Daga Abdulwasiu Hassan
A cikin babban tsarin abubuwa na ɗabi'a, za a sa ran samun alaƙa mai kyau mai ɗorewa tsakanin kiwon dabbobi da noma.
Nijeriya, inda noma ya zama ɗaya daga cikin jigogin tattalin arziki, amma kuma sai ya zamo wani lamari da ke jawo rarrabuwar kawuna a cikin tsarin, inda makiyaya da manoma suka daɗe suna samun saɓani.
Rikicin da ya ƙi ci ya ki cinyewa, ya kasance yana ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya, inda a lokuta da dama yake haifar da faɗace-faɗacen da ke haddasa asarar rayuka da ɓarna mai yawa.
Mafi muni shi ne yadda wannan hargitsin ya haifar da ‘yan fashi da makami, lamarin da ya sa sace-sacen mutane da tsoratarwa ya zama ruwan dare, musamman a yankin Arewa maso yammacin Nijeriya.
Girman matsalar da ta shafi kiwo a Nijeriya da kuma illolin da ke tattare da zamantakewar al'umma su suka sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi tunanin ɗaukar wani mataki da yake ganin zai iya zama mafita a kwanan baya, inda ya ƙaddamar da kwamitin Shugaban Ƙasa kan aiwatar da sauye-sauye a fannin kiwo.
Ajuri Ngelale, mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan harkokin yada labarai kwanan nan ya fitar da wata sanarwa inda ya ce an ɗauki matakin ne "domin magance matsalolin da ke kawo cikas ga ayyukan noma da kuma buɗe hanyoyin da za su amfani manoma da makiyaya da masu sarrafa kayayyaki, da masu rarrabawa a cikin tsarin noma da kiwo."
Samar da Ma'aikatar Kula da Kiwon Dabbobi ta tabbatar da wannan alkawari.
Dr Joseph Nyager, tsohon babban jami'in kula da dabbobi a Nijeriya ya ce "bangaren kiwo na Nijeriya yana da girma, yana ba da gudunmawar sama da kashi 30% ga ma'aunin tattalin arzikin ƙasar.
Yana da damar bunkasa da sauri fiye da haka idan aka samar da ingantattun tsare-tsare masu kyau," kamar yadda Dr Nyager ya shaida wa TRT Afrika.
Nyager na ganin sanarwar ta nuna cewa gwamnatin Nijeriya na ƙara mai da hankali kan harkar kiwo a kasar tare da tura karin albarkatu domin bunkasa ci gaban kasar.
Ajandar gyara
Kiwon shanu a Nijeriya ya ta’allaka ne kan yadda ake yin kiwon a al'adance, wato kiwon sake, inda makiyaya suke kaɗa shanunsu daga wannan waje zuwa wancan don neman inda dabbobin za su fi samun abinci sosai.
Hakan ya ta'azzara rikici kan samun wurin kiwo a tsawon shekaru, musamman saboda kwararowar hamada.
Rikicin manoma da makiyaya da ake samu akai-akai kan amfani da filaye ko kutsen da dabbobi ke yi a gonakin manoma ya haifar da ƙalubalan bin doka da oda tare da yin tasiri ga samar da abinci a kasar ta yammacin Afirka.
Ƙoƙarin magance waɗannan rikice-rikicen albarkatu sun haɗa da gabatar da shawarwarin noman dabbobi a gida ko a killace, amma samar da mafita mai ɗorewa ta kasance jan aiki. Gwamnati ta yi imanin cewa garambawul a fannin kiwo ne kawai mafita daga wannan matsalar.
A yayin taron da aka yi a Abuja inda ya bayyana wannan shiri, Shugaba Tinubu ya ce za a sake duba hanyoyin kiwon dabbobi na gargajiya tare da samun goyon bayan masu ruwa da tsaki.
