Daga Coletta Wanjohi
Ministan Harkokin Wajen Djibouti, Mahmoud Ali Youssouf ya zama sabon shugaban Tarayyar Afirka, wanda lamari ne da ya haura na mika ragamar jagorancin nahiyar kawai.
An zabi Youssouf da kuri' 33 daga 49 da aka aka jefa a wajen taron AU na shekara a Addis Ababa a ranar 15 ga Fabrairu.
Toh, diflomasiyyar Djibouti ta yi nasara kan rugugin siyasar Kenya da burin Madagascar.
Tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga, babban mai kalubalantar Youssouf, ya karbi sakamakon zaben. Shugaban Kenya William Ruto da ya dinga yi wa Odinga kamfe ya sanar ta shafinsa na X cewa babba abin da ya fi muhimmanci shi ne manufar da ake da ita.
"Wannan zabe ba wai na daidaikun mutane ba ne ko kasashe; za mu ci gaba da aiki don samar da hadin kan Afirka mai karfin fada a ji a fagen kasa da kasam" in ji shi.
Dan takarar Madagascar, Richard Randriamandrato ya amince da zaben tun da fari inda ya ma janye takarar tasa saboda rashin samun isassun kuri'un zuwa zagaye na gaba..
"Cikin kankan da kai na amince da sakamakon zagaye na uku na zaben shugaban AUC, inda aka sallami takarata saboda rashin isassun kuri'u," ya fada ta shafinsa na X.
Underlying mechanics
Batutuwa da dama ne ke taka rawa a zaben Tarayyar Afirka. batun bambancin yare tsakanin masu magana da Turancin Ingilishi da Turancin Faransa na taka rawa sosai a siyasar nahiyar Afirka, shaida shi ne yadda aka ga sakamakon zaben AU na wannan karon.
Nahiyar na da kasashe 26 masu magana da Faransanci da 27 masu magana da Ingilishi, inda wasu kasashen suke magana da yaruka biyu, wasu shida kuma suke magana da yaren Portugal.
A matsayin wakilin kasar da ke magana da yaren Faransanci, Youssouf ya samu goyon baya daga kasashen da ke magana da yaren.
"Kwarewar Youssouf a diflomasiyya, sadarwa da yaruka da dama ne ya sanya shi zama wanda ya fi cancantar rike mukamin," Nuur Mohamud Sheekh, wani mai nazari kuma tsohon kakakin kungiyar IGAD, ya fada wa TRT Afrika.
Kwararru na cewa sauye-sauyen yanki da siyasa, ciki har da kusancin yankuna da siyasa da zaman takewa da tattalin arziki, duk suna taka rawa wajen zaben shugaban nahiyar.
"Kimar Djibouti a matsayin jigon zaman lafiya da dabarun diflomasiyyar yankin, ciki har da helkwatar IGAD, sun bayar da zaman ta gudunmowa ga sakamakon," in ji sheekh.
Bayyana manufa
'Yan takarar uku sun gabatar da manufofin a wajen muhawarar da aka yi a bainar jama'a karkashin AU a ranar 13 ga Disamban shekarar bara.
Youssouf ya yi amfani da kwarewarsa a fannin diflomasiyyarsa, kokarin ganin babban yanayi tare da hade su waje guda don cim ma burin nahiyar.
Ya ce "Ina mai alkawarin kare Afirka da wakilcinta a hukumomin kasa da kasa da kuma karfafa rawarta a kungiyoyin duniya. Dole ne Afirka ta zama mai fada a ji a tattaunawar samar da makoma ga duniya, yana mai habaka cigaban tattalin arzikinta."
A yayin da zaben ya karato, mambobi da dama sun gamsu da irin kanfe din da ya yi.
"Manufofin sabon shugaban na AU da ya bayyana a cikin kundin manufofinsa da ya gabatar a yayin gana wa da jama'a, ya zama babban abinda ya sanya ya samu tallafi," in ji sheekh.
Shekaru da kwarewa ma sun ba shi karin dama. A shekaru 60, Youssouf ya zama mafi abin zabi sama da Odinga mai shekaru 80.
"A matsayin daya daga Ministocin Harkokin Waje a Afirka mafi dadewa, an aminta da tsagwaron kwarewarsa. An kuma yi duba ga karancin shekaru, inda ake son matashi da zai kai Afirka tudun mun tsira." Sheekh ya fada wa TRT Afirka.
Me ke gaban Youssouf
A matsayin sabon shugaban AU, Youssouf na da aikin aiwatar da manufar cigaba ta 2063 da shugabannin kasashen Afirka suka samar, wadda ta bayyana manufofin bai daya na cigaban nahiyar, samar da arziki mai dorewa da zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci.
Wa'adin jagorancin Youssouf ya zo daidai da lokacin da ake fama da kalubalen tsaro a nahiyar, kamar yadda shugaban AU mai barin gado Moussa Faki Mahamat ya bayyana.
"Nahiyar na fama da tsananin tasirin rikice-rikice," in ji Mahamat.
"Yaduwar ta'addanci da tsaurin ra'ayi, ci gaba da rikicin Sudan, a Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, rarrabuwar kai a Libya.. rikice iri-iri a yankin Sahel, Gabar Gini, a Mozambique, a Kahon Afirka da yankin Babban Tafki, akwai jerin rikice-rikice a Afirka," Ya kara fada.
Baya ga matsalolin tsaro, dole ne Youssouf ya aiwatar da manufofin lafiya a Afirka da CDC ta samar, tare da tabbatar da inganci da karfin hukumar lafiya ta nahiyar.
Karin fifiko sun hada da samar da kudade a cikin gida ga Tarayyar Turai, saukaka basussuka, da kafa Hukumar Jinkai ta Afirka.
Sauyin da ake ci gaba da samu a yanayin siyasar duniya, ciki har da dawowar Donald Trump a matsayin Shugaban Kasar Amurka da karuwar adawa da Yammacin duniya a Afirka, wani batu ne na daban da sabon shugabancin Tarayyar Afirkan za su duba wajen gudanarwar.
Da yawa na kallon zabar Youssouf a matsayin lokaci mai muhimmanci a lokacin da suke ayyukan magance matsalolin nahiyar tare da karfafa rawar da take taka wa a siyasar duniya.
Hadin kwarewarsa a fannin diflomasiyya da matasantaka sun sanya zama mai iya kawo sauyi a tsarin shugabancin Afirka tare da salon hade kai da ciyar da Afirka gaba.