Drone na saukaka ayyukan noma a Nijeriya: Photo/Femi Adekoya

Daga Abdulwasiu Hassan

Dole ne manomi ya zama mai fatan samun alheri a ko yaushe, ko kuma ba zai kasnace a matsayin manomi ba, Will Rogers, jarumin Amurka kuma mai wasa ban dariya, ya yi wannan magana a dai-dai a lokacinda ya fadi hakan a lokacin da suke gwagwarmayar noma.

Tsawon lokaci bayan Rogers ya rasu a 1935, har ma a wasu yankuna na duniya a yau, noma na ci gaba da kasancewa wani kokari da ake yi da kayan aiki na gargajiya, inda ake dauka tsawon awanni ana ta abu guda.

Samson Ogbole, manomi dan Nijeriya da nasararsa a noman da ba a gonaki ba ya sanya shi yin shuhura, na da ra'ayin cewa babu wani lokaci da mutun zai sa ran amfana da nomansa, kar ma ku damu da kalubalen sauyin yanayi.

"Fesa maganin kwari da habakar amfani na iya zama babban aikin. Ka yi tunanin a ce kana noma eka 400 na kwakwar manja! Drone zai iya yi maka hakan... Wannan ba shi ne ma labari mai dadi ba," in ji matashin manomin a wani sako da ya fitar ta shafin Twitter.

"Labari mai dadi: fesa magani yadda gona ke bukata. Drone na tashi sama tare da fesa maganin a wajen da ya shanshana ya ji akwai shukar kwakwar manja. Sannan za ka iya feshi a kan bishiyu ma, babu wahala."

Fasahar feshin maganin da fasahar drone, na zuwa ne daga kamfanin 'Integrated Aerial Precision', kamfanin da a karon farko ya fara aikin da ya kira "babban sauyin ayyyukan noma da ke sauya ayyuka a Nijeriya da Afirka".

Wani bidiyo da Ogbole ya yada tare da sakonsa a shafin X ya nuna wasu mutane na zuba wani abu mai ruwa a cikin tankin drone, daga baya kuma jirgin mara matuki ya tashi sama tare da fara feshin maganin kwari da cututtukan tsirrai.

Duk da cewa ayyukan Ogbole noma ne a wajen da aka killace kuma ba tare da kasa ba, amma ya yi amanna cewar bidiyon ya zama misali mai kyau kan abinda aikin gona zai iya zama, musamman a yankin Afirka.

Sauyi daga jiya zuwa yau

A lokacin da mutane suke tunanin noma da kiwo a Afirka, abu na farko da suke fara hakaitowa shi ne yadda manoma ke kare wa da garma, adda da fatanya don gyara kasar noman.

Fasahar amfani da jirgin sama mara matuki na inganta ayyukan noma: Photo/Femi Adekoya

Madalla, labarin na sauya wa a yayin da matasa da ke da manufa ke amfani da fasahar zamani a ayyukan noma. Femi Adekoya, shugaban kamfanin 'Integrated Aerial Precision'. daya daga cikin su ne.

"Muna samarwa manoma kayan noma na zamani. Tare da amfani da drone da alkaluman bincike, muna taimaka wa manoma su yi nomansu cikin dabara da samun amfani mai yawa," ya shaida wa TRT Afirka.

"Mafitar kan kanta ba wani sabon abu ne, amma yadda muka yada wannan ilimi ya sha bam-bam. Mutum biyu za su dauki tsawon rana guda suna feshi a gonar shinkafa hekta daya, amma drone zai maka haka a mintuna 10 kawai."

Sannan manoma za su ribaci kashi 90 na ruwan da siuke amfani da shi wajen yin feshi da injin hannu. Baya ga feshi da ake yi, za kuma a iya amfani da drone wajen duba amfanin gona, da ma sauran ayyuka.

Fadada abokan hulda

Mafi yawan abokan huldar Adekoya manoma ne da ke noma don samun riba kuma suke da karsashin amfana da fasahar zamani don habaka amfanin da suke samu.

Amfani da fasahar zamani a Nijeriya ba wani ba shi da kalubale ba ne: Photo/Femi Adeyemi

"Manufarmu ita ce mu taimaka wa tsarin da zai habaka kasuwanci. Amma kuma muna son ma mu fara taimaka wa kananan manoma da irin tsarin da ya kamata su tafi a kai," ya fada wa TRT Afrika.

Daya daga cikin kalubalen fadada amfani da fasahar zamani shi ne rashin kayan ayyuka a kauyuka, kamar yadda aka gani ta hanyar yada bidiyon Adekoya a shafin X. Bidiyon ya nuna shi yana tafiya a hanya mara kyau a kan babur zuwa gona.

"Ka yi tunani a ce ka shafe awanni sama da biyar a kan babur a hanya mai kura, ramuka da isa zuwa kauye a jihar Oyo. Kuma hakan na zuwa ne bayan ka yi tafiya da mota zuwa yankin daga Legas. Yawanci ba na fadar halin da na ke shiga, amma wannan tsokaci ne kawai," ya rubuta a sakon da ya fitar.

Duk da wadannan kalubale, har yanzu Adekoya na ci gaba da kokarin cika burinsa na kai drone ga yankuna masu nisa da ke ciki da wajen Nijeriya. Yana horar d amutane da koya musu sarrafa shi.

Makarantar koyon wannan aiki da Adekoya ya kafa, na horar da mutane yadda ake amfani da drone a ayyukan noma.

"Wannan kokarina da manufar samarwa da rainon manoma da ke da ilimin fahasar zamani wajen noma. Mun fahimci cewa abinda amuke yi a fannin noma zai kawo babban juyin juya hali a fannin." in ji shi.

Manomin mai fika-fikai ya ce fasahar kere-kere ce makomar manoma mai kyau a nan gaba :Photo/Femi Adekoya

"Muna bukatar habaka ayyukanmu, kuma makarantar Koyar da Aikin ita ce jigon habaka ayyukan."

Kamar yadda yake game da duk wata fasaha ta zamani da ke kawo sauyi, wasu mutanen na ganin drone na kawo hatsari ga rayuwa idan suka shiga hannun manoma.

Adekoya ya shaida wa TRT Afirka cewa "Ba su gano cewa koyon sarrafa drone don feshi a gonaki zai taimaka musu wajen samun ayyukan da za su ba su kudade da yawa. Haka kuma, a wasu yankunan da ba su da manoman da yawa, drone na ada amfani sama da na feshi kawai."

TRT Afrika