"Muna bukatar samar da ƙwarin guiwa don bai wa Nijeriya damar da a ƙarshe za ta ci moriyar noman kiwo. Kayayyakin abinci da ake samarwa ta kiwo suna da fa'ida mai yawa ta haɓaka kasuwanci da tattalin arziki," in ji Shugaba Tinubu yana cewa.
Magance rikice-rikice
Tsawon shekaru, an gaza magance rikici tsakanin makiyaya da manoma duk da ƙoƙarin kawo ƙarshensa da aka sha yi.
Don haka, a ina ake samun saɓanin haduwar gaskiya, da aiwatarwa da sabon shirin gwamnati? Wane alfanu wannan shirin na gwamnati zai kawo wajen ci gaban ƙasar.
Shugaba Tinubu ya nuna farin cikinsa game da damar samun nasara a wannan karon.
"Lokacin da muke da damarmaki masu yawa a jihohinmu, me ya sa 'yan Nijeriya za su ci gaba da fuskantar rikice-rikice?" Ya faɗa a wajen taron.
"Mun ga mafita da damarmaki. Tare da wadannan matsaloli da suka addabe mu tsawon shekaru, na yi imanin cewa a yanzu mafita da ci gaba sun zo - a hannunku. Da irin darajar mutanen da suke nan wajen, akwai wata dama ta musamman da za a samu a ƙirƙirar ma'aikatar nan ta kula da kiwon dabbobi."
A cewar shugaban, shirin zai bai wa likitocin dabbobi samun damar yin bincike a kan dabbobin kiwo iri-iri. "Za mu iya dakatar da kisan gillar da ake samu (saboda wannan rikicin na manoma da maikiyaya)," in ji shi.
Komawa tushe
Masana sun yi imanin cewa sabon shirin zai iya yin aiki ne kawai idan ya magance tushen matsalar nan take.
"Makiyaya a Nijeriya suna tafiya da dabbobinsu domin neman kiwo da ruwa. A tsawon shekarun da suka wuce, wannan yunkuri ya kara jawo rashin hadin kai saboda babu iyaka," in ji Dokta Nyager a hirarsa da TRT Afrika.
“Hakan ya jawo arangama tsakanin makiyaya kai tsaye da manoma, wanda hakan ke haifar da munanan faɗace-faɗace, wanda ya haddasa asarar rayuka, da dabbobi da dukiyoyi tare da kawo cikas ga ayyukan noman rani.
Wannan ya zama ruwan dare gama gari kuma yana kashe mutane, tare da aikata laifuka sannan siyasa da addini sun shiga cikin lamarin sun sake dagula shi. "Ya zama batun tsaron kasa," in ji Dr Nyager.
A matsayinsa na mai ba da shawara kan ci gaban aikin gona mai ɗorewa, ya shawarci gwamnati da ta ƙarfafa yankuna daban-daban na ƙasar "don haɓaka albarkatun dabbobinsu gwargwadon fa'idarsu - ta muhalli da jinsi da al'adu".
Babban zato
Sabuwar ma'aikatar kula da kiwon dabbobi za ta gano abin da masu ruwa da tsaki a fannin suka rasa a halin yanzu tare da samar da su gaba daya.
Daya daga cikin hanyoyin yin hakan ita ce ta hanyar tuntubar juna da kuma ƙara ƙaimi a tsakanin masu ruwa da tsaki, wanda Dr Nyager ya ce a halin yanzu bai wadatar ba.
Sauran wuraren da aka fi mayar da hankali su ne samar da tallafin ababen more rayuwa da samun rance marar kuɗin ruwa sosai da taimakawa tallata haja da kuma haɓaka nau'ikan dabbobin.
Ƙwararru sun yi amannar cewa ya kamata a faɗaɗa ma'aikatar ta wuce ta harkokin kiwon dabbobi kawai.
"Tana iya ƙara kula da harkokin kiwon wasu dabbobin irin su aladu da zomaye da kifaye. Sannan ma'aikatar za ta iya zuba jari a kan kayan abinci don samun ɗorewa da kuma samar da nau'ukan abincin dabbobi," in ji Dr Nyager.