A daren Alhamis ne gobara ta kama wata makaranta a tsakiyar Kenya. / Hoto: Citizen TV/X

Daga Pauline Odhiambo

Mutuwar ɗaliban makarantar kwana 21 a makarantar Hillside Endarasha Academy da ke gundumar Nyeri, sakamakon gobarar da ta kama a daren 6 ga Satumba, inda ake cikin jimamin sake samun irin wannan ibtila'i a ƙasar ta gabashin Afirka.

Daliban da ibtila'in na baya-bayan nan ya rutsa da su duk yara ne masu shekaru 10 zuwa 14. Suna daga cikin yara dalibai 156 da ke kwance a dakunansu a lokacin da gobarar ta kama a ginin, inda wasun su suka kasa kubuta.

Bayan kwanaki biyu wata gobarar ta sake afkuwa a makarantar babbar sakandiren 'yan mata ta Isiolo da ke tsakiyar Kenya, kimanin kilomita 140 arewa maso-gabas da makarantar Hillside Endarasha Academy, inda akalla dalibai uku suka samu raunuka.

A yayin da a makon da ya gabata aka fara gwajin sinadaran halitta don tantance daliban na Endarasha, wata tambaya da ake yi kan batun ita ce: Me ya sa ake yawan smaun gobara a makarantun Kenya?

Rashin kofofin yanayin gaggawa

"Na dora laifin kan yadda aka tsara wadannan gidajen kwanan da ke Kenya: yawancin su an gina su ba tare da hanyar guduwa idan wata matsala ta afku ba," in ji wani uba da ke Nairobi, Wambu Gituku yayin tattaunawa da TRT Afirka.

"Akwai yiwuwar wadannan yaran na Endashara sun mutu ne yayin kokarin guduwa daga kofa kwaya daya."

Agnes Onyango, wata mahaifiyar dalibin babbar sakandire a yammacin kenya ta bayyana ba za ta iya jure ganin danta ya tsinci kansa a irin wannan yanayi ba.

"A shekarun baya, dakunan kwanan dalibai na makaranyar da na yi sun kama da wuta sau biyu. Duk mun yi nasarar kubuta ba tare da ko jikkata ba," in ji ta. "Matukar za a yi biris da matakan kariya, wadannan gobara za su ci gaba da afkuwa."

Matsalolin hanyoyin lantarki da aka gaza kawar da su

Mujallar 'Kenya Studies Review' ta bayyana cewa iyaye da dama a Kenya sun zabi tura yaransu zuwa makarantun kwana saboda sun yi amanna da sun fi bayar da kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa.

Gobarar da ta kama a makarantar Hillside Endarasha Academy na iya tilasta wasu iyayen kwashe yaransu daga makarantun kwana.

Har yanzu ba a bayyana me ya janyo gobarar ranar 6 ga Satumba ba, amma an yi amanna da cewa ibtila'in ya faru ne bayan fashewar da kwan lantarki ya yi.

Wasu iyayen sun musanta wannan ikirari, suna masu cewa an samu 'yar hayaniya a tsakanin daliban kwana guda kafin gobarar, wanda hakan ya janyo abinda ya faru tsakar dare.

Jaridar The Daily Nation ta ambato wata uwar ɗalibai tana cewa ɗanta, ɗalibin je-ka-ka-dawo da ke aji bakwai, ya taɓa gaya mata cewa wasu ɗalibai sun shiga "zullumi" da wajen ƙarfe 4pm na yamma, ranar 5 ga Satumba.

Ɗaliban sun kwashe "tsawon lokaci" cikin ɗakunan kwana "suna tattauna wasu batutuwa", wanda baƙon abu ne.

An ambato ta tana cewa, "Tsarin da aka saba shi ne yara da ke tafiya ɗakunan kwana da rana an bayyana shi a fili. Suna zuwa can tare da meturon, inda za su ɗauki duk abin da suke so, sannan su koma nan-take. Me ya sa aka saɓa wa wannan tsari".

Hukumar makarantar ta ƙi cewa komai game da ibtila'in.

Saɓa wa tsarin kiyayewa

A 2008, ministan ilimi na lokacin, Sam Ongeri, ya wallafa jagoran kiyayewa ga makarantu, inda aka ba da cikakken bayani kan karɓaɓɓen tsari ga makarantu.

Jadawalin ya wajabta cewa duka ɗakunan ɗalibai ya samu ƙofa a kowane bango da kuma wata a tsakiya a matsayin kafa ta uku, wadda za a rubuta "Mafitar gaggawa".

A saka injinan kashe gobara masu aiki dab da kowace ƙofa, da tazarar faɗin aƙalla ƙafa biyar, da kuma ƙararrawar gobara a wuraren da ke da sauƙin kai wa.

Da yawa cikin waɗannan matakan kiyayewa an yi watsi da su, waɗanda ƙwararru suka bai wa alhakin yawan faruwar gobara cikin shekarun nan.

Sama da kashi 70% na makarantu a Kenya ba su taɓa yin atisayen kashe gobara don koyar da mutane yadda za su yi idan gobara ta afku, a cewar Usawa Agenda, wata ƙungiya da ke jin ra'ayi kan makatin koyo a Kenya.

"An samu kusan gobara shida a makarantu biyar a watan Satumba kacal," in ji Dr Emmanuel Manyasa, babban daraktan Usawa Agenda, da yake zanta wa da TRT Afrika. "Ana mace-mace ne saboda yawancin makarantu a ƙasar ba sa bin matakan kare haɗura."

Da yawan ɗakunan ɗalibai sun yi cikar wuce iyaka, inda kashi 46% ne kacal suke da wujin tattara mutane lokacin gobara.

Barazanar saka wuta

A cewar wani rahoto na 2022 na jami'ar University of Nairobi, wasu gobarar da aka yi a Kenya tayar da su aka yi.

A 2017, Hukumar binciken manyan laifuka ta Kenya (NCRC) ta gano cewa wasu ɗalibai sun fusata saboda baƙin cikin talaucin rayuwa da yanayin karatu ko tsawaitar lokacin karatu bisa dalilin gasannin motsa jiki da sauran ayyukan da ba na karatu ba.

Ƙungiyar ta ta'allaƙa wannan rashin tabbas kan tasirin abokai da masu yin kwaikwayo da suka ji labarin faruwar goabara a wasu makarantun.

A bayanan majalisa, hukumomin Kenya sun tattara bayanan gobara 130 a makarantu da ke da alaƙa da tashin hankalin ɗalibai, inda aƙalla 63 tayar da su aka yi a 2018 kawai.

Irin wannan gobara takan faru ne da dare kuma yawanci a ɗakunan kwanan ɗalibai.

Ya ce, Manyasa ya lura cewa gobarar makarantu sun fi yawaita lokacin jarrabawa. "A wasu lokutan, laifukan malamai da aka ɓata wa rai ne. Ya kamata doka ta yi aiki kan masu alhakin wannan laifi."

Tasgaro a harkar wayar da kai

Wani rahoto na majali a 2018 game da rikici a makarantu da matsalolin hakan ya ambata rashin ayyukan wayar da kai a makarantu a cikin matsalolin da ke ta'azzara batun.

Manyasa ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "A gano ɗalibai da suka ga halin tashin hankali da wuri don a ba su shawarwari".

"A yanayin da wayar da kai kaɗai bai yi aiki ba, ɗalibai da ke da matsala a kasa su a makarantun da aka yadda da su don taimaka musu a halayyarsu."

TRT Afrika