Opec ta ce yawan ɗanyen fetur din da Nijeriya ke samarwa ya ƙaru

Yawan danyen fetur din da Nijeriya ke samarwa a duk rana ya ƙaru da ganga 152,000 kullum a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, kamar yadda sabbin bayanan da Ƙungiyar Ƙasashen da Suka fi Samar da Fetur ta Duniya, OPEC ta fitar suka nuna.

Bayanan na OPEC MOMR na watan Disamban 2024 sun ce fetur din da kasar ta samar sun haɗa da ƙaruwar da aka samu ta kashi 11 cikin 100 daga gangar mai miliyan 1.333 da ta fitar a watan Oktoban 2024 zuwa ganga miliyan 1.486 a watan Nuwamba.

Bayanan sun nuna cewa ƙarin da aka samu duk rana ya kai ganga 152,000 kuma daga tsakanin Oktoba da Nuwamba kawai an samu ƙarin kusan ganga miliyan ɗaya.

Waɗannan sabbin bayanai na zuwa ne lokaci kaɗan bayan da hukumar kula da samar da fetur ta ƙasar (NUPRC) a rahotonta na Disamban da ya gabata ta ce an samu raguwa a fitar da fetur da ƙasar ke yi da kashi 1.35% daga ganga miliyan 1.690 da ake samarwa duk ranar a watan Nuwamban 2024 zuwa ganga miliyan 1.667.

Wasu bayanan hukumar NUPRC sun kuma nuna cewa yawan man da aka samar a Disamban 2024 ya kai ganga miliyan 1.79 yayin da mafi ƙaranci shi ne ganga miliyan 1.57.

A jumlace yawan man da aka samar a Disamban 2024 shi ne ganga miliyan 51.69, inda aka samu ƙrin kashi 1.9 cikin 100 idan aka kwatanta da ganga miliyan 50.71 da aka samar a Nuwamban 2024.

TRT Afrika