Masana suna cewa Matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa na iya taɓarɓarewa ba tare da mutum ya farga ba.  / Hoto: Others      

Daga Firmain Eric Mbadinga

Dr Anna-Corinne Bissouma, likitar masu fama da taɓin hankali manya da yara mazauniyar Abidjan a Côte d'Ivoire, ta san yadda fama da cutar ƙwaƙwalwa take.

Ta kwashe tsawon shekaru tana yin magani, da bayar da shawara ga mutanen da ke fama da alamun da aka sani na takaici, da yanke zato da kuma fargaba.

"Fama da cutar ƙwaƙwalwa ba ciwon hauka ba ne. Sannan kuma ba batun gushewar zahirin al'amari ba ne." Dr Bissouma ta gaya wa TRT Afrika.

"Matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa wani abu ne mai kai komo. Batu ne game da yadda ka ke ji a cikin kanka domin ka iya fuskantar ƙalubalen rsyuwar yau da kullum, idan ka ji daidai a ƙwaƙwalwarka, za ka zama mai yin abu daidai, har ma jajircewa da ci gaba."

Ranar 10 ga watan Oktoban kowacce shekara ana bukin tunawa da Ranar Lafiyar Ƙwaƙwalwa Ta Duniya, wani tuni ne game da buƙatar ƙara ƙaimi wajen inganta al'amuran da ke alkinta lafiyar ƙwaƙwalwa.

Kafin a yi nasara a kan haka, masa tunanin ɗan adam da kuma likitoci kan tunanin ɗan adam sun yi nazari kuma suka koyar da batutuwa masu nasaba da matsalolin ƙwaƙwalwa da sauran al'amuran rayuwa da ke taka rawa a bangaren lafiyar ƙwaƙwalwa.

Waɗannan ƙwararrun sun bayar da shawarar ɗaukar wasu matakai domin kauce wa batutuwa masu alaƙa da lafiyar ƙwaƙwalwa.

Dawowa asali

Shawarar Dr Bissouma ta farko game da lafiyar ƙwaƙwalwa tana da alaƙa da tsaftataccen tsarin rayuwa.

"Lafiyayyen tsarin rayuwa ya ƙunshi cin abinci mai gina jiki da kuma tabbatar da isasshen barcin dare. Idan ka ci abinci mai gina jiki kuma ka samu wadataccen barci, ka inganta ƙwayoyin halittar garkuwar jikinka don su iya yin galaba kan cututtuka."

Ƙari kan waɗannan abubuwa na farko, waɗanda suka dogara da mutum, masana sun bayar da shawarar a ci abincin da bai ƙunshi mai da suga da gishiri mai yawa ba. Har wa yau, sun bayar da shawarar a nisanci kwankwaɗar barasa.

Idan so samu ne, Dr Bissouma ta bayar da shawarar a kaucewa shan kayan ruwa kamar shayi da kofi. Shan taba ma shi ma an gabatar da shi a matsayin abin da ke da hatsari ga lafiya.

"Raba kanka da rashin hutu, manta da damuwoyinka, akwai buƙatar ka yi wasan motsa jiki kuma ka motsa jiki. Takawa da ƙafa na aƙalla minti talatin a kullum kuma ka yi hakan aƙalla sau uku a mako yana da muhimmanci," ta gaya wa TRT Afrika.

"Za ka iya buga wasan motsa jiki na cikin rufaffen wuri ko na fili fallau a waje. Ko da lokacin da kake yin ayyukan gida kana amfani da ƙarfi sosai.

"Idan aka yi batun nishaɗi, akwai buƙatar ka yi ƙoƙarin ziyartar abokanai da ƙawaye, ka je inda za ka sha iska mai daɗi, kuma wani lokaci ka zauna a waje kawai. Ka ɗaga kai ka kalli samaniya, ja numfashi ka samu nutsuwa."

Abubuwan da suka saba haddasawa

Masana lafiyar ƙwaƙwalwa sun ce rashin kuɗi na ɗaya daga cikin abubuwan da suka saba jawo matsalar rashin barci Hoto: Getty Images

Abubuwa kamar matsin lambar aiki, da zafin kai lokacin cunkoson ababan hawa da yin mu'amala da uban gida mai wuyan sha'ani da ma yanayin rayuwa sanannun kalubalen rayuwar birni ne da suke bayar da gudummawa wajen taɓarɓarewar lafiyar ƙwaƙwalwa.

A irin wannan yanayin, samun abokan zama da iyali masu taimakawa waɗanda mutum ke zaune lafiya da su yana da muhimmanci wajen cim ma burin mutum.

"Ya kamata mu yi takatsatsan da mu'amala. Muguwar mu'amala tana hana mu cigaba. Hakan har wa yau na nufin yin aiki wajen sasanta saɓani. Idan ka samu saɓani da wani, dole ka yi ƙoƙarin magance shi.

