Daga Abdulwasiu Hassan
Ka yi hasashen cewa ga ka nan za ka yi tafiya daga babban birnin Faransa, Paris zuwa babban birnin Nijeriya Abuja, amma sai jirgin saman da ka bi ya ajiye ka a N'Djamena, babban birnin Chadi, inda bai fi nisan kilomita 1,100 ba daha wajen da za ka sauka.
Wasu 'yan Nijeriya da a kwanan nan suka yi irin wannan bulaguron da jirgin saman ƙasar Faransa wato Air France sun yi ƙorafi kan yadda aka bar su a Chadi a cikin wani yanayi da suka kasa fahimtarsa.
Lamarin ya faru a jejjere, har sai da 'yan Nijeriya suka buƙaci Ministan Sufurin Jiragen Sama na ƙasar Festus Keyamo da ya shiga tsakani.
"Tuni na bai wa sashen da ke kula da walwalar abokan hulɗa na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya da su yi abin da ya dace su kuma tattauna da Afir France... Ina buƙatar Air France da su fitar da sanarwa a kan batun waɗannan 'yan Nijeriyar," kamar yadda Keyamo ya wallafa a shafin X.
Mummunan yanayi
Bayan nan ne sai Air France ta fitar da sanarwa tana mai cewa an bar fasinjoji masu zuwa Abujan a Chadi ne saboda jirgin ba zai iya ƙarasawa Nijeriya ba saboda mummunan yanayin da ake fuskanta. Sai dai kamfanin ya yi alkawarin kai 'yan Nijeriyar Abuja da kaɗan da kaɗan.
Duk da cewa babu nisa sosai tsakanin N'Djamena zuwa Abuja, to kuɗin jirgin na da matuƙar tsada.
Ƙwararru a fannin sufurin jiragen sama sun ce kuɗin jirgin na tsada ne saboda ba a faye samun jiragen da ke zirga-zirga tsakanin biranen Afirka ba sosai. Alal misali, nisan da ke tsakanin Nairobi babban birnin Kenya zuwa Dubai na UAE kusan ɗaya ne da Lagos, amma idan Lagos mutum zai je daga Nairobi sai ya biya kuɗin tikiti dala 900, yayin da zai biya dala 600 zuwa Dubai.
A wasu lamurran kuwa, dolen matafiya na Afirka su bi jiragen da za su yada zango a wata nahiyar daban a tafiyar da za su yi zuwa wata ƙasar ta Afirka.
Tasirin mulkin mallaka
Rashin samun jiragen da ke zirga-zriga kai tsaye a tsakanin biranen Afirka na sa bulaguri matuƙar tsada a nahiyar.
Masu sharhi a kan sufurin jiragen sama sun ce rashin samun jirage masu zirga-zirga kai tsaye a tsakanin ƙsashen Afirka sun nuna yadda mulkin mallaka ya yi tasiri a kan fannin sufurin jirgi da tsare-tsare.
Abubuwan more rayuwa da aka gina a zamanin mulkin mallaka sun fi fifita zirga-zirga tsakanin manyan biranen ƙasashe da suka yi mulkin mallakar a kan na kasuwanci a tsakanin ƙasashen Afirkan.
"Alal misali bari mu kalli Nijeriya, a can baya an tsara zirga-zirga ne tsakanin Abuja zuwa London, yayin da a Senegal kuma aka tsara tsakanin Dakar zuwa Paris," kamar yadda Kyaftin Sanusi Ado, shugaban ƙungiyar kamfanonin jiragen sama na Nijeriya ya shaida TRT Afrika.
Kyakkyawan fata
Amma duk da ɗumbin ƙalubalen da ake fuskanta na bulaguri a tsakanin ƙasashen nahiyar, ana hasashen cewa fannin sufurin jiragen sama na Afirka zai bunƙasa nan da shekaru masu zuwa.
"Afirka ta samu ƙaruwar masu tafiya da kashi shida cikin 100, inda ya ƙaru daga miliyan 15.1 a watan Mayun 2023 zuwa miliyan 15.9 a watan Mayun 2024, lamarin da aka alaƙanta shi da sabbin wuraren zuwa da aka samu da kuma ƙaruwar zirga-zirgar," kamar yadda Ƙungiyar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Afirka, AFRAA ta faɗa a wani sabon rahotonta.
Rahoton ya ƙara da cewa kuɗaɗen da fannin sufurin jiragen sama ke samu ya ƙaru sosai a wannan ɗan tsakanin.
AFRAA ta yi hasashen cewa zirga-zirgar sufurin jiragen sama za ta ƙaru nan da ƙarshen shekarar 2024, kuma bulagurin jiragen sama a naihyar zai ƙru da kashi 15 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2023.
'Akwai gwaggwaɓan alheri a gaba'
Shugaban kamfanin Jiragen Sama na Rwanda, RwandAir, Yvonne Makolo wanda shi ne shugaban daraktocin Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasa da Ƙasa (IATA), shi ma yana da kyakkyawan fata kan cewa fannin sufurin sama zai bunƙasa nan ba da jimawa ba.
"Afirka nahiya ce mai yawan al'umma fiye da biliyan ɗaya. Babbar nahiya ce, wacce kashi ɗaya cikin biyar na yawan al'ummar duniya ke cikinta, amma take da kashi biyu kacal cikin 100 na sufurin jiragen sama na duniya," kamar yadda ta shaida wa IATA kwanan nan
"Akwai (duk da haka) babbar dama ta sufurin jiragen sama don ba da gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar nahiyar."
Ta ci gaba da cewa, shirin Focus Africa, wani shiri na kungiyar kamfanonin jiragen sama na duniya, ya bayyana manyan batutuwan da masana'antar ke fuskanta a nahiyar.
Bukatar zuba jari
Batutuwan da aka bayyana sun hada da "bukatar zuba jari don bunkasa ababen more rayuwa, da bukatar aiwatar da ka'idoji da za su inganta tsaro da kuma yiwuwar samar da kasuwar sufurin jiragen sama na Afirka guda daya don inganta bulaguro a cikin nahiyar."
Sanarwar da kamfanin kera jiragen Boeing ya fitar a shekarar 2023 na cewa zai bude cibiyar samar da kayayyakin jirage a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, ta sanya fata ga masu ruwa da tsaki a fannin sufurin jiragen sama na Afirka.
"(Idan aka aiwatar da ita), matakin zai yi kyau ga masana'antar sufurin jiragen sama a nahiyar," in ji Sanusi na Nijeriya, inda ya bukaci kamfanonin ƙera jiragen su ma su kafa cibiyoyin hada-hadar kasuwanci a Afirka.
Kwararru kan harkokin sufurin jiragen sama sun ce bunkasa masana'antar ƙera kayayyakin jirgi a Afirka zai taimaka wajen rage matsalar tashin jirage a lokuta da dama sakamakon rashin isassun jiragen.
Sufurin jiragen sama na bai-ɗaya
Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta amince da kasuwar sufurin jiragen sama guda daya ta Afirka (SAATM), wani shiri da ke da nufin samar da hadaddiyar kasuwar sufurin jiragen sama a nahiyar Afirka, don ci gaban fannin sufurin jiragen sama a Afirka, da kuma zama wani abin da zai karfafa tattalin arzikin nahiyar, nan da shekarar 2063.
"Ina fata kasashen Afirka za su rungumi wannan shiri na (AU) da kuma aiwatar da shi don tabbatar da cewa an kara inganta alaka a kasashen Afirka," in ji Sanusi.