Tsawon shekaru Zimbabwe na fama da matsalar hasken lantarki. Hoto: TRT Afrika

Daga Takunda Mandura

Aluwaine Tanaka Manyonga ya karancin fannin lantarki ne saboda samun mafita ga irin rashin isasshiyar wutar lantarki da ƙasarsa ta Zimbabwe ke fuskanta.

"Kusan a shekarar 2019 baki ɗaya mukan shafe tsawon awa 19 a kullum ba mu da wuta," ya gaya wa TRT Afrika.

"A lokutan da nake yawan yin gwaje-gwajen yadda zan samo mafita ga batun lantarkin nan, amma sai yawan ɗauke wuta da ake yi ya dinga zame min cikas a lokutan karatuna.

Abin da ya faro a matsayin fasahar satar wutar lantarki, a yanzu yana ƙara ƙarfafa mafarkin ɗaruruwan yara a yankunan karkarar Zimbabwe, inda babu wutar lantarki kwata-kwata ko kuma ta lalace.

Ana kiran lantarkin da matashin injiniyan ya ƙirƙiro Chigubhu Lantern, wanda ke taimaka wa yara yan makaranta da ba su da wuta a gidajensu yin amfani da lantarkin nasa mai amfani da hasken rana don karatu da daddare.

Fitilar na da sauƙin amfani, kuma an ƙera ta da kayayyaki masu sauƙin haɗawa, sannan tana magance matsalar tara bolar robobi da kayan lantarki, tun da a kan yi amfani da su wajen sabunta su a ƙera fitilar.

Fitilar Manyonga na taimakawa yara 'yan makaranta da ba su da lantarki. Hoto: TRT Afrika

Bangarorin fasahar ƙere-ƙere ne ke jagorantar aikin Manyonga, inda yake amfani da hasken rana, da kuma aiki da bolar da ake iya sake sabunta ta don samar da tsaftataccen lantarki da ya yi tasiri sosai kan tsarin ilimin kasar ta kudancin Afirka.

Rabuwa da duhu

Bai fi kaso 50 na jama'ar Zimbabwe ne ke da hasken lantarki ba, kamar yadda Rahoton Makamashi na Bankin Duniya na 2021 ya bayyana.

Wadannan alkaluma masu bakanta rai na sake saka damuwa idan aka kalli kauyuka, inda kaso 30 ne kadai ke da hasken lantarki.

Daya daga cikin bangarorin da suka fi illatuwa da wannan matsala ta rashin lantarki ita ce sashen ilimi.

Manyonga, wanda ya kammala digiri na farko a Jami'ar Zimbabwe, ya samu tunani da fasahar samar da Fitilar Chigubhu a yayin da yake kokarin warware matsaloli biyu da abu daya.

Bayan gamsuwa da cewar wannan aiki zai yiwu kuma zai yi nasara, sai ya yi rajistar kamfaninsa da ake kira 'Zambezi Ark Technology' (Zar Tech) a watan Satumban 2022 don samun damar gabatar da wannan aiki ga jama'a.

Tuni Zar Tech ya fara karfafawa da tallafawa jama'ar kauyuka, tare da fitilar Manyonga mai saukin sarrafawa.

Wannan sauyi da aka samu mai dadin amfani da kyautata muhalli da ya maye gurbin lantarkin da aka saba da ita, na rage gurbata muhalli ta yadda yake sake sarrafa robobin da aka yi amfani da su, sannan yana aiki da kayan lantarki da aka zubar irin su kwayaye da batiran lithium.

Manyonga ya tunatar da cewa "A yayin da na ke tunani kera wannan fitila, na samu kalubale wajen wanne irin fanko zan yi amfani da shi.

Sai na gano zan iya amfani da kwalaben roba da aka zubar a shara. Fitilar da ke aiki da hasken rana na da kyawun gani kuma na aiki sosai yadda ake bukata.

Riba da yawa

Kayan da ake shiga da su Zimbabwe daga China ne kayan lantarki mafiya yawa a gidajen kasar.

Mafi yawan wadannan fitilu na LED da sauran kayan da ba su da inganci sosai, na saurin lalacewa, kuma ba sa aiki na tsawon lokaci da yawa, wanda hakan ke sanya taruwar kayan lantarki a shara da yawa.

Kaso 50 na jama'ar Zimbabwe ne ke da hasken lantarki. Hoto: TRT Afrika

Manyonga ya kuma ce "Baya ga bukatar samun sauyi ga lantarkin da aka saba da shi, daya daga abubuwan da suka sanya ni fara wannan aiki shi ne yadda ba mu da lantarki mai dadewa yana aiki.

Mafi yawancin ƙwayayen LED ba sa daukar tsawon lokaci suke mutuwa, wanda hakan ke kara yawan bolar kayan lantarki."

A duniya baki daya, sharar robobi na bayar da kalubale sosai. Zizmbabwe na tattara shara tan milyan 1.9 a kowacce shekara, wanda kaso 20 na sharar robobi ne.

Kwararru sun gamsu da cewa sake sabunta shara don samar da wasu kayayyakin amfanin yau da kulluma na da amfani sosai.

Zaburarwa da yabo

Babban abin da yake gamsar da Manyonga shi ne yadda abin da ya kirkira ke taimaka wa daliban karkara inda ba su da lantarki ko mafarkin ma su same ta.

Kayan da Manyonga ya samar sun kawo masa suna da samun kambi. Hoto: TRT Afrika

Daliban makarantu biyu a Chihota, garin su Manyonga, sun samu babban horo na samar da lantarki mai dore wa. Nan da karshen shekara, Zar Tech na fatan fadada tallafa wa dalibai 6,000.

Manyonga ya shaida wa TRT Afirka cewa "Ina tunanin za mu iya tallafawa dalibai da dama a yayin da aikinmu ke kara samun tallafi daga kungiyoyi daban-daban."

Wannan abu da Manyonga ya kirkira da zaburarwr zamantakewa sun sanya shi yin suna da kuma samun kambi da yawa da suka hada da na COP27 da aka gudanar a Masar a 2022, yana kokarin samarwa da kamfaninsa duk abin da yake so don ya habaka - yana koyarwa da samun tallafi.

TRT Afrika
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince