Shugaban China Xi Jinping ya gayyaci shugabannin ƙasashen Afirka 50 zuwa Beijing a wannan makon don halartar taron da ke da manufar haɓaka alaƙarsu da nahiyar, musamman a yankunan da gogayya da ƙasashen Yamma take da karfi.
Ƙasar da ke karɓar baƙin ta gudanar da taron maraba da zuwa a wajen Babban Taron Haɗin Kan China-Afirka (FOCAC) a matsayin girmamawa da nuna muhimmanci ga ƙawayen kasuwanci. China ce babbar ƙawar kasuwancin Afirka kuma wadda ta fi baiwa ƙasashen nahiyar bashi.
Tsarin bayar da bashin ya baiwa China damar bayar da biliyoyin daloli na gudanar da manyan ayyuka a karkashin shirinta na 'Belt and Road (BRI)'.
Shugabannin Afirka sun isa wajen taron a Beijing a wannan makon da babban burin samar da alaƙar kasuwanci da kowane ɓangare zai amfana da zuba jarin da zai samar da ayyukan yi.
"Daga cikin dukkan manyan taruka takwas ina tunanin wannan ne ya fi samun nasara idan aka kalli karsashin da kasashen Afirka suka nuna. Sun san irin abinda suke so. Suna kokarin tabbatar da sun kare manufofinsu," in ji David Monyae, daraktar Cibiyar Nazarin Alakar Afirka-China da ke Jami'ar Johannesburg.
Shugaba Xi ya yi alkawarin ɗaukar nauyin ayyuka na sama da dala biliyan $50 a Afirka a shekaru uku masu zuwa, tare da samar da ayyukan yi miliyan guda, duk da zargin manufar bayar da bashi ta China na barin kasashen Afirka cikin gwagwarmayar biyan basussukan.
"A fikirance, amfanin waɗannan ayyuka a nan gaba ya fi na basussukan muhimmanci saboda suna kawo habakar tattalin arziki. Sai dai kuma, ma'aunin wannan amfani na da wahala sabod amatsin lambar da ake yi wa kasashen don biyan basussukan, wanda hakan ke sanya wa ake kallon kamar wata dawainiya ce maimakon abu mai amfani," in ji Beverly Ochieng, babbar mai nazari a 'Control Risk', kamfanin bayar da shawarwari a Yammacin Afirka.
Ta kara da cewa "Kasashen Afirka kuma sun zabi manufofin bashin China saboda yadda ba ta saka wasu sharudda na yadda za a kashe kudaden."
Sabuwar mahanga
Ana tsammanin taron zai bayar da mahanga kan kawancen China da Afirka bayan annobar Corona. Shugaba Xi ya yi nuni da raguwar yin manyan ayyuka da mayar da hankali ga tsarin kasuwanci da bayar da bashi ta hanyar amfani da hukumomi, in ji Ochieng.
Ta ce "China ta sake farfado da zuba jarinta da mayar da shi ga tsarin da zai iya ɗorewa ta fuskar bayar da bashin saboda matsalolin tattalin arziki a cikin gida. ta kuma kulla yarjejeniya kan sharuddan bayar da basussuka ga kasashe irin su Zambia da Kenya don dorewar alaƙarsu da tabbatar da an biya basussukan."
A yayin halartar taron, shugabannin Afirka sun nemo karin basussuka don gudanar da manyan ayyuka na bututun mai, da samar da makamashin lantarki da layin dogo na jiragen kasa, kamar yadda sanarwar bayan ganawar Xi da shugabannin ɗaya-bayan-ɗaya ta bayyana.
Nijeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar makamashin nukilya. Salva Kiir na Sudan ta Kudu ya tattauna da kamfani China don shirin shimfiɗa bututun mai ta zuwa Djibouti don habaka fitar da albarkatun man zuwa kasashen waje.
Tanzania da Zambia sun sanya hannu kan yarjejeniyar farko don gina layin dogo a muhimmiyar hanya don fitar da copper daga Zambia.
Shugaban Kasar Kenya Williams Ruto ya nemi kudade don daukar nauyin samar da ingantaccen layin dogo da zai hada babban birnin Nairobi da garin Mombasa na gabar teku bayan China ta dakatar da bayar da kudaden.
Makamashin da ba ya gurɓata muhalli da sauyin yanayi - bangarorin da a yanzu China ke jagoranta a duniya - na daga batutuwan da aka kulla yarjeniyoyi a kai a wajen taron.
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya fada wa kamfanonin China cewa yana neman masu zuba jari a fannin makamashi a yayin da kasarsa ke fama da matsalar lantarki, wanda ya munana a cikin shekaru tare da lalata kasuwanci da jindadin rayuwar jama'a.
"China ta samu nasara wajen ci gaban samar da makamashi da ba ya gurɓata muhalli. Tare za mu iya samar da makamashi mai dorewa da ba ya cutar da muhallinmu kuma ya amfani kasashenmu gaba daya," in ji shi yayin gana wa da 'yan kasuwa a Beijing.
Ja-in-ja saboda Afirka
Ayyukan kasashen irin su China a Afirka a shekaru 20 da suka gabata sun sauya yadda nahiyar ke mu'amala da manyan ƙasashen Yamma.
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta bayyana cewa rashin tunani ne Tarayyar Turai ta gina hanya daga wajen hakar ma'adanin copper zuwa gabar teku idan har dukkan wuraren mallakin China ne.
Masu nazari na gargadi, amma kuma, cewa ci gaba da samun karfin fada a ji na China ba abin da za a duaka sako-sako ba ne a Afirka ta fuskar alakar diplomasiyya da sauran kasashen duniya manya da ke da ruwa da tsaki a zuba jari a nahiyar.
Sun bayyana cewa sauran bangarori na iya ci gaba da kasancewa masu aiki a fannoni daban-daban kamar yadda China take, amma dole ne kasashen Afirka su yi kokarin samun cigabansu da kan su maimamakon ka da kai kacokan da gwagwarmayar manyan kasashen duniya.
"Aikinmu a Afirka ba shi ne bin wani bangare ba, muna bukatar dabbaka kishin Afirka tare da tafiya da duk wanda ya zo da wani abu da zai amfane mu," in ji Monyae.
Manyan kasashen duniya za su ci gaba da amfani da diplomasiyyar shirya tarurruka don hada kai da Afirka. taron ya ya samu karbuwa da muhimmanci, a lokacin da ake rikici tsakanin Rasha da Ukraine.
"Kasashen Afirka za su ci gaba da zama wajen fafutukar ƙasashe daban-daban. Har yanzu nahiyar na gabatar da damarmki na ci gaban tattalin arziki da amfana da yawaitar dan adam," in ji Ochieng.
Ta kara da cewa "Akwai gogayya mai karfi a tsakanin manyan ƙasashen duniya wajen gudanar da irin wannan taro da zai ƙara karfinsu a Afirka."