Wani babban jami’in Kwastam ya yanke jiki ya fadi ya mutu a yayin da ake tsaka da sauraron bin bahasi a Majalisar Wakilan Nijeriya.
Mai magana da yawun majalisar Wakilan, Akin Rotimi a wata sanarwa ya ce lamarin ya faru ne bayan da babban jami’in Kwastam din ya shiga wani yanayi na rashin lafiya a lokacin.
Jami'in mai muƙamin Mataimakin Konturola ne, kuma ana cikin sauraron bin bahasin ne sai ya fara tari inda aka yi maza aka garzaya da shi asibitin dake cikin majalisar inda a can aka tabbatar da mutuwarsa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A cikin bakin ciki muke tabbatar da rasuwar wani babban jami’in hukumar Kwastam ta Nijeriya wanda ya je Majalisar Dokokin kasar domin tattaunawa da wani kwamitin majalisar.
“Ana tsaka da tattaunawar ne da misalin karfe 1:00 na rana a ranar Talata, 25 ga Yuni, 2024, kwatsam sai jami’in ya samu matsalar rashin lafiya. Duk da kokarin gaggawa da ma'aikatan jinya suka bayar a asibitin majalisar dokokin kasar, amma abin takaici ya rasu.
"Saboda mutunta iyalansa, ba za a bayyana sunan jami'in ba a wannan lokacin.
“Majalisar Wakilai tana mika sakon ta’aziyyarta ga ‘yan'uwa da abokan arziki da abokan aikin marigayin a wannan mawuyacin lokaci. Mun san irin gagarumar gudunmawar da ya bayar ga Hukumar Kwastam ta Nijeriya da kuma al’ummarmu.
"A shirye Majalisar wakilai take don tallafa wa kokarin fahimtar yanayin da lamarin ya faru kuma za ta ba da cikakken hadin kai tare da duk hukumomin da abin ya shafa don tabbatar da bin duk ka'idojin da suka dace."