Ministar Kudin Zainab Ahmed ta ce gwamnati tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan lamarin/ HOTO: Reuters

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta samo bashin dala miliyan 800 don saka wa a tsarin tallafi na rage radadin cire tallafin mai da za a yi a cikin watan Yunin shekarar 2023.

Da take amsa tambayoyi daga manema labarai bayan an gama zaman majalisar zartarwar kasar ranar Laraba, Ministar Kudi, Zainab Ahmed ta ce za a raba kudi ga iyalai miliyan 10, wadanda bayanansu ke hannun gwamnati a fadin kasar.

Ta ce iyalai miliyan 10 din da za su amfana da tallafin, suna wakiltar ‘yan Nijeriya miliyan 50 ne.

“Ya kamata mu samu karin kudin don mu iya yin abin ya fi raba wa mutane kudi kawai, kuma a cikin tattaunawarmu da masu ruwa da tsaki a lamarin abubuwan da za mu yi sun wuce raba kudi kawai,” in ji ministar.

Ta ce kungiyar kwadagon kasar za ta iya fara tunani kan yadda za ta samar wa mabobinta motoci masu daukar mutane a saukake.

Nijeriya na kashe biliyoyin daloli kan tallafin mai duk shekara don 'yan kasar su samu man fetur a farashi mai sauki/Hoto Reuters

A makon da ya gabata ne Ministan Kwadagon kasar, Dr Chris Ngige ya ce gwamnati za ta bar maganar rage radadin cire tallafin mai wa gwamnati mai jiran gado.

Yawancin ‘yan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata a Nijeriya ciki har da Bola Tinubu da ya yi nasara, sun yi alkawarin cire tallafin mai idan suka hau mulki.

TRT Afrika da abokan hulda