Kamala Harris tana ziyayar mako guda a Afirka/Photo AA

Mataimakiyar Shugaban Amurka, Kamala Harris, ta ce za ta yi kokari wajen bunkasa zuba jari a nahiyar Afirka.

Kamfanin dillacin labaran Ghana ya ruwaito Kamala Harris jim kadan bayan ta sauka a Ghana tana cewa “ina son aiki na ya mayar da hankali kan kara zuba jari a cikin nahiyar nan, da habaka cigaban tattalin arziki tare da samar da dama”.

Ziyarar da ta kai Ghana zango daya ne a cikin ziyarar mako guda da take yi a wasu kasashen Afirka, ciki har da Zambiya da Tanzaniya, wadda ake ganin tana yi ne domin dakile karfin tattalin arzikin China a Afirka.

Kasar China ta zuba jari kan ababen more rayuwa a Afirka cikin ‘yan shekarun nan, yayin da karfin fada aji na kasar Rasha ke karuwa a cikin nahiyar ta fuskar soji.

Ta yaya masana ke kallon wannan ziyarar ta mataimakiyar shugaban kasar Amurka?

Jibrin Ibrahim, babban jami'i a cibiyar nazarin dimokradiyya da cigaba da ke birnin Abuja a Nijeriya, yana ganin tsoro ya sa Amurka take neman kawance a Afirka.

“A yanzu Amurka ta gane cewar babu tabbas kan karfin da take tunanin tana da shi a duniya,” a cewarsa. "Domin China tana samun cigaba ta fannin harkar kasuwanci da kasashen Afirka da kuma wasu kasashen duniya."

Shugaban Amurka, Joe Biden, ya ce zai ziyarci Afrika nan gaba/Photo AA

Ya shaida wa TRT Afirka cewar yana ganin Amurka na neman kawance ne domin: “Rikicin Yukrain da Rasha ya sa Amurka ta gane cewar zatonta cewar kasashen Afirka za su bi bayanta ba shi da tushe.”

Ya kara da cewar wannan ya fito fili a lokacin da kasashen Afirka suka ki fitowa su soki Rasha kan yakin Yukrain.

“A wannan yanayin ne Amurka take zawarcin kawaye a Afirka kuma take neman shawo kansu domin su kasance masu mara wa Amurka baya,” in ji Jibrin Ibrahim.

Ya ce yanayin yadda tattalin arzikin duniya ke tafiya ya nuna cewar lokacin da Amurka kadai ke da karfin fada a ji a duniya ya wuce.

Ta yaya ziyarar ta Kamala Harris za ta amfani ‘yan Afirka?

Duk da kasancewar shelar kara zuba jari a Afirka da Kamala Harris ta yi wata dama ce ga ‘yan Afirka, Dr Patrick Opo Asuming, babban malami a fannin nazari a kan kudi na Jami’ar Ghana ya ce cin gajiyar shirin na Amurka ya danganta game da irin shirin da kasashen Afirka ke da shi.

“Dole mu fahimci cewar ta zo Afirka ne domin ta tallata hajar Amurkawa kuma ta nema wa kamfanonin Amurka karin damarmaki a nahiyar Afirka,” a cewar Dakta Asuming a hirarsa da TRT Afrika.

Ya ce hakan ka iya zama damar samun alfanu ga kasashen Afirka, amma hakan ya danganta ne game da “ko muna da wasu dabarbaru na kasuwanci da Amurkawa,” in ji Asuming.

Alal misali, malamin ya ce an dade da kadaddamar da shirin AGOA wanda ya sa Amurka ta bai wa amfanin gona daga Afirka fifiko wajen saya, amma kasashen Afirka ba su yi amfani da wannan damar ba wajen bunkasa fitar da kayayyakinsu zuwa Amurkan.

Ya ce zai fi kyau idan kasashen Afirka za su hada kai wajen fitar da dabarar tinkarar wannan shelar da Amurka ta yi saboda nahiyar ta samu alfanu mai yawa daga shirin na Amurka.

Ya kara da cewar idan aka samar da dabarar tinkarar kasashe masu karfin tattalin arziki da ke son kulla kawance da kasashen Afirka,‘yan nahiyar za su samu alfanun cudanyar kasashen masu zawarcin Afirka.