Hukumar Kwastam ta ce ta daƙile ƙoƙarin fasa-ƙwaurin lita miliyan 2.93 ta fetur daga Nijeriya.
A sanarwar da ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata, Kwastam ta ce yawan fetur ɗin ya kai adadin man da ake kai wa jihohin ƙasar shida na tsawon wasu kwanaki.
Sai dai Kwastam ba ta yi ƙarin bayani a kan tsawon lokacin da ta ɗauka wajen daƙile fasa-ƙaurin da kuma inda za a kai man ba.
Amma ta ce yawan man ya kai wanda ake kai wa jihohin Zamfara na tsawon kwana huɗu, da Jigawa tsawon kwana tara da Borno tsawon kwana uku da Gombe na tsawon kwana huɗu da Filato tsawon kwana uku da Ekiti kwana tara da kuma Imo kwana biyu.
TRT Afrika