Daga Kudra Maliro
Shekara daya bayan Jamhuriya Dimukradiyyar Congo ta samu amincewar shiga kungiyar Raya Gabashin Afirka, ‘yan kasuwa a kasar sun yi tsammanin samun damar shiga kasashen Afirka shida cikin faraga. Amma ba a samu wani sauyi ba har yau.
Kambale Makolongo, wani dan kasuwa ne a Jamhuriya Dimukradiyyar Congo. Ya bayyana yadda ya ji bayan samun labarin kasarsa ta shiga Kungiyar Raya Gabashin Afirka ta East African Community (EAC), a matsayin mamba ta bakwai.
A 2019 ne Congo ta nemi shiga kungiyar, tare da fatan inganta dankon ciniki da siyasa tsakaninta da makwabtanta na yankin gabashin Afirka.
A watan Maris na 2022, an amince da Congo ta zamo mambar EAC, wanda ke nufin mutanen kasar su miliyan 90 za su samu damar zirga-zirga cikin sauki, da kasuwanci a sauran kasashe shida mambobin kungiyar.
Hakan kuma na nufin kasuwanci zai samu karin hanzari da sauki, da rangwamen farashi, sakamakon fadadar harkokin kasuwanci tsakanin mambobin kungiyar.
Sai dai kuma shekara daya bayan nan, har yanzu Kambale yana biyan dala 45 don gwajin Covid, da kuma dala 50 don samun bizar shiga kasashen mai wa’adin wata uku.
Kambale ya fada wa TRT Afrika cewa, “Ina tafiya sau uku ko hudu tsakanin Congo zuwa Uganda, ina kashe kamar dala 300 a biyan kudin biza kawai. Idan biza ta zamo kyauta gare mu, wannan dala 300 za ta taimaka min na sayi wata hajar.”
Wata majiya daga hukumar kungiyar EAC ta sanar da cewa dole sai Majalisar Dokokin Congon ta amince da dokoki da tsare-tsaren EAC, kafin su fara aiki kan Congon.
Sakamakon haka, ‘yan Congo da ke son tafiya zuwa kowace kasa cikin mambobin kungiyar EAC ba tare da biza ba, za su jira wani lokaci yayin da ake kammala shigar da kasar cikin EAC. Hakan zai iya daukar watanni da yawa, har zuwa shekara guda.
Amma kuma kasar Sudan ta Kudu ta dauki watanni hudu kacal ne kafin ta zamo cikakkiyar mambar kungiyar EAC, bayan ta rattaba hannu kan yarjejeniyar shiga kungiyar a watan Afrilun shekarar 2016.
Haka ma wani dan kasuwar, Maguy Mundeke, ya ce direbobi da yawa da ke zuwa daga Uganda ko Kenya ko Tanzaniya, suna fuskantar kalubale daban-daban da suka hada da bin layi don samun bizar shiga Congo.
Wannan yakan janyo musu jinkirin kwanaki da yawa kafin a ba su izinin shiga da kayansu iyakar kasar. Sannan sukan kashe kudi wajen fakin motocinsu da kuma ajiyar kayansu a ma’ajiya.
Maguy Mundeke ya ce “Hajojina sukan kwashe kwanaki a bakin boda yayin da nake jiran samun izinin shiga. Da a ce mun sami ikon shiga kyauta, da na samu saukin kashe kudade, kuma da kayan nawa sun yi rahusa a kasar Congon.
Da yawan ‘yan Congo da TRT ta zanta da su sun nuna fatansu na ganin kungiyar Raya Gabashin Afirka ta rungumi harshen Faransanci, a matsayin daya daga harsunan amfani a kungiyar.
Hakan zai taimaka wa ‘yan Congo masu jin Faransanci su samu saukin hadewa da sauran jama’ar kungiyar.
Sai dai kuma, hadewa da kasa mai girman iyaka, kuma mara cikakken tsari kamar Congo, wani kalubale ne babba ga kungiyar ta EAC.
Akwai wasu karin kalubale da sauran kasashen EAC suke jajantawa, kamar na rashin ababen cigaba, da kuma musammar matsalar tsaro.
A fahimtar masana kan harkokin cinikayya, ababen cigaba a shingayen shiga kasar Congo ba su wadatar ba, musamman idan aka kwatanta da na sauran kasashe makwabta.
Bugu da kari, ana bukatar a inganta hanyoyin shiga manyan biranen Congo, saboda a yanzu suna cikin yanayi mara kyau matuka.
A zantawarsa da TRT Afrika, Farfesa Solomon Asimwe, wani mai sharhi kan tsaro da siyasa a Afirka, ya ce kasashen gabashin Afirka suna amfani da sabbin katin shaida na zamani, a wajen ketarawa iyakokinsu, wadanda kasar Congo ba ta da irin tsarin zuwa yanzu.
Kenan har yanzu kasar Congo tana bukatar jiran lokaci kafin a ba ta damar shiga kasashen ba tare da biyan kudin biza ba.
Farfesa Asimwe ya kara da cewa, “Tsorona shi ne sauran kasashen suna tararrabin yanayin tsaro a Jamhuriyyar Dimukradiyyar Congo, saboda har yanzu akwai rashin tabbas a kasar.
A ra’ayina, an yi gaggawa wajen shigar da kasar Congo cikin kungiyar EAC, saboda akwai bukatar kasar ta dauki mataki kan wasu matsalolinta na cikin gida, kamar na tsaro, da ‘yancin bayyana ra’ayi, da batun rashawa da kuma cikakken tsrin dimukradiyya.”