Kimanin mazauna ƙauyen Gaoui da ke fama da fari, a N'Djamena, Chadi su 400 yanzu suna noman kayan lambu a gona mai girman kadada-5 a ƙarkashin shirin nomar rani Hoto: WFP Daga Firmain Eric Mbadinga      

Daga Firmain Eric Mbadinga

Alhadj Dandal Abdoulaye and Haoua Mahamat a galibin lokaci suna karaya idan suka tuna lokacin da rani kan kwashe kafin ya wuce.

Rayuwa da gudanar da aikin noma a yankunan Chadi marasa dausayi sosai kusa da babban birnin N'Djamena, inda rijiyoyin ruwa suke da daraja tamkar rijiyoyin mai, suna jarabtar ruhin ɗan adam yadda abubuwa kaɗan ne kan yi hakan.

Yayin da ake yanke ƙauna kan ƙasar mai ƙarancin dausayi, manoma kamar Abdoulaye da Mahamat - dukkansu mazauna ƙauyen Gaoui - sun miƙa wuyansu ga yanayin.

Tasirin sauyin yanayi a ƴan shekarun da suka gabata musamman ya yi munin gaske, inda ruwan saman da jifa jifa ake yin shi yake matuƙare wahalar sauka.

A ɗaya daga cikin yankuna mafi zafi a duniya hakan za a iya cewa hakan mutuwar tsaye ce ga manoma.

Kamar a yawancin arewacin Chadi, noman kayan marmari da kayan lambu a Gaoui ana masa kallon harka mai kasada saboda taɓarɓarewar yanayin da ya siffantu da hauhawar zafi da ba a saba ganin irinsa ba.

A wajen galibin mazauna karkara a yankin, noma domin ci shi ne kaɗai lungun da in an bi yake ɓullewa.

Godiya ga Allah, wani aikin noman rani da ya mayar da hankali kan Gaoui, mai nisan kilomita 10 a arewa maso gabashin babban birnin N'Djamena, ya farfaɗo da shauƙi tsakanin manoma ta hanyar ceto gonakin masu girman kadada da yawa daga gusatowar hamada.

Babban maƙasudin kaddamar da aikin a wannan ƙauyen, wanda ya shahara kan gine ginensa na gargajiya da gina tukwanen ƙasa, shi ne don a tallafa kuma a horas da masu kasuwancin aikin gona kan hanyoyin da aka shata don samun galaba kan ƙalubalen sauyin yanayi.

An fara shirin ne tun farkon wannan shekarar, cikin Shirin Abinci Na Duniya Na Majalisar Ɗinkin Duniya tare da ƙawancen L’Agence Nationale de la Grande Muraille Verte du Tchad (ANGMV), domin a farfaɗo da aikin gona da tattalin arziƙin ƙauyen Gaoui.

Shirin sauya lamura

Mamane Salissou shugaban sashen ƙarfafa guiwa a Shirin Samar Da Abinci Na Chadi, ya yi imanin cewa shirin zai iya bunƙasa aikin gona a yankin har ta kai ana iya sayar da kayan gona.

 Bayan an tona rijiyoyin burtsatse masu aiki da hasken rana domin shirin nomar rani, mazauna Gaoui sun duƙufa noman kayan lambu iri iri. / Hoto: WFP

"Ta cikin wannan shirin karfafa guiwar, abokan hulɗar su biyun suna da hadafin tallafa wa mutane masu rauni don su dena dogaro da agajin jinƙai.

ANGMV na gudanar da aiki a faɗin Chadi da suka ƙunshi yankunan da ke ƙarƙashin shirin Great Green Wall a yankin Sahel, ya faɗa wa TRT Afrika.

"Bayan samar da wadataccen abinci, tunanin shi ne a taƙaita barazanar sauyin yanayi sannan a duƙufa wajen samar da tartiban matakai da suke da kyawawan tasiri kan muhalli. Aikin na Gaoui na nuni da burin da muke son cim ma."

