Daga Firmain Eric Mbadinga
A kan hanyar komawa gida bayan aiki mai wahala, abin da ya fi damun Jean Ralph Odzaga shi ne yadda zai samu motar bas ɗin da za ta kai shi inda zai je da wuri.
Zafin rana da cunkoson jama'a da kuma hirar da fasinjoji ke yi haɗe da ƙarar ababen hawa a waje - duk ba za su kwatanta irin gajiyar da ta mamaye jikin wannan ma'aikacin gini a Libreville na Gabon ba.
Wannan rana ta bambanta da sauran ranaku, Jean ya gaji sosai kamar kullum, amma ganin wasu ma'aurata da suke koƙarin rarrashin 'ya'yansu biyu daga cikin uku a cikin bas ɗin.
Daga cikin yaran biyu, masu shekaru tsakanin ɗaya da rabi da kuma uku, Yayin da yaran biyu suka yi ta tsala ihu, Jean ya kafa idanunsa akan babbar yarinyar, 'yar kimanin shekaru biyar, wadda ta yi shiru fuskarta a takure.
Matar da ke zaune kusa da Jean, ita ma ta zuba wa yarinyar ido. Ta saki ajiyar zuciya kafin tace ''Yaro yaro ne! Muna cikin hatsari na sace wa yarinyar nan ƙuruciyarta."
Jean ya yi mamaki. "Na yi ƙarfin hali wajen tambayar matar me take nufi da hakan," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
"Ta yi tunanin cewa mai yiyuwa ne yarinyar ba ta samun kulawar da take bukata tun da iyayenta sun mayar da hankali wajen kulawa da jarirai biyu, watakila ma ba ta da mataimaka a gida. Ta yiwu ma ta kasance ita ce mai rainon 'yan'uwanta a irin wadannan yan shekaru."
''Ta kara da cewa akwai yiwuwar yarinyar ba ta samun kulawar da ta ke buƙata tun da iyayenta sun shiga wata sabgar ta kula da kannenta biyu, watakila babu wani taimako a gida. Ta yiwu ma ita take lura da 'yan'uwanta a 'yan shekarunta."
Daga nan sai ta sauƙa daga motar. A nan ne Jean ya fahimci abin da yawancin mutane suke sani amma suke daukar shi a matsayin abin da yake a zahiri wato ''Yarintar da aka sace wa ƙururciya.''
Yaduwar rashin lafiya
Tun daga zamanin iyaye da kakanni har ya zuwa yanzu, sannan daga Afirka zuwa sauran sassan duniya, lafiyar kwaƙwalwar yara da jikinsu batu ne da ke yawan janyo hankalan mutane.
Hikimar sanya yara masu shekaru 5 zuwa 16 su yi koyi aiki a wuraren koyon aikin hannu ya kasance abu da ake yawan yi har zuwa ƙarshen ƙarni na 18, musamman a ƙasashen Yamma.
Don tabbatar da cewa dukkan yara a duniya sun mori ƙuruciyarsu da samun ilimi da ingantacciyar kulawa, Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya kafa Asusun Tallafawa Ƙananan Yara na Majalisar (UNICEF) a shekara ta 1946.
Dakta Comlam Kouassi, masanin ilimin halayyar ɗan adam da ke aiki a birnin Cotonou na ƙasar Benin, ya bayyana batun sace ƙuruciyar yara a matsayin wata matsala ta al'umma wacce ke damatukar tasiri ga ci gaban kwakwalwar yaran a gaba idan suka girma.
''Lokacin da muke yara, lokaci ne na wasa, da kuma dogaro kan 'yayyenmu, kana akwai buƙatar mu soma horar da kanmu tare da shiri zuwa ga balaga. Amma a ƙasashen Afrika da dama, cikin har da Cotonou kasarmu ta Benin, yara da yawa suna aiki don su tallafa wa kansu," kamar yadda ya shaidawa TRT Afrika.
