Ana sa rai sabon shugaban na WHO a yankin Afrika zai samar da tsare-tsaren da za su saka hukumomin lafiya a yankin su ƙara azama wajen biyan bukatun kiwon lafiyar ƙasashen yankin

Daga Sylvia Chebet

Ƙasashen Afrika guda huɗu - Nijar da Ruwanda, da Senegal da kuma Tanzania - kowacce tana da ɗan takara a fafitikar neman zama daraktan WHO na yankin Afirka na gaba, matsayin da ke tattare da manyan kalubalen magance ɗimbin matsalolin kiwon lafiyar al'ummar yankin.

Duk wanda aka zaɓa daga cikin huɗun a matsayin magajin wanda ke kai, Dr Matshidiso Moeti na Botswana, a babban taron Afrika jiƙo na 74th daga 26 zuwa 30 ga watan Agusta a Congo Brazzeville, zai gaji muƙamin mai cike da ƙalubale.

Afrika na fafitikar magance cututtuka mabanbanta masu buƙatar kulawar gaggawa na ban mamaki guda 100 kowace shekara a tsarin kiwon lafiya da ke buƙatar a inganta shi.

Maziko Matemba, wani mai fashin baƙi kan kiwon lafiya, ya lissafo sauyin yanayi, da rashin samun kula da lafiya yadda ya kamata, da raguwar bayar da tallafi da kuma ɓarkewar annobar cututtuka masu yaɗuwa da marasa yaɗuwa a matsayin ƙari a kan matsalolin da tuni suka yi wa tsarin kiwon lafiyar katutu.

Ƴan takara guda huɗun da ke neman muƙamin daraktan yankin - Dr Faustine Engelbert Ndugulile na Tanzania, da Dr Ibrahima Socé Fall na Senegal, da Dr Richard Mihigo daga Rwanda da kuma Dr Boureima Hama Sambo na Nijar - dukkansu gogaggun jami'an kiwon lafiya ne da suke sane da abin da suke fuskanta.

Ana sa rai sabon shugaban na WHO a yankin Afrika zai samar da tsare-tsaren da za su saka hukumomin lafiya a yankin su ƙara azama wajen biyan bukatun kiwon lafiyar ƙasashen yankin, sannan su zama suna alla-alla su yi aiki tare da gwamnatoci don samun Afrika mai ƙarin lafiya.

"Wannan muƙami ne da ke shata manufofin da ke kula da tsarin kiwon lafiya a Afrika," Matemba ya sheda wa TRT Afrika."

"Muna fata gwamnati da masu ruwa da tsaki za su zaɓi ɗantakara mafi cancanta - wanda ya fahimci tsare-tsaren kiwon lafiyar nahiyyar kuma zai iya aiki tare da gwamnatoci da kungiyoyi da mutane ɗaiɗaiku, da suka haɗa da kungiyoyin fararen hula da na masu zaman kansu, domin cim ma muradun kiwon lafiya na duniya zuwa shekarar 2030."

Kowanne daga cikin ƴantakarar ya gabatar da ƙudurori da ya yi alƙawarin za su inganta samar da kiwon lafiya ƙarƙashin tsarin WHO ta Afrika idan aka ba shi damar shugabantar hukumar.

A matsayinsa na likita, ɗansiyasa kuma ƙwararre a fannin shugabanci, Ndugulile ya yi imanin yana da duk wani abin da ake buƙata don riƙe muƙamin.

A matsayinsa na likita, ɗansiyasa kuma ƙwararre a fannin shugabanci, Ndugulile ya yi imanin yana da duk wani abin da ake buƙata don riƙe muƙamin.

Abu mafi muni shi ne, yayin da nahiyar ke fama da barazanar kiwon lafiyar jama'a, wasu sun fara ɗora alamar tambaya kan tasirin WHO.

