Daga Nuri Aden
A yayin da lokaci ke karato wa na zaben shugaban Hukumar Tarayyar Turai da za a yi a watan Fabrairu mai zuwa, Shugaba William Ruto na Kenya na d anasa dan takarar da yake tura wa gaba.
Tsawon watanni, Ruto na ta tuntubar masu ruwa da tsaki a nahiyar don tallata tsohon Firaminista Raila Amolo Oginga a matsayin wanda ya fi dace wa da kujerar, kuma zai iya kai Afirka tudun mun tsira ta yadda za a samu "#AfirkadaMukeSo".
Yunkurin diflomasiyya na shugaba Ruto da ya fara jim kadan bayan kaddamar da takarar Ruto a hukumance a watan Agustan bara a gaban shugabannin kasashen Gabashin Afirka, ya samu karbuwa sosai a 'yan makonnin nan.
Dantakara daga Kenya Raila Odinga na takara da Mahmoud Al Youssouf na Djibouti da Richard J. Randriamandrato na Magagascar.
Gangamin Ruto ga ma'aikacin gwamnatin da ya koma dan siyasa, a matsayin shugaba a nahiyar da ke son dunkulewa da samun cigaba.
Kokarin diflomasiyyar ya samu ganawar manyan mutane da dama wanda ke nufin fadadan dabarun Kenya na karfin siyasa da tattalin arziki a nahiyar.
Tara da takara mai zafi ta neman shugabancin na Tarayyar Afirka, kokarin Ruto ya kai shi ga manyan biranen kasashen Afirka da dama, yana neman goyon baya ga takarar Odinga, inda yake hada da kira ga hadin kai, goyon bayan junan yanki, da dabbaka manufofin cigaban Afirka.
"Wannan matsayi ba nasa ba ne, na dukkan nahiyarmu ne da kuma kasarmu. A yayin da kuke yi wa Kenya Addu'a, ku tuna da shugabanmu, yaya Raila Odinga don ya zama shugaban nahiyarmu, a lokacin da muke jiran sabon shugaban Hukumar AU, ta yadda idan muka samu damar, sai mu sake neman wasu kujerun," Ruto ya fada wa mahalarta coci a Nairobi a ranar Lahadin da ta gabata.
Nasarar diflomasiyya
Jerin sunayen manyan baki da aka rubuta za su halarci kaddamar da takarar Odinga ta neman shugabancin Hukumar Tarayyar Afirka a Fadar Shugaban Kasa da ke Nairobi ya sake tabbatar da matsayin Kenya na jagora a yankin.
Daga cikin manan bakin da suka halarci bikin akwai Shugaba Yoweri Kaguta Museveni na Uganda, takwararsa ta Tanzania Samia Saluhu Hassan, da Salva Kiir Mayardit na Sudan ta Kudu.
Halartar su taron ya aike da babban sako na nuna goyon baya ga takarar Odinga, inda suke kuma taimaka wa kawancen siyasar Kenya tare da dabbaka manufofin Gabashin Afirka na Hadewa da Aiki Tare.
A ziyara ta baya-bayan nan da ya kai Kenya, Shugaban Kasar Uganda Yoweri Museveni ya jaddada goyon bayansa ga Raila Odinga inda ya yi nuni ga cewa ciyar da nahiyar gaba na rataye a wuyayen gwamnatocin kasashen Afirka.
"Muna goyon bayan takarar Raila do zama shugaban Hukumar Tarayyar Afirka. Zai taimaka mana wajen farkar da jama'a, amma babbar damar na tattare da mu. Mu ne muke jagorantar wadannan kasashe.
"Mu ne za mu ce mun yi gaba, kuma mu yi din. Gare shi, zai iya magana ne, amma shugabannin gwamnatocin kasashen ne ke da damar a hannayensu." Museveni ya bayyana.
Wannan goyon baya na yanki ya sake samun daukaka da ganawa da shugabannin wajen Gabashin Afirka a yayin da Ruto ya dauki zagayen diflomasiyyarsa zuwa matakin kasa da kasa.
A watan Satumban 2024, wata guda bayan kaddamar da takarar Odinga, Ruto ya fara yawon zagaye a nahiyar da ma wajen ta.
