Kanye West zai sayi dandalin sada zumunta na zamani na Parler

Kwanan nan aka toshe shafin West na Twitter da Instagram saboda karya dokokin aiki da su bayan ya yada bayanan nuna kyama ga Yahudawa.

Idan West ya mallaki Parler hakan zai ba ta damar jya akalar shafin yanar gizo da zai ba shi ‘yancin bayyana ra’ayinsa a shafin sada zumunta ba tare da wani ya tantance mai zai yada ba. Amma abun tambayar shi ne wa zai surara?

Ko a tsakanin shafuka da manhajojin sadarwar zamani dake goyon bayan ‘yancin fadar magana ba tare da tsangwama ba, ba a cika samu a Parler ba, kuma mafi yawanci dattijai dakeson tattaunawa kan siyasa ne suke hawan sa, babu wani tsari na fadada shi da zai sanya shi gogayya da sauran manyan shafukan sadarwa na zamani.

Idan mamallakin Tesla Elon Musk ya ci gaba da yunkurin sayen Twitter, abbuwa na iya zama masu rikitarwa sosai ga Parler. Saboda Musk ya riga ya bayyana zai rage tsauraran dokokin Twitter, da tantance abubuwan da ake yadawa, zai ma dawo da shafin tsohon Shugaban Kasar Amurka Donald Trump. Idan mutanen da suke ganin an matsa musu wanda hakan ya sanya suka bar Twitter zuka ga yanzu dama ta samu, an rage dokoki, an dawo da shafin Trump, to shafuka irin su Parler, Gad da wasun su za su rasa mabiya.

Kamfanin Parlement Technologies da ya mallaki Parler, da West a ranar Litinin sun bayyana mallakar kamfanin za ta tabbata a watanni uku na karshen shekara, amma kuma ba a bayyana farashi da sauran bayanai ba. Parlenement Technologies ya bayyana yarjejeniyar ta hada da amfani da ma’ajiyar bayanansa da kayayyakin amfaninsa na gajimare.

A watan da ya gabata ne Parler ya sauya fasalin kasuwancinsa don kafa Parlement Technologies, wanda suka ce na da manufar zama “dandalin da ya fi kowanne bayar da ‘yancin magana ba tare da tsangwama ba a duniya”.

Hakan na nufin maimakon gudanar da dandali guda daya kamar Parler, kamfanin na son samar da aiyuka ga sauran shafukan sadarwar yanar gizo da ake kallon suna da tsauri kuma sauran kamfanunnuka ba za su agaza musu ba. Kakakin Parlement ya ce, a lokacin da aka sauya fasalin kamfanin ba a ma fara maganar sayar da ahsi ga West ba, kuma aiyukan biyu daban suke da juna.

An hana Ye yada bayanai a Twitter da Instagram na mako guda saboda yada kalaman nuna kyama ga Yahudawa da mahukuntan shafukan suka ce ya sabawa ka’idojin amfani da su. A wani sakon Twitter, Ye ya ce nan da wani lokaci zai je “death con 3 JEWISH PEOPLE,”, bayanan yanar gizo na bayyana cewa yana nufin shirin ma’aunin yanayin dakarun tsaron Amurka da ake kira DEFCON.

Ye ya kuma bayyana cewar bauta zabi ne, ya kuma kira allurar riga-kafin Corona da “alamun jakai”. A farkon wannan watan, an soke shi kan yadda ya sanya rigar dake dauke da rubtun ‘Whites Lives Matter’ (Rayuwar Farare na Muhimmanci) a wajen Taron Makon Sutura na Paris.

Candace Owens kuma, baya ga zama mai tsaurin ra’ayi, mai mabiya da yawa dake auren Shugaban Kamfanin ‘Parlement Technologies’, George Farmer, mace ce da ta bayyana tare da West ita ma sanye da rigar dake dauke da rubutun ‘Whites Lives Matter’ (Rayuwar Farare na Muhimmanci), abun da ya janyo tayar da jijiyar wuya.

A wata sanarwa da Ye ya fitar ya fadi cewa “A duniyar da ra’ayin masu ra’ayin rikau ke zama mai rikitarwa, dole ne mu tabbatar ‘yancin fadin maganganun da muke s.”

