Bayan wani bincike aka gudanar, Hukumar Kula da Gogayya ta Rasha dake yaki da zamba ta ci tarar kamfanin Google sama da dala miliyan 160, sakamakon yadda yake amfani da damar da yake da ita a kasuwanni ba bisa ka’ida ba kan manhajojin wayoyin hannu.
Manhajar kamfanin dake California ce ta mamaye dukkan wayoyin hannu masu amfani da Android da ake amfani da su a Indiya da kaso 95, kamar yadda wani bincike da aka gudanar ya fitar.
Amma Hukumar Gogayya ta Indiya ta ce Google ya yi wasu dabaru a dandalin yanar gizo don wuce abokan hamayyarsa ba bisa ka’ida ba, da suka hada da YouTube da sahar bincike ta Chrome.
Sanarwar da Hukumar ta fitar ta ce Android na da manhajpojin Google da aka sakko da su a kan wayoyin hannun mutane a suka hada da sahar bincike ta kamfanin, wadda ke bayar da gogayya babba a tsakanin su da abokan hamayyarsu.
Sanarwar ta kara da cewa “Ya kamata a yi gogayya da kwarewa, kuma ya kamata Google ya sani gogayyarsa ba ta bisa wanan turba.”
Karfafar na’urorin dake amfani da Android
Hukumar ta bayyana cin Google tarar rupee biliyan 13.4 (Dala miliyan 162) tare a umartar kamfanin da kar ya sake tursasawa masu amfani da Android sauko da manhajojinsa.
Haka zalika ta fadawa Goggle da kar ya kulla wata yarjejeniya da masu samar da wayoyoin hannu na zamani da za su zaburar da su kan su sayar da manhajojin Android kadai ko kuma su ne kawai za su yi amfani da manhajojinsu.
Indiya ce ke da mafi yawan masu amfani da wayoyin hannu na zamani a duniya bayan China.
A shekarar 2021 kasuwar wayoyyin hannu na zamani na Indiya ta habaka da kaso 27 shekara bayan shekara, inda a shekara aka sayar da sama a kwara miliyn 169, kamar yadda Hukumar ta bayyana.
Sama da kaso 60 na wayoyin hannu da aka sayar a kasar sun fito ne daga masu samar da wayoyin hannu na China da suka hada da Xiomi da Oppo.
Apple ya zama mara taka rawar gani wajen kasafin kudi, amma ya dan samu shigaa ‘yan shekarun nan, kuma kamfanin ya sanar da shirinsa na samar da Iphone 14 a cikin gida.