Daga Pauline Odhiambo
Crystal Asige ta rasa ganinta sakamakon cutar glaucoma a lokacin da take farkon shekarunta na 20, sai dai a yayin da lokaci ke ja, hangen nesanta a matsayinta na mai fafutukar kare hakkin ɗan'adam na ɗaɗa karfi sosai.
A shekara 33, Crystal ta zama sanata a majalisar dokokin kasar Kenya inda ta soma wakiltar mutane masu fama da nakasa a hukumance daga shekarar 2022.
Kafin ta fara siyasa, takan yi wa kanta lakabi da "VIP", ma'ana "masu fama da lalurar rashin gani". "Mutumiyar" da ta kammala karatun zuwa "majalisar dokoki".
Duk da cewa Crystal ba ta taɓa tunanin shiga harkar siyasa ba, abin da ta sani a ko yaushe shi ne waka da kare haƙƙin ɗan'adam su ne burin rayuwarta.
''Zama sanata wani ƙarin matsayi ne ga muryata da kuma baiwar waƙa da Allah ya ba ni'', kamar yadda mawaƙiyar, kuma ƴar majalisar ta shaida wa TRT Afirka.
"Da farko nakan yi amfani da waƙoƙina wajen fafutukar kare 'yancin jama'a, yanzu kuma a matsayina na Sanata nakan fito fili na yi magana kan hakkinsu.''
Soma shirin fafutukar Crystal na zama wani ɓangare da ya samo asali daga ƙuruciyar rayuwarta tana makarantar yara ta Nusery inda ta sha gwagwarmaya da masu cin zarafinta a filin wasa, a maimakon ta kai wa iyayenta ƙorafi sai ta gwamnace ta koma gida ta yi waƙa a kan abin da ya faru.
Lalacewar ganinta
A lokacin da take makarantar sakandare, Crystal ta kasance mai ƙwazo a fannin wasan kwaikwayo da nishadi bayan da ta lura da cewa yanayin karatu na ɗaɗa wahala.
Daga nan ta soma tunkarar kalubalenta wajen zama a layin gaba a cikin aji a kullum don ganin rubutun allo da kyau.
"Nakan haddace rubuce-rubucena da zarar an bani ta yadda zan iya rike duka layin a kaina, a yayin karatu kuma ba zan ji kunyar karantawa a gaban sauran yaran da muke tare ba," in ji ta.
Bayan kammala karatunta na sakandare a 2007, Crystal ta tafi kasar Birtaniya don karanta fannin Fim da nishadi a Jami'ar Bristol ta Yammacin Ingila.
Sai dai zauren daukar karatun na da matukar girma ba kamar irin na makarantar da ta baro ba, don haka aka tillasta mata yin gwajin ido, daga ta gano tana dauke da cutar glaucoma.
Glaucoma cuta ce da ke lalata jijiyar gani na ido, wadda a mafi yawan lokuta ta ke kara matsa lamba a cikin ido, kana ta lalata jijiyoyin gani.
Likitoci sun yi hasashen Crystal za ta makance gabaki daya a shekarar 2013.
Labarin ya jefa ta cikin damuwa. Ta yi ta tunanin kashe kanta duk da cewa an yi mata aikin tiyata da dama don rage matsi a idanunta.
Daga nan ne Crystal ta samu nutsuwa a cikin wakoki, inda ta fitar da ƙundin wakokinta na farko, mai suna Karibia (Get Closer), a shekarar 2014.
Kundin ya samu yabo saboda salon ƙidar da ya kunsa, kazalika wakar Pulled Under, guda daga cikin kundin, ya haura zuwa lamba 1 akan ɗaya daga cikin shafin auna nasarar wakoki a Birtaniya a 2016.
Waka da Siyasa
Kafin ta shiga siyasa, Crystal ta gina sana’arta a matsayin mai magana da jama’a wato ''public speaker'' inda take magana a manyan tarukan jama’a a duniya. Amma siyasa ta bambanta.