Wasu yaran ma sai sun yi aiki don sama wa iyayensu abin da za su ci, sun rasa abin da ya kamata su samu a kyauta.
''Ana tilasta musu yin rayuwa a matsayin waɗanda suka mallaki hankalinsu. Zan kira wannan al'amari matsayin 'tarbiyyar yara' duk da kasancewarsu yara, dolene su nemi abin da za su ci na yau da kullun, '' in ji Dokta Kouassi.
Tilasta balaga da wuri
Jack De Souza, ɗan ƙasar Togo, ɗan shekara 17, mai gyaran gashi ne a Lomé. Sana'a ce da Jack ke yi ba don yana so ba amma saboda yanayi.
iyayensa sun yi watsi da shi lokacin da yake ɗan shekara 12, Jack bai samu gata ko wata kulawa a yarintarsa ba. Ya girma ne a cibiyar kula da marayu ta Kpa Domeviwo, wacce ta tallafa masa tun yana ɗan karami.
''Duk da ya samu abin yi ta hanyar gyaran gashi, Jack ya ce yana jin radaɗin abubuwan da ke kan shi''
''A zahiri ni na ke biya wa kaina buƙatu a rayuwa biyo bayan watsi da iyayena suka yi da ni ba tare da wani dalili ba, dole na koyi sana'ar gyaran gashi don in tallafa wa kaina. Duk lokacin da ga yara kamar ni tare da iyayensu, nakan ji ba daɗi tare da rashin samun irin wanna dama, Amma haka rayuwa ta gaba,'' in ji shi.
Masana kimiyyar zamantakewa sun bayyana cewa wasu yara ba sa samun damar more kuruciyarsu saboda matsi na attalin arziki ko zamantakewa, kazalika rushewar tsarin iyali na ɗaya daga cikin abubuwan da ke haifar da wannan lamarin.
Ɓoyayyen sirri mai hatsari
A cewar kungiyar Consortium for Street Children, wata ƙungiyar ba da agaji ga yaran da aka yi watsi da su galibi suna fuskantar “cin zarafi, ta jiki, ko ta rai, tare da fadawa cikin damuwa ko kamuwa da cutar HIV/AIDS”.
Wasu suna fada wa wajen aikata laifuka, wasu kuma suna fuskantar ƙalubalen lafiyar kwakwalwa. Emmanuel Dogbevi daga Ghana bai ƙare a kan tituna kamar Jack daga Togo ba, amma ya fuskanci tsananin wahala a daidai lokacin ƙuruciyarsa bayan iyayensa sun rabu.
''Na girma ne a hannun mahaifiyata ita kadai. Mu tara ta haifa, kuma mun fuskanci wahalar rayuwa,” in ji shi.
“Bayan na gama makarantar firamare a 1983, ina ɗan shekara 15, sai aka ce na nemi aiki. Shi ya sa na ɗauki tsawon lokaci kafin na yi karatun boko. Na shiga jami'a ina da shekara 31," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Emmanuel, yanzu sanannen ɗan jarida ne mai bincike a Ghana, ya fita daban. Sace yarintar ko kuruciyar yara abu ne da ke da tasiri sosai wanda yawanci ba a iya mantawa da shi.
Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan 'yancin yara ta ba wa yara wasu muhimman abubuwa guda bakwai, kuma kusan kowace ƙasa ta amince da ita a shekara ta 2002.
Kasashen da suka sanya hannu dole ne su tabbatar da cewa kowane yaro ya samu kulawar iyali (iyayensa na asali ko akasin haka), da ilimi, da ƙauna, da matsuguni, da nishaɗi, da kuma kulawa.
Abin takaici, yawancin wannan har yanzu fata ne.
A cewar UNICEF, a yankunan kudu da hamadar sahara, karuwar mutane, da matsanancin talauci, da rashin isassun matakan kare al'umma, su ne manyan dalilan da suka sa yara kusan miliyan 16.6 ke shiga aikin dole a cikin shekaru hudu da suka wuce. Jimlarsu ta kai kusan miliyan 40 a yanzu.