Daga Dayo Yusuf
Wata na tara a kalandar Hijira, kalandar Musulunci ne watan da Annabi ya yi hijira daga Makka zuwa Madina, kuma wannann lokacin ne Musulman duniya su sama da biliyan 2.5 suke azumin Ramadhan.
Wata ne guda daya cif na yin aibadar azumi daga huduwar alfijir zuwa faduwar rana, ana gudanar da Ibada da addu'o'o.
Kamar yadda koyarwar Annabi Muhammad ta nuna, Ramadhan ba wai yana sanya Mu'uminai kara jin tsoron Allah a tunani da ayyukansu ba ne kawai. Albarkar wannan wata na karfafa jiki da zuciya, kamar yadda yake tsaftate ruhi.
Lokaci ne na kame kai, ibada da mika wuya, wanda ke kai wa ga murnar karfafar imani, kusantar iyalai da al'umma.
Ibadar watan azumi
Kamar yadda Alkur'ani ya bayyana, Azumi Ibada ce da aa wajabtawa dukkan Musumai.
"Ya ku wadanda kuka yi imani, an wajabta muku azumi, kamar yadda aka wajabta wa wadanda suka zo kafin ku, ko don kwa ji tsoron Ubangiji." Surah Al-Bakrah
A ra'ayin Malaman Musulunci, azumin Ramadhan na wajibi na alfanu sosai da mutum.
"Wannan wata ne da mutane ke rokon Ubangiji gafarar zunubansu. Amma kuma suna amfani da wannan dama wajen kyautatawa iyalai, abokai da al'ummar da suke zaune a cikin ta," In ji Shaaban Ismail, malamin Musulunci da ke zaune a Nairobi a yayin tattaunawa da TRT Afirka.
"Dole ne dukkan Musulmai baligai, in ban da wasu 'yan kadan, su yi azumin Ramadhan."
Shika-Shikan Musulunci
Azumi a watan Ramadhan na daya daga cikin shika-shikan Musulunci, wadanda dole kowanne Musulmi ya yi aiki da su.
Na farko shi ne aShahada', Shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu Manzon Allah ne.
Sai na biyu kuma Sallah biyar da ake yi a kowacce rana. Sai Azumin watan Ramashan, sannan bayar da Zakkah, da kuma zuwa Aikin Hajji ga wand aya samu iko.
Iyaye Musulmai na koya wa yaransu tun suna kanana yin azumi a watan Ramadhan kamar yadda Allah Ya umarta, yana d amanufar zama hanyar bunkasa ra yuwarsu ta fannoni daban-daban.
"Wadanda aka ce ba za su yi azimun Ranadhan ba su ne tsofaffi da yara kanana, da kuma wadanda suke yin rashin lafiyar da za a sa warkewar ta. Maimakon azumi, sai su ciyar d aabinci a tsawon watan," in ji Shaaban.
"Idan daya ya zama ya yi kasa ko ya yi tafiya, daukar cki, shayarwa ko zubar da jini, to duk wadannan an dauke musu yin azumin
Batun a fadade
Ba kame wa daga cin abinci da sha ba ne kadai watan Ramadhan. Ana bukatar Musilmi ya kame kansa dada bukatar jima'i. Ana kuma kiran Musulmai da su taimaka wa marasa karfi a wannan watan.
A bayyana yake karara cewa har wadanda ba Musulmai ba ma suna bayyana muhimmancin Ramadhan.
A duniya, wasu wadanda ba Musulmai ba na yi azumi tare da Musulmai a watan mai albarka - wasu saboda bin umarnin Ubangiji da ladabtar da kai, wasu kuma kawai suna yi ne sbaoda kyautayin d ake musu.
Shaikh Shaaban ya kara da cewa "Ana sa ran Musulmai su kame kansu daga duk wasu ayyuka na zunubi. Amma a lokacin wannan wata, suna ribanya ayyukan alheri tare da nisantar duk wasu ayyuka na sabo. Wannan na janyo zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al'umma."
Al'adar bude-baki ko karya kumallo bayan rana ta fadi a kowacce rana wani bangare ne na ibadu a watan na Ramadhan.
Mutane na yawan gayyatar abokai, 'yan uwa da makota zuwa su yi bude-baki tare da kayan abinci na musamman. Iftar a watan Ramdhan ba wai cin abinci ne kawai ba, igiya ce da ke kara kulla zumunci a tsakanin al'umma.