Daga Sylvia Chebet
Gawawwakin ƴan Namibiya kimanin mutum 70,000 waɗanda aka halaka a abin da ake ganin shi ne kisan-kiyashi na farko wanda aka yi a ƙarni na 20 na kwance a saharar da ke jejin Namibiya.
Haka kuma akwai wasu gawawwaki da dama da ruwa ya tafi da su cikin tekun Atlantika.
Kisan-kiyashin wanda aka kashe jama'a da dama, sojojin Jamus ne suka aikata shi kan jama'ar Herero da Nama a tsakanin shekarun 1904 da 1908.
Kamar yadda marigayi Sukarno na Indonesia ke cewa, " Kada ku manta da tarihi. Zai iya mayarwa da sauya ko mu su wane ne."
A shekarar 2021, bayan shafe shekaru ana tattaunawa, Jamus ta amince da abin da aka yi a tarihinta na mulkin mallaka a matsayin "kisan-kiyashi".
Domin ƙoƙarin biyan diyya, ƙasar da ke Turai ta amince da biyan kuɗin wani aiki a Namibiya wanda ya kai kimanin dala biliyan 1.3 a tsawon shekaru 30 sakamakon hannunta a kisan-kiyashin.
Sai dai kafin wannan ƙurar ta kwanta kan rashin adalcin da ya faru shekara 120 da ta gabata, sai Jamus ta ɗauki wani mataki wanda ya girgiza Nambiya tare da sake buɗe wannan tsohon ciwo.
Jamus ta yi alƙawarin shigar wa Isra'ila bayan da Afirka ta Kudu ta kai Isra'ilar ƙara a Kotun Duniya da ke Hague kan wani abin da jama'a da dama ke ganin "kisan-kiyashi" ne kan Falasdinawa a Gaza.
Munafunci
Namibiya na kallon hakan a matsayin Jamus ba ta yi nadamar mummunan abin da ta aikata a tarihi ba.
A wata sanarwa da Shugaban Namibiya Hage Geingob ya fitar, ya bayyana cewa " Har yanzu gwamnatin Jamus ba ta yi nadama kan kisan kiyashin da ta yi a ƙasar Namibiya ba".
Jamus ta kasa bayar da goyon baya ga Majalisar Ɗinkin Duniya game da kisan kiyashi, har da ɗaukar nauyin kisan kiyashin da aka yi a Namibiya, inda take goyon bayan irin kisan-kiyashin da ake yi a Gaza," in ji shi.
A yayin da take goyon bayan maganar Geingob, marubuciya kuma ƴar wasan kwaikwayo Girley Jazama ta bayyana cewa rashin Jamus na amincewa da kisan-kiyashi a Gaza na nufin "ku (Jamus) ba ku amince da abin da kuka yi ga jama'ar Namibiya ba daga 1904 zuwa1908.
"To, ta yaya za mu yi wa mutane hisabi game da ayyukansu? Shin za mu zauna a gefe mu bari haka ta faru? Shin hakan na nufin mantuwa ce kenan? Har yanzu ba su koyi darasu daga abin da ya wuce a baya ba? kamar yadda ta bayyana.
Duk da cewa abin da ya faru a Namibiya da Gaza ya faru a ƙarni daban-daban, sai dai Jazama ya ta babu wani sauyi da aka samu sosai.
Wannan lamari ne mai ban tsoro kan cewa a 2024 irin wannan lamari na ci gaba da faruwa," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika. "Na kaɗu da jin cewa Jamus ba ta kallon abin da Isra'ila ke yi a matsayin kisan-kiyashi.
Abin da aka ɓoye a tarihi
Kakannin Jazama waɗanda ƴan Herero ne, sojojin Jamus sun kashe su sakamakon sun ƙi amincewa a ƙwace musu ƙasarsu.
"An bayar da umarnin kashe mutanenmu, inda aka kore mu zuwa sahara domin mu mutu da yunwa da ƙishirwa. A yau, ana gudanar da hakan a Gaza, inda ake yi wa Falasɗinawa ƙawanya," in ji ta.
Wasu ƴan ƙabilar Herero 13,000 waɗanda suka tsira daga wannan abin tsoron a saharar Namibiya an tura su zuwa fursunoni inda aka kashe su.
"Sai dai abin mamaki ba kowa bane ya san da labarin kisan-kiyashin Namibiya," in ji Jazama. "An ɓoye shi daga tarihi."
Wasu daga cikin masana tarihi na da ra'ayin cewa wasu daga cikin sansanonin fursuna na Namibiya su suka zaburar da sojojin Nazi na Jamus inda suka yi sansanin fursunoni na Yahudawa, inda aka kashe miliyoyin Yahudawa a ƙarƙashin mulkin Adolf Hitler.
A yayin da ake kisan-kiyashin a Jamus, Birtaniya ta yi alƙawarin kafa ƙasar Yahudawa a Falasɗinu a ƙarƙashin yarjejeniyar Balfour.
Rikici bayan kisan-kiyashi
A daidai lokacin da hijirar Yahudawa zuwa Falasɗinu ke samun karɓuwa, sai adadinsu da ke a Falasɗinu ya ƙaru daga kashi 6 cikin 100 zuwa kaso 33 a tsakanin 1918 zuwa 1947.
Wannan ne ya sa Falasɗinawa hankalinsu ya tashi kan yadda adadin Yahudawan ya ƙaru, har aka samu fargaba, lamarin da ya jawo aka yi yaƙin Falasɗinawa da Isra'ila.
Rikici na baya-bayan nan tsakanin Isra'ila da Gaza ya soma ne a ranar 7 ga watan Oktobar bara, wanda zuwa yanzu ya kashe sama da Falasɗinawa 27,000, kusan rabin waɗanda aka kashe yara ne.
Sai dai Isra'ilar ta kafe kan cewa hare-haren da take kaiwa ba ƙaƙƙautawa ta sama da ƙasa tana yin su ne domin mayar da martani kan harin da ƙungiyar Hamas ta kai musu.
Sai dai Jamus da kakkausar murya ta yi watsi da zargin kisan-kiyashin inda take da ra'ayin cewa Isra'ila na ƙoƙarin "kare kanta" ne.
A idon Jazama, Jamus ta zo daf da daf. Bayan aikata kisan-kiyashi sau biyu a Namibiya da kuma kasarta, a yanzu ana kallonta a matsayin mai bai wa Isra'ila goyon baya a yayin da take fuskantar tuhumar kisan ƙare-dangi a Gaza.
Wasu masana na kallon matsayar ta Jamus a matsayin sakamakon irin waɗannan abubuwan.
"Fassarar ita ce Nama da Herero da Falasɗinawa ba bil'adama bane a idanun Jamus. Yahudawa da wasu farar fata ne kaɗai mutane a wurinsu," in ji Everisto Benyera, wani farfesa a Jami'ar Afirka ta Kudu a tattaunawarsa da TRT Afrika.
Benyera ya bayyana cewa hukuncin da kotu za ta yanke a lamarin Isra'ila "zai kasance wani mataki na auna adalcin kotu a duniya kanta".