Abin da ya haddasa zazzafar muhawara kan tsarin iyali a Morocco

Abin da ya haddasa zazzafar muhawara kan tsarin iyali a Morocco

Tsarin da ake kokarin yi wa kwaskwarima ya kunshi batutuwan da suka shafi aure da rabon gado.
 A shekarar 202 adadin matan da suke aiki a Moroko ya kai  kashi 19.9 cikin 100 idan aka kwatanta da adadin 70.4 cikin na maza. Hoto: Brahimi Zidi.  

Daga Mohamed Touzani, TRT Afrika, Rabat, Morocco

A yanzu haka dai gwamnatin Maroko ta kaddamar da wani shiri na yi wa kundin tsarin iyali ko Moudawana a kasar kwaskwarima.

An samu rarrabuwar kawunan al'umma tsakanin masu fafutukar tabbatar da cewa an dora daga inda ake da kuma masu yin kira kan a yi gyara.

A watan Satumban da ya gabata ne, Sarki Mohammed na VI ya kara bai wa masu kira da samar da daidaito tsakanin jinsi karfin gwiwa ta hanyar kafa musu hukuma wacce ke da alhakin tuntubar kungiyoyin mata da malamai (masu ilimin addini) da masana da ma’aikatun gwamnati don samar da wani tsari na kawo sauyi ga kundin tsarin iyali bisa ga tsantsar gaskiya.

Tsarin zai mayar da hankali wajen tafiya da sauyin tattalin arziki da zamantakewa da siyasa da aka samu a Moroko cikin shekaru 20 da suka gabata.

An sa ran hukumar ta gabatar da rahotonta ga Sarki Mohammed na VI a cikin tsawon watanni shida.

A matsayinsa na Amir Al Mouminine (Shugaban Muminai), sarkin zai yanke hukunci kan kwaskwariman da ake shirin yi kafin mika wa gwamnati daga kuma ya isa waurin majalisar dokoki don aiwatar da shi a matsayin doka.

Tsarin rayuwar mata a Maroko ya tashi daga kashi 75.6 a 2010 zuwa shekaru 78.3 cikin 100 a shekarar 2020. Hoto: Brahimi Zidi.

"Burinmu shi ne mu ci gaba da gina kasar Maroko tare martaba darajarta, don haka, yana da matukar muhimmanci ga dukkan 'yan kasar Moroko maza da mata su taka rawar gani wajen samar da ci gaban da ake bukata," a cewar Sarkin yayin da yake gabatar majalisar dokokin kasar a shekarar 2022 bukatar samar da wannan doka.

Hanyar samar da ci-gaba

Shekaru kadan bayan hawansa karagar mulki a shekarar 1999, Sarkin ya kaddamar da wani gagarumin sauyi a kundin tsarin iyali, wanda kasashen duniya suka yaba da shi a matsayin wani gwaji na farko a yankin.

A cewar Hukumar Kula da tsare-tsare a Maroko (HCP), ilimin karatun mata a Maroko, da adadinsu ya kai kashi 50.3 cikin 100 na yawan al'ummar kasar a shekarar 2020, ya karu zuwa kaso 53.9 cikin 100 a shekarar 2019 daga kaso 39.6 cikin a shekarar 2004.

Adadin yara mata masu shekaru tsakanin 15 zuwa 17 da suka shiga makaranta ya kai kaso 90.5 cikin 100 a birane sannan kashi 39.2 cikin 100 a yankunan karkara a cikin shekarar 2020.

A ma'aunin kasa, tsawon rayuwar mata a lokacin haihuwa ya karu daga shekaru 75.6 a shekarar 2010 zuwa shekaru 78.3 a shekarar 2020.

A yankunan birane, ya kai shekaru 76.9, yayin da a yankunan karkara, ya kai shekaru 71.4.

