Rahoton da WHO ta fitar ya ce babu bambanci tsakanin kasashe masu tasowa da kasashen da suka cigaba a yawan matsalar rashin haihuwa /PHOTO:Anadolu

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce mutum daya cikin duk mutum shida wato kimamin kashi 17.5 cikin baligai a duniya, suna fama da matsalar rashin haihuwa.

Wani rahoton da hukumar ta fitar ranar Talata ya ce alkaluma sun nuna akwai bukatar gaggawa ta samar wa wadanda suke fama da matsalar rashin haihuwa ingantaccen magani mai saukin farashi.

Sanarwar da WHO ta fitar ta ambato shugabanta Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, yana cewa “rahoton ya bayyana wata muhimmiyar gaskiya: cewa larurar rashin haihuwa ba ta nuna bambanci.”

Kashi 17.8 cikin 100 na mutanen da ke fama da larurar a kasashen da suka cigaba suke, yayin da kashi 16.6 cikin 100 na mutane da ke fama da larurar a kasashe masu tasowa suke, in ji rahoton.

Me ke janyo matsalar rashin haihuwa?

An bayyana matsalar rashin haihuwa a matsayin rashin iya daukar ciki idan mace da namiji suka yi shekara daya suna saduwa ba tare da amfani da abin hana daukar ciki ba.

“Ana raba rashin haihuwa na mata gida biyu. Akwai rashin haihuwa na macen da ba ta kai shekara 35 ba da na wadda ta kai shekara 35,” kamar yadda Dr Surayya Muhmammed Usman ta babban asibitin Gwarimpa da ke Abuja ta shaida wa TRT Afrika.

“Duk lokacin da aka ga yaro namiji ko yarinya ta mace tana da matsala a al’aura, a garzaya a je a ga likita."

Dr Sabo Ahmed na Kwalejin Lafiya a Jami’ar Jos a Nijeriya

Matsalolin da ka iya kawo rashin haihuwa a mata sun hada da matsalar da ke iya faruwa daga kwakwalwa da kiba da yawan motsa jiki da kuma kin cin abinci, in ji Dr Surayya.

Ta ce matar da ta kai shekara 35 kuma tana tare da mijinta amma ba ta iya daukar ciki ba cikin wata shida za a iya cewa tana da matsalar rashin haihuwa.

Amma ga macen da ba ta kai shekara 35 ba za a iya cewa tana da matsalar haihuwa in ta kai shekara daya ko biyu tana tare da mijinta amma ba ta dauki ciki ba, in ji likitar.

Dr Sabo Ahmed na Kwalejin Lafiya a Jami’ar Jos a Nijeriya ya ce rashin lafiya kamar hangum da kumburin ‘ya’yan maraina da kuma rashin jakar kwai a mace ka iya yin silar matsalar rashin haihuwa.

Likitan ya ce idan hangum ya sami yaro zai iya samun matsala a ‘yan maraina, lamarin da zai iya sa yaron ya samu matsalar haihuwa a lokacin da ya girma ya yi aure.

Masana sun ce ya kamata iyaye su  kai  'ya'yansu asibiti da zarar sun ga wata matsala tare da su don guje wa matsalar rashin haihuwa/ HOTO: Anadolu

Kulawar ba ta tsaya a kan kananan yara ba. Likitan ya ce ya kamata a ringa kula da al’aurar maza da mata ko sun girma, kuma a ga likita da zarar an ga wani abu da ba a saba gani ba don kauce wa matsalar rashin haihuwa nan gaba.

Cututtuka irin su ciwon suga da dabi'u irin su shan sigari da shan giya da yawa, da kuma damuwa mai yawa na cikin abubuwan da ke hana mace samun juna biyu, kamar yadda Dr Surayya ta shaida wa TRT Afrika.

Ta yaya za a iya kauce wa matsalar rashin haihuwa?

Masana sun ambaci wasu hanyoyin da ya kamata a bi wajen kauce wa matsalar suna cewa rigakafi ya fi magani.

“Duk lokacin da aka ga yaro namiji ko yarinya ta mace tana da matsala a al’aura, a garzaya a je a ga likita,” in ji Dr Sabo Ahmed.

Ga wadanda suke da matsalar rashin rashin haihuwa sakamakon irin salon rayuwarsu kuwa, to akwai mafita, in ji Dr Surayya.

Ta ce irin wadannnan suna bukatar sauya salon rayuwarsu ta hanyar barin shan sigari da giya da kara ko rage motsa jiki da kuma rage damuwa, suna iya taimaka wa irin wadannan mutanen su samu juna biyu.

Dr Ahmed Sabo ya kawo misalin macen da aka haifa ba tare da jakar kwai ba, yana mai cewa kawo yanzu babu fasahar dashen jakar kwai.

Kazalika ga namijin da 'yan marainansa suka lalace, ya ce za a dinga bin dabarun kwantar masa da hankali ta yadda zai yi rayuwarsu ba tare da matsala ba.

Wanda bai samu haihuwa ba zai iya daukar dan wani ya mayar da shi nasa ya kuma masa tarbiyya, likitan ya ba da shawara.

"Kashi 17.8 cikin 100 na mutanen da ke fama da larurar a kasashen da suka cigaba suke, yayin da kashi 16.6 cikin 100 na mutane da ke fama da larurar a kasashe masu tasowa suke."

Rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya WHO

“Yadda zai ji dadin rainon wanda ya haifa na jininsa, haka zai ji dadin rainon wani in dai ya hakura ya mayar da al’amarinsa ga Allah. Kuma zai sami lada cikakke,” Dr Ahmed ya kara da cewa.

Rahoton da hukumar WHO ta fitar ya ce matsalar rashin haihuwa ka iya janyo tashin hankali, abin kunya da kuma tsantsar rashin kudi.

Dr Fatima Yunusa Anga ta asibitin tarayya a Abujan Nijeriya ta ce yin aure su dan ja zai iya sa ma’aurata su dauki ciki da wuri sannan su kauce wa matsalar rashin haihuwa.

Masana sun ce ya kamata gwamnati da hukumomi na kasa da kasa su tallafa ta wajen rage tsadar maganin rashin haihuwa/ HOTO:Anadolu

Ta yaya za a sa samun maganin rashin haihuwa cikin farashi mai sauki?

Rahoton hukumar WHO din ya ce duk da girman matsalar, ba a bai wa fannin samar da maganin kudaden da suka dace.

Sai dai kuma hanyoyin samun maganin sun fi karfin mutane da yawa saboda rashin kudi da kunya da kuma karancin wuraren samar da maganin.

Dr Surayya ta ce za a iya samar da maganin matsalar cikin sauki idan kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa da ke bayar da taimako a fannin lafiya za su tallafa.

Wannan tallafin zai iya sa mutane su sami maganin cikin sauki, ba sai sun kai shekaru 50 suna kokarin tara kudi ba kafin su nemi magani, in ji Dr Surayya.

Dr Fatima ta ce idan gwamnati ta tallafa wa mutane ta hanyar inshorar lafiya, samun maganin rashin haihuwa zai yi wa ma’aurata sauki.

TRT Afrika