Uganda da wani kamfanin Turkiyya sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar gina layin dogo mai tsawon kilomita 272 a ranar Litinin, wanda ke nuna wani muhimmin mataki na inganta ababen more rayuwa a gabashin Afirka.
Ana sa ran layin dogo wanda aka tsara don inganta saurin gudu da kuma jigilar kaya, ana sa ran zai karfafa alakar Uganda da hanyoyin kasuwanci a yankin, gami da tashar ruwan Tekun Indiya ta Mombasa.
Babban Sakatare na Ma'aikatar Ayyuka ta Uganda Bageya Waiswa da mataimakin shugaban kamfanin Yapi Merkezi Holdings Erdem Arioglu ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a Kampala.
Ministan Ayyuka da Sufuri na Uganda, Janar Edward Katumba Wamala, da jakadan Turkiyya Fatih Ak na daga cikin jami'an da suka halarci taron.
Bageya ya ƙara da cewa, shirin na Standard Gauge Railway (SGR) zai taimaka wajen rage farashin sufuri da saukaka kasuwanci a fadin yankin.
Ƙwarewar Turkiyya
Sabon layin dogo wanda zai taso daga kan iyakar Malaba da Kenya zuwa Kampala babban birnin Uganda, ana sa ran zai samar da sufurin kaya cikin sauri da inganci fiye da tsarin da ake amfani da shi na ma'aunin mita da ake amfani da shi a halin yanzu.
Da farko an ba kamfanin China Harbor Engineering kwangilar gina layin dogo amma bayan shafe shekaru takwas ana jinkiri, Uganda ta koma Yapi Merkezi domin fara aikin.
Jakadan Turkiyya Ak ya jaddada aniyar Turkiyya na amfani da gwanintarta ta gina layin dogo don taimakawa zamanantar da layin dogo na Uganda.
Kamfanin gine-gine na Turkiyya Polat Yol Yapi yana aiki a Uganda, yana aikin hanyar Muyembe-Nakapiripirit, wanda zai hada Uganda zuwa Kenya, Sudan ta Kudu, da Habasha.
Da yake magana da Anadolu, karamin jakadan kasar Uganda a Istanbul, Levent Davisoglu, ya jaddada muhimmiyar rawar da Uganda ke takawa a matsayin mai hadewa a yankin gabashin Afirka.