"Ya kamata ka amince da ɗaya mutumin da kai kanka, tare da ajizancika, tasirinka da rauninka," Dr Bissoums ta bayyana.

Kuɗi na ɗaya daga cikin ɓangarorin rayuwa da suka fi muhimmanci da ya kamata mutane su iya sarrafa su. Ko shakka babu, an gano cewa rashin kuɗi ɗaya ne daga cikin abubuwan da aka sani suna haddasa cutar rashin barci.

Masana sun bayar da shawarar amfani da tunani mai kyau domin kaucewa faɗawa tarkon almubazzaranci, wanda wani lamari ne da ke haddasa tsananin damuwa.

"A nan ne mutum ya kwaɓi kansa da kansa ke taka muhimmiyar rawa," Dr Bissoums ta gaya wa TRT Afrika.

"Idan ana son kauce wa karɓar bashin da ya fi ƙarfin mutum, dole mutane kame kansu."

Alamun gargaɗi

Lafiyar ƙwaƙwalwa na iya taɓarɓarewa ba tare da mutum ya ankara ba - kusan kamar ɗan shisshigin da ya yi wa rayuwar mutum kutse.

"Matakin farko da za a ɗauka zai iya sosa rai. Mutum na iya fama da rashin walwala akai akai da ke haifar masa da tsoro, da zaƙuwa da kuma saurin fushi. Watakila a samu mutum ya dinga jin ƙasƙanci," Dr Bissoums ta yi bayani.

Duk waɗannan za su iya haifar da batutuwa na ɗabi'a. A wajen wasu, yi wa kai kallon ƙasƙanci na haifar da yanayi mara tabbas, rashin haƙuri da rashin sha'awar gudanar da al'amurran yau da kullum.

Irin waɗannan mutane za su iya faɗawa ta'amali da miyagun ƙwayoyi.

"A matakan ilimi da fahimta, za mu iya fama da wahalar mayar da hankali kan abu da wahalar yin tunani na hankali, da kuma samun matsala wajen yanke hukunci kan abu da yawan mantuwa," inji Dr Bissoums.

Matakai masu yawa

Kimiyyar lafiya na kallon batun lafiyar ƙwaƙwalwa ta fuskar abu mai kyau, ɗaukan mataki kan wani tunani da kuma yawan tunane tunane.

Mataki na biyu shi ne idan alamun mutum na fama da matsalar ƙwaƙwalwa suka bayyana.

Sanadin ka iya zama sauyin aiki, rabuwa haihuwa aure ko makoki. Haƙiƙa, wannan yanayi na buƙatar mutum ya saba da mawuyacin yanayi.

Sakamakon yawanci shi ne ɗaukan mataki kan mugun tunani saboda mayar da martani ne ga wata matsala wacce mutum ke fuskantar wahalar sabawa da ita.

Mataki na uku shi ne idan mutane suka rasa yawancin yadda za su ci gaba da daidaita tunaninsu.

Dr Anna-corinne Bissouma, wata likitar masu taɓin hankali,ta ce fama da damuwar tunani ba cutar ƙwaƙwalwa ba ce. /Hoto: Anna-Corinne Bissouma

Yayin da damuwar tunani ke ƙara taɓarɓarewa, sai su fara bayyana wasu alamu na taɓin hankali. Tsananin damuwa, da tunane tunane masu hargitsa ƙwaƙwalwa kamar jiye-jiye da gane-gane da kuma tsananin rashin hutu dukkansu manyan alamun shiga wannan yanayin ne.

"Wasu mutane ɗaiɗaiku na iya fama da matsalar cin abinci. Ɗabi'ar abu ya zama wa mutum jiki babu yadda zai yi da ita, na iya bayyana Ita ma,inji Dr Bissouma.

Neman taimako

Ba tare da la'akari ko yanayi na buƙatar martani ga mugun tunani ne ko ganowa ana fama da matsalar ƙwaƙwalwa ce ba, masana na bayar da shawarar a dinga neman shawarwarin likitan ƙwaƙwalwa domin kauce wa masomin taɓin hankali.

A cewar Hukumar Lafiya Ta Duniya, mutane masu fama da matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa suna mutuwa shekaru 20 tsakaninsu da sauran mutane.

Marigayi likitan Birtaniya Stephen Hawking ya yi fama da nau'in wata matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa na tsawon shekaru 55 daga cikin shekaru 76 da ya yi a rayuwarsa.

Yana da kowane irin uzuri na kallon rayuwarsa a matsayin mara amfani amma ya zaɓi ya tallata samun ƙarfin guiwa.

Idan aka kwatanta tsakanin yanke ƙauna da tsananin damuwa, Hawking ya bayar da shawara ga mutanen da ke fama da matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa.

"Munin matsalar rayuwa bai kai yadda ake bayyana shi ba. Ba ƙarshen rayuwa ba ne kamar yadda aka ɗauka a baya. Abubuwa za su iya sauyawa daga wancan yanayin wataƙila zuwa wani."

TRT Afrika