A lokacin da ya je New York, ya gana da shugabannin Afirka da dama ciki har da Shugaba Bassirou Diomaye Faye na Senegal da Shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe, wadanda duk sun bayyana goyon bayansu ga Odinga don zama shugaban Hukumar Tarayyar Afirka.
Diflomasiyyar Ruto ta isa ga Shugaba Assimi Goita na Mali, wanda ya bi sahun jerin shugabannin Afirka da suka nuna goyon baya ga takarar Odinga.
A Malabo, Ruto ya gana da Mataimakin Shugaban Kasa Teodoro Nguema Obiang Mangue na Equitorial Guinea, kuma ya samu goyon baya ga Odinga.
Shugaba Umaro Sissoco Embalo na Guinea-Bissau, ma, ya sake jaddada goyon bayan kasarsa ga takarar Odinga, a lokacin da si da Ruto suka gana a Beijing.
A Addis Ababa, babban birnin Etiopia, Shugaban Kasar Kenya ya hadu da takwaransa na Saliyo, Julius Maada Bio.
Shugaba John Mahama na Ghana, abokin na tun tale-tale, ya zama mai neman a mara wa Kenya baya, a lokacin da ya ziyarci Nairobi a ranar 29 ga Disamban bara.
Daga baya Ruto ya halarci taron rantsar da Mahama a Accra, ghana, inda ya sake samun damar gana wa da shugabannin yankin.
Jerin sunayen shugabannin ya kunshi Shugaba Faure Gnassingbe na Togo da Joao Lourenco na Angola, wadanda dukkan su suka nuna goyon bayansu ga takarar da Kenya ke yi.
Fadada kudiri
Baya ga ganawa a hukumance, wannan kokari na diflomasiyya na bayyana faffadar manufar Kenya wajen fitar da makomar Afirka.
Babban jigon wannan manufa shi ne hadin kan Afirka da ke son dabbaka kasuwanci tsakanin kasashen Afirka, hadin kai a koyaushe, da hadin kan tattalin arziki mai kyau.
"Jinsina na tabbatar da Sauyin Tattalin Arziki; Karin Yawan kasuwanci Tsakanin Nahiyar; Daidaito da Adalci a tsakanin jinsi; habaka ayyukan noma da kiwo.
Magance Illolin Sauyin Yanayi; Inganta Matasa; Habaka Sadarwa da Kirkirarriyar Basira da Zaman Lafiya da Kwanciyar Hankali a nahiyar," Odinga ya bayyana wani sako da ya fitar ta shafin Facebook.
A kokarinta na tallatar takarar Odinga na neman shugabancin Hukumar Tarayyar Afirka, Kenya ta kara fadada tuntubar shugabanni, ciki har da Firaministan Mauritius Navinchandra Ramgoolam, Shugaban Kasar Algeria Abdulmajid Tebboune, da Shugaba Duma Boko na Bostwana.
Amintar da Algeria ta nuna a yayin taron G7 a garin Apulia na Italiya, na da muhimmanci, yana kuma bayyana karfin diflomasiyyar Kenya da kasashen Arewacin Afirka.
Tangarda a kan hanya
Ba dukkan taruka da ganawar da aka yi ne suka haifar da da mai ido ba wajen bayyana goyon baya ga Odinga.
A yayin da sakamakon diflomasiyyar Ruto ya yi armashi sosai ganawarsa da Shugaban Chadi Mahamat Idrss Deby Itno, Shugaban Zambia Hakainde Hichilema da Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud a wajen taron Afirka-China a Beijing, sun kammalu ba tare da bayyana goyon baya ba.
Duk da haka, wadannan misalai, tattaunawa game da hadin kan Afirka na ci gaba, inda dukkan bangarori suke bayyana muhimmancin aiki tare don habaka tattalin arziki da hadewar yankin, misali yarjejeniyar AfCTA.
Doguwar tafiya
A yayin da takarar Odinga ta shugabancin Hukumar Tarayyar Turai ke ci gaba da daukar hankali, ayyukan diflomasiyyar Kenya na kara yawa.
Alakar da Shugaba Ruto ya gina na iya sauya fasalin matsayin Kenya a matsayin babbar mai taka a Tarayyar Afirka, baya ga habaka takarar Odinga.
Kokarin Ruto na na bayyana yadda shugabancin Kenya a yau da gobe zai zama mai muhimmanci wajen gina gadoji tsakanin kasashen yankuna daban-daban.