"Akwai buƙatar biyan buƙatun ƙasashe mambobi. Akwai buƙatar mu rungumi shirin kiwon lafiya na Afrika a matakin duniya. Har wa yau, akwai buƙatar tattaunawa da shugabannin da masu tsara manufofi a nahiyar, da kuma mutanen da ke da faɗa a ji a harkar kasafin kuɗi da samar da kiwon lafiya," ya faɗa.

Nduguleli, Wanda ɗan'majalisar dokoki mai ci ne a ƙasarsa ta Tanzania, ya bayar da shawara kan a samar da abin da ya kira "shugabancin kiwon lafiya don kawo sauyi", kafin a ga tasirin hukumar WHO ta yankin Afirka a nahiyar.

Takwaransa na Senegal, Fall, ya fara cin karo da matsalar kiwon lafiya ta gaggawa a karo farko a shekarar 1996 lokacin da ɓarkewar cutar sanƙarau a yankin Sahel ya yi sanadiyar mutuwar mutane 30,000.

"Na tsinkayi cewa kiwon lafiyar jama'a na gaskiya bai tsaya kan magance cututtuka ba kaɗai. Fahimtar sabuban kiwon lafiya na zamantakewa da magance manya daga cikin su, yana taimaka wa rayuwar jama'a," ya bayyana.

Fall ya bayar da shawarar a samar da shirye shiryen bayar da tallafin kiwon lafiya da za su mayar da hankali kan jama'a kuma masu la'akari da al'adun jama'a kafin tsare-tsaren su yi tasiri

"Akwai buƙatar mu saka batun kiwon lafiya a tsakiyar matakan siyasa da ake ɗauka, kuma a tabbatar an samar da isassun kuɗaɗen aiwatar da su," a cewar Fall, Wanda ke riƙe da muƙamin daraktan WHO na Shirin Magance Cututtuka Da Ake Sako Sako Da Su Na Duniya.

Mihigo na Ruwanda, wanda ke hulɗa da WHO tsawon shekaru 18 kuma ya yi aiki a matsayin jami'i a shirin rigakafi, sannan ƙusa ne kuma babban darakta na rarraba allurar rigakafin COVID 19, ya ce, Afrika za ta cutu idan ta jira sai wasu ne za su kuɓutar da ita

"Hangena shi ne yankinmu ya iya saka batun kiwon lafiya a manyan tsare-tsarensa na cigaba," ya faɗa.

Sambo na Nijar, wanda ya yi aiki da WHO a muƙamai daban daban tun shekarar 2007, likita ne da ya mayar da hankali kan cututtuka marasa yaɗuwa.

"Duba da yadda na yi aiki a faɗin yankin Afrika, na fahimci sha'anin ɓarkewar cututtuka da kuma raunin da tsarin kiwon lafiya ke da shi. Akwai buƙatar mu yaƙi bambance bambance a tsarin kiwon lafiya," ya bayyana.

Tafiya ita ce alƙiblar

A wajen duka ƴantakarar su huɗun, muhimman abubuwan da suka yi tarayya a kai sun haɗa da gaggauta shirin samar da kiwon lafiya na duniya ta hanyar samar da ingantattun ayyukan asibitoci a matakin farko, da yawaita wayar da kan jama'a da kuma hana ɓullar cututtuka tare da bayar da kulawa ta musamman kan shirin kiwon lafiya na ko-ta-kwana.

Iya kula da cututtuka marasa yaɗuwa, da ƙara mayar da hankali kan cutar ƙwaƙwalwa da kuma wadata fannin lafiyar mata da kananan yara, su ma sun shiga jerin abubuwan da suka ce za su yi.

Yayin da kwamitin yankin Afrika na hukumar WHO ke hallara a Brazzaville nan gaba a wannan watan domin su zaɓi sabon shugaba, akwai wasu batutuwan bayan batun kawo sauyi.

Makomar kiwon lafiyar Afrika da kuma ingancin tsarin kiwon lafiyarta su ne kan gaba yayin da ƴantakara huɗun ke gabatar da ƙwarewarsu kan shugabancin nahiyar ta wannan ɓangaren mai cike da kalubale.

TRT Afrika