Daga Pauline Odhiambo
Patience Achieng na da shakara 14 lokacin da ciwon mutuwar ɓarin jiki ya same ta inda ta zama gurguwa.
Yarinyar mazauniyar Nairobi ta dawo yin magana bayan makonni biyu, amma za ta dauki tsawon shekara uku kafin ta sake iya tafiya da ƙafafunta.
"Lamarin ya faru a shekarar farko da na ke sakanadire a 2014. Na je dakin shan magani na makarantar bayan jin alamun zazzabi. Snn zaci Malaria ce, sai aka ba ni wasu kwayoyin cutar," in ji Patience da ke da shekara 24 a yanzu haka yayin tattaunawa da TRT Afirka.
A lokacin da yanayin jikin Patience bai yi kyau ba, iyayenta sun kai ta asibti,.
Makonni biyu bayan kwantar da ita a asibiti, an sallami Patience don ta je ta ci gaba da farfadowa a gida. Amma cikin 'yan kwanaki yanayin jikin nata ya sake ta'azzara.
"Na farka da safe ba tare da jin zan iya taka wa da kafafuna ba," in ji ta. "Ba na iya jin ina hannayena suke kuma ba zan iya takawa ba."
Gwaje-gwajen da aka yi sun nuna wani busasshen jini ne ya janyo daina zuwan jini ga kwakwalwar Patience, wanda hakan ya janyo mata mutuwar barin jiki.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce mutuwar barin jiki saboda dunkulen jini na iya afkuwa saboda dalilai daban-daban.
A tattare da yara 'yan kwanaki 29 zuwa shekara 18, mutuwar rabin jiki na faruwa ne sakamakon matsalar zuciya da kwayoyin cutar sikila.
Wasu bangarorin da ke kawo hatsari su ne cututtuka masu yaduwa, ciwo a kai ko wuya, cututtukan cikin jijiyoyi da matsalar gudanar jini.
Patience ta ce "Likita ya fada mana cewa ba zan sake iya magana ko tafiya ba saboda yanayin mutuwar rabin jikin nawa ya munana sosai, kamar wata karama ce yadda na dawo na fara magana da ma tafiya daga baya."
"Na wayi gari ina motsa baki inda na fada wa mahaifiyata, 'Kin san zan iya magana yanzu? Kamar mutuwar rabin jikin, maganata ta dawo ba zato. Shi kan sa likitan ya yi matukar kaduwa da ganin hakan."
Balaguron waraka
Patience ta yi amfani da abubuwan taimaka wa wajen yin tafiya da yawa, ciki har da kujera da sanda, kafin daga baya ta fara tafiya amma dai ba kamar kowa ba.
Burinta na komawa makarantar sakandire ne ya sake zaburar da ita wajen ganin ta dawo tana tafiya.
Makarantu da dama sun ki karbar ta, suna bayyana ba su da kayan aikin tallafawa nakasassu.
"Na yi gwagwarmaya don samun gurbi a makaranta, amma komawar wata tafiya ce ta aminta da kai," in ji Patience, wadda a yanzu ke samar da wani shiri kan yadda makarantu za su samu hanyoyin tafiyar nakasassu.
"A lokacin ina amfani da sanda, a lokacin ne lamarin ya ta'azzara na fahimci lallai ina da wannan nakasa. Iyalina na taimaka min da duk abin da na ke bukata, amma yana da wahala yadda a yanzu sai dai na dogara kan abokan karatu don tallafa min."
Tun da kafa da hannun hagu na Patience sun yi rauni, tana fama wajen shiga da fita daga dakin karatu.
"Zai dauke ni tsawon awa guda wajen tafiya zuwa aji. Haka ma rubutu da zane na ba ni wahala saboda ba na iya amfani da dukkan hannayena, wanda hakan ke sanya wasu malaman kin yin hakuri," in ji ta.
Wasu daga tsaffin abokan karatun Patience sun zamar mata garkuwa. "Suna taimaka mana wajen tattaki, suna raka ni zuwa aji, suna kasancewa tare da ni a koyaushe." in ji Patience.
Wata rana, tana kokarin neman taimako, Patience ta gwada yin tafiya ita kadai ba tare da taimakon abokan karatunta ba.
Nan da nan ta fadi tare da jin ciwo a kafarta. Bayan gwada hakan a lokuta daban a baya, matashiyar a karshe dai ta fara tafiya ita kadai.
"Ina bukatar yin hakan don rayuwa sannan na kuma ji dadi a karan kaina," in ji Patience da ta kammala Sakandire a 2019 ta kuma shiga jami'a.
"A yanzu na daina amfani da sanda ko wata madogara don tafiya, duk da akoyaushe akwai damuwa game da samun daidaito. Idan ina son na tsaya kyam, sai na lwankwasa kafata ta hagu. Amma idan ba haka ba, Ina ji na kalau." in ji ta.
Warakar kwakwalwa
Karatun Patience a jami'a ya samu tsaiko saboda kalubalen kudade, yanayin da ya sake dawo mata da kuncin rayuwa.
"Na yi ta kai komo na kashe kai, ina yawan tambayar kaina, 'Me ya sa mutum zai dinga wahala haka? Cikin nasara, iyayena sun kai ni wajen masanin halayyar dan adam, wanda ya taimake ni wajen farfadowa," in ji ta.
Patience ta fara rubuta makala tare da raba ta a wurare daban-daban tare da neman taimako ga nakasassu, kuma ta dinga samun jawabi mai kyau da karfafa gwiwa.
"Na gaji da jiran tsarin karatu ya karbe ni ydda ya dace, sai na mayar da hankali ga taimakawa yara kanana da masu tasowa don su ji ana ba su kariya," in ji Patience da a yanzu haka ke aiki da UNICEF da Cibiyar Gifted Community ta Nairobi.
"Na mayar da hankali ga samun lafiyar kwakwalwar yara kanana da ke da nakasa, tare da tabbatar musu da cewa akwai manufofin kare hakkokinsu don su je makaranta kuma a kula d asu yadda ya kamata."