An taɓa gano wasu gawarwaki da aka cire wa wasu sassan jiki a wata babbar bola a Nairobi. Hoto: AFP

Daga Coletta Wanjohi

A watan Maris ɗin 2023 ne wani mutum ya je ofishin ‘yan sanda a Kenya cikin matuƙar damuwa don ya ba da rahoton ɓatan matarsa da ‘yarsa da ya ce ba a sake jin ɗuriyarsu ba tun halartar wani taro da suka yi a coci.

Ya shaida wa ‘yan sanda cewa ganin ƙarshe da ya yi wa matar da ‘yar tasa shi ne kafin su yi wani bulaguro daga Nairobi zuwa wani gari da ke cikin surƙuƙi don halartar taron addini da wani fasto mai suna Paul Mackenzie ya shirya.

Ƙoƙarin neman uwa da ‘yar ya janyo an kutsa har dajin Shakahola da ke cikin Gandun Dajin Tsavo East. An gano cewa Mackenzie yana gudanar da wata ƙungiyar asiri wacce ta yi sanadin ɓatan ɗaruruwan mutanen da ake kasa gano inda suke.

An gano ƙaburburan bai-ɗaya da yawa a cikin dajin mai girman eka 800 inda aka tono gawarwakin mutane 400.

Tuni wasu iyalan har sun gano gawarwakin danginsu ta hanyar yin binciken jini na DNA suka kuma sake yi musu sutura. Wasu kuwa har yanzu suna jiran jin labarin halin da ‘yan uwansu da suka ɓata ke ciki.

Mackenzie ya ci gaba da kasancewa a tsare, inda zai fuskanci wata doka mai tsauri da za ta sa ya fuskanci hukunci fiye da aika-aikar da ya yi ta Shakahola.

Ramadhan Rajab, babban mai fafutukar neman 'yancin fadin albarkacin baki a kungiyar Amnesty International ta Kenya, yana ganin akwai cikas na shari'a wajen tinkarar irin wannan lamari.

"Har yanzu Kenya na ci gaba da amincewa da Yarjejeniyar Kare Dukkan Mutane daga Bata (ICPPED) saboda haka, yana da wahala a gurfanar da mutane ko kuma a hukunta su kan tilasta ɓatan mutane," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

"A Kenya, ɓatan mutane bisa tilas ba laifi ba ne a bisa ka'ida, wanda za a iya tuhumar ku da shi har sai an gano gawar wanda ya ɓace. Ana ganin hakan ya bambanta da satar mutane, wanda kuma babbar matsala ce."

Dokoki

An amince da ICPPED a babban taron Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2006 kuma ta fara aiki a ranar 23 ga Disamba, 2010.

Yarjejeniyar ta bayyana cewa "kowace ƙasa za ta dauki matakan da suka dace a kan duk mutumin da ya aikata ko ya ba da umarni ko kuma ya jawo aiwatar da tilasta ɓatan mutane".

Kasashen Afirka da suka amince da ita sun hada da Burkina Faso, Cote d'Ivoire, Gabon, Gambia, Malawi, Mali, Mauritania, Najeriya, Nijar, Senegal, Afirka ta Kudu, Sudan da Zambia.

A Kenya, an zargi gwamnatocin da suka shude da rashin ƙarfafa tanadin doka don hanzarta gurfanar da su a shari’o’in da suka shafi bacewar da aka yi musu ba tare da tabbatar da satar mutane ba.

"Ba tare da wata fargabar samun saɓani ba, ba za a sake yin kisan gilla ba," in ji Shugaba William Ruto yayin wani taron coci a ranar 21 ga Afrilun bana.

Kasa da watanni uku bayan haka, a ranar 12 ga watan Yuli, kasar ta shiga cikin firgici a lokacin da aka tsinci gawarwakin wasu mata shida da aka jibge a wata shara a birnin Nairobi, lamarin da ya haifar da cece-ku-ce kan batun satar mutane da ɓatar da su.

Bayan kwanaki uku, ‘yan sanda sun kama wani mutum wanda suka ce ya amsa laifin kashe mata 42. A ranar 15 ga watan Agusta, rahotanni sun ce ya tsere daga ofishin ‘yan sanda inda yake tsare.

A Uganda, wata kasa ta Gabashin Afirka da har yanzu ta amince da ICPPED, mijin Sarah Damulira, John ya ɓata tun shekaru hudu da suka wuce.

"Mun ji labarin ɗauke shi aka yi, ina ta nemansa a gidan yari, ban samu ko da labarinsa ba," kamar yadda Damulira, wadda lamarin ya tilasta mata kula da ‘ya’yansu bakwai ita kadai, ta shaida wa TRT Afrika.

John ya ɓata ne a watan Nuwamban shekarar 2020, a dai dai lokacin da mawaƙin kasar Uganda Robert Kyagulanyi, wanda aka fi sani da Bobi Wine, ke yunkurin hambarar da Shugaba Yoweri Museveni.

Kungiyoyin kare hakki sun yi zargin bacewar John, daya daga cikin matsalar ɓatan mutane da ba a warware ba a Uganda, ko ta yaya na da alaka da siyasar lokacin.

Gagarumar matsala

Bisa kididdigar da kungiyar agaji ta Red Cross ta yi, sama da mutane 71,000 a fadin Afirka ne aka yi wa rajista a matsayin waɗanda suka ɓata, inda aka samu ƙari zuwa kashi 75 cikin 100 daga adadin shekarar 2019.

Wasu abubuwan da ke da alhakin hakan su ne rikice-rikicen da aka dade a sassan nahiyar da bala'o'i, da sauyin yanayi.

Mutane da dama, musamman daga kasashen yankin kusuwar Afirka, sun ɓata yayin da suke kasadar tafiye-tafiye ba bisa ka'ida ba zuwa kasashe daban-daban domin neman abin rayuwa mai kyau da inganci.

"Batun mutanen da suka ɓata, ya kasance daya daga cikin yanayi mafi lalacewa da dadewa sakamakon rikice-rikice na makamai da sauran yanayi na tashin hankali.

Wannan yana sa matukar damuwa a zuƙatan iyalai da dangin waɗanda suka ɓata," in ji Patrick Youssef, daraktan kungiyar agaji ta Red Cross a Afirka.

Hukumar kare hakkin ɗana’dam ta Afrika ta bi sahun sauran hukumomin kasa da kasa domin yin kira da a dauki matakin kawo karshen wannan annoba.

"Muna sabunta haɗin gwiwarmu ga wadanda aka ɓatar da su bisa tilas, da kuma kungiyoyi, da ma masu kare hakkin ɗan’adam da lauyoyin da ke goyon bayansu," in ji wata sanarwar hadin gwiwa.

Yin abin da ya dace

A daidai lokacin da duniya ke bikin ranar wadanda ake ɓatar da su bisa tilas a ranar 30 ga watan Agusta, hukumomin kare hakkin bil'adama sun bukaci kasashen Afirka da su shiga babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan batun, wanda aka shirya gudanarwa tsakanin 15-16 ga watan Janairun 2025, a Geneva na kasar Switzerland.

Taron zai nemi, a tsakanin sauran batutuwa, inganta amincewa da ICPPED na duniya. "Tabbatar da taron ya samar da damar samar da dokokin cikin gida don magance wannan matsala," in ji Ramadhan.

"Ga wadanda abin ya shafa, tilast bacewa azabtarwa ce da kuma tsoratarwa. Ga iyalansu, abin takaici ne, wanda ba zai taɓa ɓacewa daga zuƙatansu ba."

TRT Afrika