Hoton Doreen a lokacin da tana karama tare da kanenta Julius wanda ya rasu sakamakon cutar HIV yana dan shekara uku. / Hoto: Doreen

Daga Pauline Odhiambo

Kusan mutum miliyan 1.5 ne ke dauke da cuta mai karya garkuwar jiki (HIV) a Kenya. A duniya, wannan adadi ne mai yawa.

A wajen Doreen Moraa Moracha, wadda ba ta san tana dauke da cutar HIV ba har sai bayan ta kai shekara 13, bai zai yiwu a ce rayuwarta ta dakata ba kawai saboda tana dauke da wata cuta.

"Iyayena sun gano ina dauke da cutar HIV tun ina da shekara 8, amma suka boye min saboda likita bai taba tunanin ma zan girma na kai munzalin balaga ba," Doreen ta fada wa TRT Afirka.

"Likita ya bayar da shawarar cewa a rinka kula da ni a wata cibiyar kula da yara masu dauke da cutar HIV, saboda ina yawan yin rashin lafiya. Iyaye na ba su yarda da wannan shawara tasa ba."

Bayan shekaru da dama, Doreen na yin rayuwarta kamar kowa, ta yi ta fafutukar ganin an cire nuna kyamar da ake wa masu dauke da cutar.

Doreen na da karfin fada a ji a shafukan sada zumunta, tana karfafa gwiwar dubunnan masu dauke da cutar. Hoto: Doreen

A matsayin wadda ta samar da dandalin "Ni Labari ne mai dadi", wani yunkuri ta yanar gizo ga mutanen da ke dauke da HIV wanda ta fara a shafin Facebook a 2015, daga baya kuma ya yadu a sauran shafuka da manhajoji, Doreen ta zama jigo da ke karfafa gwiwa ga dubunnan masu dauke da cutar don su kalubalanaci ciwon su ci gaba da rayuwarta.

"Na zabi taken 'Eh Ina da HIV' a matsayin sunana a shafukan Twitter da TikTok saboda ita ce hanyar d ane ke bi na ke tattaunawa kan cutar HIV," in ji Doreen. "Ina bayyana matsayina ne saboda ba na son hakan ya zama wani abun mamaki ko tsoratarwa ga mutane idan na fada musu. Ina rayuwa ta kamar kowanne lafiyayyen mutum."

Gano ana dauke da cutar

Mahaifiyar ta na dauke da cutar HIV, amma mahaifinta ba shi da ita, in ji Doreen wadda amfani da magungunan ARVs ya sanya ba za ta iya saka wa kowa cutar ba.

A yayin gwagwarmayar tata, matashiyar mai shekara 31 ta shirya don zama cikin farin ciki a koyaushe, a yayin da take taimaka wa wasu wajen magance kalubalen rayuwa da cutar HIV.

Mu'amalarta da kungiyoyi daban-daban ya zama mai tattare da kwarin gwiwar bayyana tana dauke da cutar.

Doreen na kokari wajen taimakawa wadanda ke dauke da cutar. Hoto: Doreen

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce rabin masu dauke da cutar HIV a duniya na zaune da abokan zaman su da ba sa dauke da cutar-wanda abu ne da a likitance ake kira 'abokan zama serodiscordant' ma'ana daya na dauke da cutar yayin da dayan ba shi da ita.

An yi hasashen cewa har yanzu rabin mutane miliyan 39 da ke dauke da cutar a dukkan duniya ba ma su san suna dauke da ita ba. Sannan wasu da ke da alaka da wasu mutanen ba su san abokan zaman su na dauke da cutar HIV din ba.

Doreen ta ce "Mahaifina ya san matsayinsa tuntuni, kuma a lokacin da ya mutu a shekarar da ta gabata ba ya dauke da kwayar cutar. Kanne na su uku ma ba sa dauke da ita, amma dan karamin kaninmu na dauke da kwayar cutar, wanda ya mutu yana da shekara uku.

Magance nuna kyama

A lokacin da dan uwanta ya mutu, Doreen ba ta san tana dauke da cutar HIV ba, kuma an tura ta ta zauna tare da 'yan uwanta a lokacin da ake shirin binne shi. Daga baya ne ta fara gano kyamar da ake nuna mata game da yanayin da take ciki.

Ta ce "Ina iya tuna yadda nake amfani da kwanuka nawa daban a gida. Ana wanke tufafina daban da na sauran 'yan uwana." Ta kuma bayyana yadda aka fara rikici a cikin gidan bayan ta sha ruwa da kofin da ba nata ba.

Doreen na tuna yadda take tafiya daga wannan gari zuwa wancan saboda mahaifiyarta, malamar makaranta, na tsoron kar abokanan aikinta, 'yan uwa ko abokai su san halin da take ciki, kuma su fada mata.

"A makarantar kwana ina yi wa kawayena karyar cewa ina da matsalar ciwon zuciya da yake bukatar na dinga shan magani kullum," in ji ta. Bayan gama sakandire, Doreen ta fuskanci kasala saboda shan magunguna wanda hakan ya sanya ta daina shan magungunan na ARVs na tsawon shekaru biyu.

Ta kara bayani da cewa "Kusan shekaru bakwai ina fama da magunguna har zuwa wannan lokaci, sai kawai na dakata da sha." Ta ci gaba da cewa "Ciwon nawa ya ta'azzara, makogorona ya kumbura ta yadda ba na iya cin abinci. Dole sai an markade abincin da zan ci sannan na ke iya kaiwa bakina."

Bayan samun shawarwari sannan na ji ba na son zama a cikin ciwo, sai Doreen ta koma amfani da kwayoyin magungunan ARVs.

Lokacin bayyana gaskiya

Doreen ta boye ciwon nata har zuwa 2015 lokacin da ta samu aiki a Hukumar Malaman Makaranta ta Kenya. Kaddara za ta bayyana, an tura ta zuwa Cibiyar Kula da HIV don a binciki lafiyarta.

"Mun dinga gwada mutane da ba su shawarwari a sannan ne na gano cewa mutane da yawa a Kenya ba su da al'adar gwajin cutar HIV. Suna tunanin ba sa dauke da cutar," in ji ta.

Bayan watanni na gwagwarmaya da wani tunani, Doreen ta aika da sakon e-mail ga editan wata jarida tana bayanin halin da matashi da ke dauke da cutar HIV yake iya shiga a Kenya.

Ayyukan Doreen a yanar gizo ya karade dandalin sadarwa da dama. Hoto: Doreen

Ta shaida cewa "Ban yi tunanin ma zan samu amsa daga editan ba, amma sai ga shi na samu. An buga labarina a shafin yanar gizon jaridar, tare da e-mail dina. A karshen ranar, na samu sakonni sama da dubu ."

A yayin da ta yi mamakin irin yadda ake tuntubar ta, sai Doreen ta yanke shawarar kafa wata cibiya don mutane irin ta.

"Ta haka na fara 'Ni labari ce mai dadi'" in ji Doreen, kuma wannan kokari nata na yanar gizo ya karade shafukan Instagram, YouTube da LinkedIn.

"Ina saka hotuna da bidiyo tare da 'yan labaraina. A wasu lokutan, ina yada wasu labaran da na samu daga mutane ta hanyar aiko sakonnin daga masu dauke da cutar HIV. Na kirkiri yanayi na bayyanawa masu dauke da ciwon cewa ba wai iya gano ciwon ba ne muke da shi, muna da labarai masu dadi."

TRT Afrika