Daga Firmain Eric Mbadinga
Ku kalli wannan: robobin ruwa ne da aka tsinto daga bola suna komawa su zama tayil da ake shimfidawa a gidaje, da kuma robobin madara ana sake sarrafa su zuwa duwatsun ado.
Wannan ba wani abin rikita zuciya ne na aikin Babs Cardini ba, duk da cewar abin da Gabriel Hawa Toure yake yi da bola ba wani tsafi ba ne ko abin ban mamaki.
Toure ya mayar da sake amfani da robobin da aka zubar a bola zuwa kasuwanci mai kawo riba a kasarsa, inda ake tara tarin bola kowacce shekara, kuma babu wata hanya ta kimiyya da za a kawar da bolar.
Wani bincike da aka gudanar ya bayyana cewa Guinea na fitar da bolar robobi tan 500,000 a shekarar 2023. Wadannan alkaluma masu tayar da hankali ne suka sanya Toure kafa kamfani a Conakry, babban birnin kasar, don dinga sauya wannan bola zuwa kayan gini.
Kamfanin Toure mai suna 'Ziama Business Group', na da ma'anar kalaman malamin kimiyyar Faransa kuma masanin falsafa Antoine-Laurent Lavoisier da ke cewa "Babu abinda aka rasa, babu abinda aka samar, komai ya sauya."
A kamfanin Ziama, robobin da aka zubar - kwalaben roba da akwatuna da kujeru da tukwane da bututu da kayan wasan yara - ba a daukar su a matsayin bola. Ana narka su da kakkarya su ta hanyar zamani da fasaha, a ware ruwan robar da datti, sannan a niƙe su su koma kayan gini.
Mataki mai kyau
Tafiyar Toure ta fara ne da fara amsa tambaya mai sauki: "Me za a iya yi da robobin da aka zubar a shara?"
Intanet ta bayar da gudunmawar bayanan yiwuwar sake sarrafa kayan amfani da suka tsufa aka zubar. "Na samu 'yan hanyoyin warware matsalar, na yi karatu, na horar da kaina ta hanyar karatu da a aikace ta hanyar gwaje-gwaje da yin duk abubuwan da ake bukata," in ji shi yayin tattaunawa da TRT Afirka.
Toure na da damar iya yin wasu kasuwancin na daban, amma bai yi hakan ba, kawai ba kudi yake son samu ba. Yana da burin kafa wani sabon abu.
"Na shiga wannan aiki ne saboda kokarin kaina," in ji shi. "Abu mafi muhimmanci, ni dan kasar Guinea ne, kuma ina ganin yadda bolar robobi ke ƙara yawaita inda ake sake sarrafa su. Na yi tunanin akwai bukatar yin wani abu."
Toure ya yi aiki tukuru don tabbatuwar aikinsa. Ya zuba jarin lokaci da kudade wajen samar da dukkan kayayyakin da ake bukata na robobi da sarrafa su don samar da kayan gini.
Ayyuka masu yawa da wahala
Ana fara aikin ne da tattara bolar robobi, wanda Toure ke saya daga abokan huldarsa da suke ware masu kyau da marasa kyau. Da zarar an tattara, sai a markade tare da mayar da su zuwa garin da ake amfani da shi don samar da duwatsun ado da tayil na gini, da ma wasu abubuwan.
"Muna samun bola kai tsaye daga babban birni saboda an fi samun sa da yawa a can. Sannan duba da yadda kamfaninmu yake a babban birnin, na taimakawa wajen hana yawaitar bolar roba a gundumomin da ke kusa," in ji Toure a tattaunawar sa da TRT Afirka.
Kamfanin ZIama ba ya son takaita ayyukansa ga samar da kayan gini daga robobin kawai. A tsawon lokaci, aikin nasa na da manufar samar da mafita don yakar yawaitar bolar roba da gurbata muhalli.
Toure na da ra'ayin cewa samar da sauyi na bukatar wayar da kan al'umma kan muhimmancin kare muhalli.
Adadin na daduwa
A kasar da ke mutane kusan miliyan 14, ana tsammanin kowanne mutum guda ya fitar da 0.6 na kilogiram a kowacce rana.
Toure ya samu wadannan alkaluma, duba ga bayanan da aka samu daga wajen Majalisar Dinkin Duniya, lamarin na da tayar da hankali. "Muna bukatar gwamnatoci da dukkan mahukunta su fahimci girman wanan matsalar tare da samar da goyon bayan kayan aiki da kudade don samar da gine-gine da cibiyoyin da za su magance matsalar."
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO) ta bayyana cewa, kusan dala miliyan 20 na bolar roba na samar da tan miliyan 400 da ake fitarwa a dukkan duniya, na fadawa ruwan teku.
Wannan adadi mai yawa na roba na karuwa sosai kuma kananan halittu na shige wa cikin kifaye da sauran halittun teku, sannan mutane su ci kifayen, wanda ka iya janyo cutar daji ko kansa.
Dukkan WHO da MDD na rajin samar da tsare-tsare irin na Toure ta yadda za a yaki matsalolin da ke damun duniya.