Daga Abdulwasiu Hassan
Ku tuna a ce kuna da kudi a asusunku na banki amma a ce ba za ku iya cirar adadin da kuke so ba har sai kun biya wani kudi ga ejan na bayan fage.
Wannan ce gaskiya marar dadin ji ga 'yan Nijeriya da dama, musamman na yankunan karkara da babu bankuna ko tsarin bankin yanar gizo yadda ya kamata.
"Domin cirar Naira miliyan daya, sai ka biya karin Naira 20,000. Wannan tsari marar kyau da muke ciki," in ji Adamu Tilde, dan kasuwa a Jihar Bauchi da ke arewa maso-gabashin Nijeriya a tattaunawarsa da TRT Afirka.
Adamu da ke kasuwancin kayan noma, na bukatar kudade da yawa kuma tsaba saboda manoman da yake mu'amala da su ba sa karbar kudi sai tsaba.
Ba shi kadai ne yake fuskantar wannan kalubale ba. Masu sayen kayan amfanin gona da yawa na cirar kudade da yawa a lokacin kakar amfanin gona, wanda ke sanyawa ake bukatar tsabar kudi, wanda hakan ke baiwa bankuna damar karbar kudade da dama daga hannun jama'a.
'Yan Nijeriya a yankuna da dama na fuskantar irin wannan matsala a lokacin da suke son biyan kudi tsaba.
Sama da kashi 90 na kimanin Naira tiriliyan 4.55 da ke kai komi tsakanin hannayen mutane a Nijeriya na wajen bankuna, in ji babban bankin kasar.
Babban abin damuwar ma shi ne yadda matsalar ke ci gaba, duk da kara zuba Naira tiriliyan 1.59 kasuwanni a shekara dayan da ta gabata.
Wawaye
Kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka ta fuskanci karancin tsabar kudade a lokacin da ake gaf da zaben 2023, wanda hakan ya zo daidai da aikin sauya fasalin kudaden Nijeriya da Babban Bankin Ƙasar ya ce zai yi don karfafa janye tsaba daga hannayen jama'a da kuma yaki da garkuwa da mutane don neman fansa da yaki da rashawa.
A matsayin wani bangare na sauyi, an bukaci 'yan Nijeriya da su kai tsaffin kudaden da ke hannayensu bankuna don karbar sababbi.
A yayin da a rubuce tsarin ya zama kamar mai yiwuwa, abinda mahukunta ba su yi hasashe ba shi ne samun dogayen layuka a bakin bankuna da na'urar ATM a fadin kasar, inda mutane ke ta gwagwarmayar sauya kudaden ko samun tsaba.
Wadanda suka matsu suna bukatar tsabar kudi, dole ne su koma ga masu POS wanda hakan ke kara yawan ladan karbar tsaba da suka yi.
Babban Bankin ya kara wa'adin da ya bayar na daina ta'ammali da tsaffin kudaden bayan Kotun Kolin Nijeriya ta yanke hukuncin cewa ba a baiwa 'yan kasa isasshen lokaci ba.
Mahukuntan bankin sun fitar da sanarwar tabbatarwa da 'yan Nijeriya cewa za a ci gaba da ta'ammali da tsaffin kudaden Naira.
Babu kudade a injinan ATM
Injinan da ake cirar kudi d ayawa a fadin kasar sun daina bayar da kudin saboda babu takardun a ciki, inda wasu mutanen suka alakanta karancin ga baiwa masu sana'ar POS kawai.
Wannan ne ya sanya Babba Bankin bayar da umarni ga bankunan kasar a karshen shekarar da ta gabata da su tabbatar da sun samar da isassun tsabar kudade ga abokan huldarsu a cikin bankuna da injinan ATM. Bankin ya yi gargadin cewa gazawar tabbatar da hakan zai janyo sanya takunkumi.
"Daga 1 ga Disamban 2024, ana kira ga jama'a da su kai rahoton duk wata wahala da suka fuskanta wajen cirar kudi a bankuna ko injinan ATM zuwa ga Babban Bankin ta hanyar lambobin waya da adireshin email da aka bayar a jihohinsu," in ji gwamnan CBN Olayemi Cardoso.
"Cibiyoyin kudi da aka samu suna aikata ba daidai ba ko zagon kasa za su fuskanci hukunci."
A ranar 14 ga Janairu, CBN ya ci tarar bankunan Nijeriya su tara kudi har Naira biliyan 1.35 saboda kin aiki da umarninsa na zuba isassun kudade a injinan ATM.
Hakama Sidi Ali, Daraktar Sadarwa ta Bankin ta ce manufar hakan ita ce a tabbatar da an yi aiki da umarnin da samun ingantaccen tsari. "Tabbatar da samun isassun kudade ba tare da cikas ba na da muhimmanci wajen samun amintar jama'a da kyawun tattalin arziki."
Duk da haka, wasu jama'ar na tantama kan ko tsarin zai tsaftatu, ganin irin rikicin da aka yi a lokacin sake fasalin Naira ba da jimawa ba, lamarin da ya sanya jama'a fitar da rai daga tsarin banki a Nijeriya.
Manufar daina tu'ammalin kudade da tsaba
A yayin da Babban Bankin ke kokarin magance muzanta takardar Naira, yana kuma ganin an koma mu'amala ta hanyar amfani da bankin yanar gizo.
A wata sanarwa mai taken "Kudaden da Za a Iya Cira Daga Bankunan 'Yan Kasuwa" a watan DIsamba an bayyana cewa babban bankin ya saka iyakance cirar Naira 500,000 ga daidaikun mutane a kowanne mako.
Wannan umarni ya shafi dukkan bankuna, manya da kanana, da ma kamfanonin kudi na yanar gizo.
Manufar saka wannan iyaka ita ce habaka kasuwanci ba da tsabar kudi ba da kuma inganta aika kudade kai tsaye daga asusu zuwa wani.
Dr Bello ya ce wannan na da saukin fada ama da wahalar aikatawa, idan aka kalli me jama'a suke so a kasuwani, kananan kasuwanci neke rike da bangare babba na tattalin arzikin kasar.
"Kiyashin da Asusun Bayar da Lamuni na Duniya ya na cewa kananan kasuwanci a Nigeria na smaar da kashi 65 zuwa 70 na tattalin arzikin Nijeriya. Hakan na nufin kashi 65 na ta'ammali da kudaden da ake yi da tsabar kudi ake yin su, ba wi ta hanyar banki ba." in ji shi a tattaunawar da ya yi da TRt Afrika.
Aliyu Alfa, wani ejan ne da ke babban binin Abuja, shi ma yana da ra'ayi irin na Dr Bello, yana mai cewa tarar da aka saka ga wadanda za su ciri kudade da yawa bai kamata ba, wannan kashe kasuwanci.
"Ka dauki misalin leburori da ke jira a biya su. Kudinsu na iya kaiwa sama da Naira 500,000. Ba ruwan ma'aikaci da wani kayyade kudaden cira daga banki ba. Kawai shi ka ba shi kudadensa kuma tsaba."
'Yan kasuwa irin su Tilde, wadanda suke yawan mu'amala da manoma da suka saba rike tsabar kudi kuma ba sa amfani da manhajar bankuna, na jiran ganin ranar da wadannan mutane za su karbi wannan tsari.
Za a ci gaba da amfani da tsabar kudi a hada-hadar kasuwanci a Nijeriya, hakan zai kau ne idan babban bankin kasar da manyan 'yan kasuwa suka samar da mafitar cike gibin tsabar kudi, ko idan suka samu nasarar samar da hanya mai sauki ta saye da sayarwa.