Hukumar da ke Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya NERC ta bukaci ‘yan kasar da ke amfani da na’urar tantancewa da kuma biyan kudin wutar lantarkinsu da su sabunta na’urar kafin zuwan watan Nuwamba na shekarar 2024.
Hukumar ta ce, idan masu amfani da na’urar ba su sabunta mitarsu ba kafin ranar da aka kayyade, ba za su iya samun damar loda kudin caji a na’urar mitarsu ba.
A sakon da hukumar ta wallafa a shafinta na X, wanda aka fi sani da Twitter, ta ce ba za a caji wasu kudade ba daga duk wanda ya sabunta na’urar ta mita a yanzu.
Kazalika NERC ta ce kamfanonin rarraba wutar lantarki a Nijeriyya(DisCos) za su fara ba da lambobin da za a yi amfani da su wajen sabunta naurar.
"Idan kuna da mita, to yanzu lokacin da ya kamata ku sabunta ta," a cewar sakon.
Hukumar ta kara da cewa sabuntawar, ba zai shafi sauran kudin da aka loda a cikin na'urar ba.
Ta kuma shawarci masu amfani da su nau'rar da su tuntubi Kamfanonin rarraba wutar lantarki da ake da su a Nijeriya don karin bayani game da wannan mataki.