Parler ya yi gwagwarmaya a tsakanin gogayya da shafukan masu ra’ayin rikau kamar shafukan Truth Social, wadanda kanana ne msamman idan aka kwatanta su da sauran shafukan sadarwa na zamani. Parler na da masu amfani kamar 725,000 a kowanne wata a Amurka a farkon wannan shekarar, kamar yadda shafin Data.ai ya sanar, wadanda suke bibiyar amfani da manhajojin wayar hannu. Wannan kasa ne da mutane miliyan 5.2 a rabin shekarar 2021. Idan aka hada da masu amfani dake wajen Amurka, Parler na da sama da mutane miliyan guda.

Truth Social na da masu amfani miliyan 2.4 a wata a wannan lokaci, duk da an kaddamar da shi a watan Fabrairu kuma a kan shagon sayayya na Apple kawai, kamar yadda Data.ai ya sanar. Kamfanin mai binciken kasuwanni ya ce wani shafin mai suna Gettr wanda aka kaddamar a watan Yulin 2021, na gaba da Parler da Truth Social da kusan mutane miliyan 3.8 dake amfani da shi a kowanne wata.

Babu wanda daga cikinsu ya kusanci Twitter, wanda ya bayar da rahoton suna da masu amfani kullum da suka kai miliyan 237.8 a watanni 3 na karshen nan. An samu shafuka da yawa da suka samu don kalubalantar dokokin takaita yada bayanai da shafuka irin su Twitter da Facebook suke kawowa, amma ba su kai su yawan mabiya ba kuma.

Wani bangare na wannan dalilin shi ne yadda mafi yawan mutane ba sa son tattauna siyasa a yanar gizo. Cibiyar Binciike ta Pew ta ce, daya bisa uku na sakon Twitter da ake fitarwa a Amurka sun shafi siyasa, amma wasu ‘yan kalina na mtane ne suke fitar da su, wadanda mafi yawan su tsofaffi ne.A lokacin matasan Amurka masu shekaru 50 zuwa kasa suke kaso 24 na masu amfani da Twitter a kasar, su suke aikewa da kaso 80 na sakonnin siyasa ta shafin, in ji Pew. Wadannan mutanen da Ye ya kamata ya yi zawarci, matukar yanason habaka Parler.

Parler da aka kaddamar a watan Agıstan 2018 amma bai fara mikewa ba har sai 2020.

A watan Janairun 2021 ne ya bayyana yanar gizo saboda rawar da suka taka wajen mamayar Capitol a Amurka. Wata guda bayan wannan harin, Parler ya sanar da sake kaddamarwa.

A watan da ya gabata kum, Google ya baiwa Parler damar dawowa shagonsa na Play Store, sama da shekara guda bayan hana shi shiga shagon.

Mai gogayya Truth Social --- wanda Trump ya kaddamar bayan an hana shi amfani da Twitter sabod aabun da ya faru a Capitol, -- ya samu damar shiga shagon Google a kasuwar Play Store, makonni kafin zabukan tsakiyar zango.

Shugaban kamfanin ‘Parlement Technologies’ Gerge Farmer ya bayyana cewa “Wannan yarjejeniya za ta sauya duniya, chanji da zai sanya duniya tunani game da ‘Yancin magana da bayyana ra’ayi.”

A lokacin da hakan ke faruwa, Shugaban Tesla Elon Musk ya aike da wani sakon barkwanci dake nuna shi tare da West suna hada shafukansu don aiki tare inda ya bawa hoton nasu taken “Ku daka ce shi” da kuma “Lokacin raha na nan tafe”.

Musk na ci gaba da kokarin sayen Twitter da biliyoyin daloli, bayan ya yi kokarin janyewa daga wannan kudiri, amma dai bai janye ba har yanzu.

Tsohon Shugaban Kasar Amurka Donald Trump, da aka dakatar da shi daga amfani da Twitter saboda fitar da sak0on dake zuga mutane su yi hayaniya,

Musk is proceeding with his $44 billion deal to buy Twitter after trying to back out of the contract, but it has yet to close. Ya tattauna da West game da sayen Parler da kuma shirin su ci abincin dare tare, kamar yadda shafin yanar gizo na mai yada labaran siyasa Politico ya bayyana.

Parler, wanda ya bayyana kansa a matsayin “mai nusarwa wajen yaki da Manyan Kamfanunnuka, Manyan gwamnatoci, tantance sakonni da adawa da al’adu marasa kyau”, a watan Satumba ya sanar da zai sauya fasalin mayar da hankali kan masu amfani da akewa barazanar fatattaka daga sahar yanar gizo.

TRT Afrika da abokan hulda