobi da suke biyan su kudi kafin yin bikin aure, da baftizma, da jana'iza. To, ta yaya coci zai karbi gawar da babu mai ita, ya mata sutura ya binne ta?"
Matsala mai maimaituwa
Cikin tsawon shekaru, gawawwakin da ba a gano masu su ba sun taru a mutuwaren gwamnati, har abin ya zamo matsala ga hukumomin.
A watan fabrairu, hukumar Birnin Nairobi ta samu izinin kotu don binne gawawwaki 250 da babu masu su. Yawancin asibitoci a fadin kasar suna ba da wa'adin mako guda kafin su binne gawawwakin da ke mutuwarensu.
Ali ya kara da cewa, "Wasu lokutan, muna gano dangi, amma sai ka ga ba su da wadatar da za su biya kudin asibiti, da na hidimar jana'iza. Mukan nemi tara kudin tallafi a wani lokacin ko dai ta soshiyal midiya, ko a masallaci".
Da yawa daga gawawwakin da ba a gano masu su ba, an buge su a titi ne, ko sun yi mutuwar kwatsam.
A cewar hukumar Birnin Nairobi, sauran abubuwan da ke sanadin mutuwar gwawwakin su ne kashe-kai, wutar lantarki, mutuwa a ruwa, da harbin bindiga.
Ali ya ce, "Salon rayuwa ya sauya, ta yadda mutane suna zama a birane ba tare da kulla zumunci da danginsu da ke karkara ba. Hakan ke sa idan abi ya faru da su, babu wanda yake iya sani".
Ali ya ce, "Dokar Lafiya ta Kasa ta ce binne tarin mutane a kabari daya, babu mutuntawa a cikinsa. Za ka tarar da gawar namiji an hada ta da ta mace, tamkar gumaguman itace. Wannan ba hanyar da ya dace a yi bankwana da mutum ba ce."
A yanzu, dai, da zarar kotunan sun amince da bukatun neman kawar da gawawwakin, hakan zai sanya adadin gawawwakin da za a binne a shekarar 2023 kadai ya kai 500.