"Da kyar nake iya magana a watannin farko da na shiga majalisa, a takure na ke cikin daukka jaga-jigan siyasa da suka shafe shekaru 30 suna fagen,'' Crystal ta shaida wa TRT Afrika.
"Amma daga karshe da na yi magana, sai takwarorina suka fara ganina a matsayin kwararre a fannin, ba wai karamar yarinyar da aka kawo don a tabbatar da aikinta ba kawai."
Haɗa waka da fafutukar siyasa, Crystal ta fitar da waƙarta ta Tattoo wadda ya zo daidai da karuwar take hakkin mata da cin zarafinsu a Kenya.
“A ranar masoya taVALENTINE, na gabatar da kudirin dage zaman majalisar don tattauna batun take hakkin mata, tun da farko na yi kira ga mata ƴan majalisar da su sanya bakaken tufafi maimakon ja a ranar don nuna goyon baya ga matan da suka rasa rayukansu ta hanyar jinsi da tashe-tashen hankula ko kuma wadanda ake cin zarafinsu," in ji Crystal.
Dokar Nakassasu
A watan Fabrairun 2024, Crystal ta gabatar da wasu kudurin doka guda hudu wandanda suka haifar da muhawara a Majalisa kana aka zartar da su gaba daya a wani yunkuri mai cike da tarihi wanda ya sa ta kasance cikin Sanatoci jajirtattu da suka kware a aiki a kasar.
Daga cikin kudurorin da aka zartar, dokar ta samarwa masu fama da nakasa ta bukaci haɗa naƙasassun ɗalibai da manyan makarantu.
Dokar Harshen Kurame ta Kenya ta tabbatar da cewa an bai wa masu fama da lalura ta kurame dama kamar kowa a tsarin ilimin kasar.
Dokar sana'o'i masu tasowa ta bayyana muhimmancin rawar da kananan kasuwanci ke takawa wajen janyo masu zuba hannayen jari daga kasashen waje kai tsaye tare da magance rashin aikin yi tsakanin matasa, gami da nakasassu.
A cewar ƙididdigar ƙidayar yawan jama'a da gidaje ta kenya na 2019, kusan mutane 918,000 masu shekaru biyar zuwa sama ne ke fama da lalura ta nakasa.
Galibin wadannan mutane ana ƙyamatarsu ba tare da hana su ko kuma takaita musu tsarin samun ilimi ba.
"Muna so mu kawar da wariya da ake nunawa a makarantu ga waɗanda ke da buƙatu na musamman don mu kara yawan masu ilimi daga mutane masu fama lalura ta nakasa," a cewar Crystal.
Kudirin naƙasassu ya kasance wanda Crystal ta fi alfahari da shi, saboda bukatar neman soke dokar 2003 kan mutanen masu lalurar nakasa.
"Dokar baya ta bukaci mutane masu lalurar nakasa su biya haraji da zarar sun samu aikin yi, to amma ina ga mutanen masu fada da tsananin nakasa da ba za su iya samun aikin yi ba saboda sun dogara ga masu kula da su? in ji ta.
Kyakkyawan wakilci
Crystal na fatan mutane da dama masu fama da nakasa za su shiga siyasa don ƙirƙirar dokar da ta dace da manufar karfafa nakasassu.
Kundin tsarin mulkin kasar Kenya ya bukaci a ware mafi karancin wakilci na kashi 5 cikin 100 na ayyukan gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu wajen nada nakasassu, sai dai abin takaicin ba a samun hakan daga sassan biyu.
"Ni kadai ce ƴar majalisa mai fama da matsalar lalurar gani a majalisar dokokin kasa sannan daya daga cikin mutane biyu masu fama da nakasa a cikin Sanatoci 67.
A cikin ƴan majalisa 359, mu nakasassu kusan 11 ne. Don haka babu shakka akwai buƙatar ƙarin wakilci" a cewar Crystal.