NCC ta ce ''duk da cewa ƙarin da aka yi, ya yi ƙasa da buƙatar samun kaso sama 100 da wasu kamfanonin sadarwa suka nema / Hoto: Wasu

Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta amince da ƙarin kashi 50 cikin 100 na kuɗaɗen kamfanonin sadarwa a ƙasar, wanda shi ne na farko da aka yi a kusan shekaru goma sha ɗaya.

NCC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin wadda ke ɗauke da sa hannu mai magana da yawunta, Reuben Mouka.

Ta ce ta bayar da izinin ƙarin ne bisa ga ikon da take da shi ƙarkashin sashe na 108 na dokar sadarwar ta Nijeriya ta 2003 (NCA).

Hukumar ta ce dokar ta ba ta damar daidaitawa da kuma amincewa da farashi da kuma ƙarin kuɗaɗen sadarwa na kamfanoni bisa ga buƙatu na yanayin kasuwa.

Sanarwar ta ce ''duk da cewa ƙarin da aka yi, ya yi ƙasa da buƙatar samun kaso sama 100 da wasu kamfanonin sadarwa suka nema, an yi shi bisa la'akari da sauye-sauyen masana'antu da za su yi tasiri wajen ɗorewar ayyuka".

Tun daga shekarar 2013 ba a yi ƙarin farashin kiran waya ba a Nijeriya, duk da ƙarin tsadar gudanar da ayyukan yau da kullum da kamfanonin sadarwa ke fuskanta, a cewar sanarwar ta hukumar NCC.

“Waɗannan gyare-gyaren za su ci gaba da kasancewa cikin ƙa’idojin jadawalin kuɗin fito da aka gindaya a shekarar 2013, kuma za a sake duba buƙatun hakan bisa ga ƙa’ida bisa ga tsarin hukumar,'' in ji sanarwar hukumar tana mai ƙari da cewa ''za a aiwatar da wannan umarni ne bisa ga tsarin ƙarin ƙudaden sadarwa na NCC da aka fitar a 2024.''

TRT Afrika