Kungiyoyin ma'aikata daga Asiya da Turai sun kaddamar da kungiyar a taron Istanbul

Kungiyoyin ma’aikata daga Asiya da Turai sun hada hannu waje guda tare da kafa Tarayyar kwadago ta Kasa da Kasa.

An kafa wannan gamayya ta kungiyoyi a ranar Juma’a a wajen taron da aka gudanar a İstanbul. Kungiyar ta kunshi Kungiyoyi 33 daga kasashe 25 wanda suke wakiltar sama da lebrori miliyan 25 a Asiya da Turai.

Tana da manufar samar da wani dandali ga kungiyoyin ma’aikata da zai dinga fitar da amonsu game da batutuwan da suka shafi ‘yan kwadagon a fagen kasa da kasa ta hanyar bayar da hadin kai daga mambobi.

Ministan Kwadago na Turkiye Vedat Bilgin a yayin bude taron ya bayyana cewa “Tsarin jari hujja mara kyau dake girmama na rusa dan adam, na lalata rayuwar ma’aikata. Rikicin da ya biyo bayan annoba ya nuna karara tsarin jari hujja ba mai dorewa ba ne.”

Ya kara da cewa, wannan gamayya ta kungiyoyi na bayar da misalin falsafar “Duniya ta fi biyar girma” wadda Shugaban Kasar Turkiye Recep Tayyip Erdogan ya kawo don suka ga tsarin da duniya take tafiya a kai yau, tare da neman a tafi tare da kowanne bangare.

AA