Mata su ke kashi 50.3 cikin 100 na yawan al'ummar Morocco. Hoto: Reuters

Sauran mahimman bayanai dai sun yi nuni da cewa adadin mace-macen mata masu juna biyu ya ragu daga mata 112 cikin 100,000 masu rai a shekarar 2010 zuwa mata 72.6 da ke mutuwa a 2018 (111.1 a yankunan karkara sai kuma 44.6 a birane).

Ko da yake, duk da gagarumin ci gaban da tsarin da aka gabatar yake da shi a lokacin, wasu matsalolin da ke cikin tsarin sun kawo cikas ga ci gaban mata, kamar yadda aka tsara a cikin kundin tsarin mulkin Moroko wanda aka kafa a shekara ta 2011 bayan juyin juya halin Larabawa.

Hukumar HCP ta yi nuni da cewa shigar mata cikin kasuwar kwadago don a dama da su a shekarar 2020 yayi kasa, inda adadin ayyukan da suke yi ya tashi da kaso 19.9 idan aka kwatanta da kaso 70.4 cikin 100 na maza.

Bangaren noma shi ke kan gaba wajen baiwa mata ayyukan yi da kaso 44.8 cikin 100.

Kira don samun canji

Shekara guda bayan jawabinsa ga majalisar, kwanan nan Sarkin ya bukaci shugaban gwamnatin kasar da ya gaggauta gudanar da aikin tsarin, wanda ke da matukar muhimmanci wajen tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata ta fuskar hakki da wajibci, tare da kafa ma’aunin iyaka ga sauye-sauyen da za a samar.

Sarkin Morocco Mohammed na shida  ya ce ba zai saba wa koyarwar addinin Musulunci ba wajen gyara tsarin iyali. Hoto: Reuters

"A matsayina na Amir Al-Mouminin (VI), ba zan iya ba da izini ga abin da Allah Ya haramta ba, ko kuma haramta abin da 'Madaukakin Sarki' ya ba da izinin a yi, musamman kan batutuwan da nassosin Alkur'ani suka gabatar," in ji sarkin.

"Ta wannan fuska, mun himmatu wajen tabbatar da cewa an gudanar da wannan yunkurin na kawo sauyi daidai da manufofin shari'ar Musulunci tare da halayyar al'ummar Moroko," in ji shi.

Kundin tsarin iyali na yanzu ya kafa dokar shekarun yin aure da shekara 18, sai dai bangaren sashi na 20 na kundin ya yi ja kan wannan mataki bisa hujjar cewa "haka zai bude kofa ga yiwuwar cin zarafi."

A Maroko, mata suna da hakkin kada kuri'a daidai da na maza. Hoto: Brahimi Zidi

Dangane da auren mace fiye da daya, doka ta tanadar da wasu matakai kamar wajibcin samun izinin mace ta farko don namiji ya sake yin aure, ko kuma mijin ya bayyana dukkan abin da mallaka wanda zai iya rike mace fiye da guda.

Sannan dole ne mijin ya ba da tabbacin iya biyan bukatu da kuma samar da wurin zama ga matansa biyu daidai gwargwado.

Adawa mai karfi

Jam'iyyar adalci da ci gaba ta (PJD) a Moroko, karkashin jagorancin tsohon Firaminista Abdelilah Benkirane, tana adawa da shirin haramta auren mace fiye da daya da kuma manufar rabon gado.

Wata guda bayan kaddamar da tsarin sake fasalin kundin tsarin iyali, ra'ayoyi sun kasance a rabe kan sauye-sauye da dama da aka gabatar.

Abin farin ciki dai, alamu sun yi nuni da cewa an samu fahimtar juna wajen kawo karshen auren wuri.

Yayin da ba da izinin aure ya dan ragu a shekaru 10 da suka gabata, masu neman aure sun karu da sama mutane 27,000 , a cewar sabbin bayanai da aka fitar.

Ministan shari'ar Maroko Abdellatif Ouahbi, ya yi kira da a ''kawo karshen wannan matsala gabaki daya''.

TRT Afrika