Fili mai ƙarancin dausayi mai girman kadada biyar shi ne madubi ga abubuwan da za a aikata nan gaba.

Daga basaraken yankin zuwa makiyayi har kan manomin da ke dogaro da gonar kayan lambunsa ta karshe da ta tsira, zaƙuwar da mutanen yankin suka nuna wajen halartar shirin ƙwarewa wanda masana daga ma'aikatar aikin gona suka tsara, shi ya zama shimfiɗar shirin.

Babbar gajiya ta farko ita ce gina rijiyar burtsatse mai aiki da hasken rana domin ta taimaka dausayi ƙasar ya dawo.

"Mun katange wajen kafin mu tona rijiyar burtsatsen," Salissou ya sheda wa TRT Afrika.

An fara aiki a wajen a watan Fabrairu tare da ɗaukar nauyi da bayar da gudunmawar ƙwarewa daga WFP.

Baya ga horaswa da aka ba wasu da kuma sanin makamar aiki da aka koya wa sauran, har wa yau, an samar da ɗinbin kayayyakin aikin gona da danginsu.

Kyakkyawan zato ya bujuro

Bai ɗauki wani dogon lokaci ba da maciya gajiyar shirin su 400, da suka yi aiki ba ji ba gani, kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

"Sakamakon farkon sun zarce yadda aka yi tsammani. Godiya ga na'urorin da aka yi aikin nomar ranin da su, mun cike wurare masu ramuka sannan muka zama da su warare da suka dace da noma na tsawon lokaci.

Tuni manoman na noman kayan lambu iri iri da suka haɗa da tafarnuwa da karas da timatiri da kuma kokumba," Salissou ya bayyana.

Babban maƙasudin shi ne a tabbatar da wadatar abinci da abinci mai gina jiki. Da zarar an cim ma hakan,duk abin da ya yi saura daga kayan gonar ana kai shi kasuwar Gaoui domin sayarwa.

Abdoulaye na daga cikin manoma da suka rungumi shirin noma mai ɗorewa a yankin da ke fuskantar fari ba ƙaƙƙautawa.

Shirin Raya Ƙasashe Na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi hasashen cewa, idan ba a yi wani abu game da farin ba, zai iya yaɗuwa zuwa har kudancin ƙasar ta yankin Tsakiyar Afrika.

"Shirin na samar da gonaki da WFP ke ɗaukar nauyi ya kasance wata kyauta daga Allah," Abdoulaye ya shaida wa TRT Afrika.

An fara shirin ne a 2024 bayan da WFP ta ƙulla ƙawance da L’Agence Nationale de la Grande Muraille Verte du Tchad (ANGMV) su cike ramukan da ke gonaki a ƙauyen Gaoui mara dausayi sosai. Hoto: WFP

"Girbin farko ya nuna mana inda muka nufa. Yanzu mun san noman kayan lambu domin ci a gida da kuma sayarwa mai yiwuwa ne ko da kuwa a irin wannan lokaci na shekara."

Gwaji ga yanki

Ribar da aka ci a cinikin farko da aka yi a kakar ta bai wa ƙauyawan da suke cikin shirin su kafa wani asusun taimakon kai da kai da zai tallafa musu a lokacin ta-ɓaci ko don aiwatar da wani aikin da za a samu kuɗi.

Nasarar da wannan haɗin kan ya samu a cikin ƙauyen abin koyi ne da mazauna ƙauyen ke fatan za a faɗaɗa shi zuwa wasu maciya gajiya.

"Bayyanar wannan shirin tattalin arziƙi da muhalli shi ne abu mafi kyau da ya taɓa faruwa da mu," in ji Mahamat.

Masana na kallon Gaoui a matsayin shiri abin koyi ga yankin, da zai bai wa mutanen yankin tabbatar da wadatar abinci sannan kuma su bunƙasa tattalin arziƙinsu na aikin gona.

TRT Afrika