Ma'aikatan sufurin jiragen sama a Kenya za su tafi yajin aiki saboda shirin Indiya na zuba jari

Ma'aikatan sufurin jiragen sama a Kenya za su tafi yajin aiki saboda shirin Indiya na zuba jari

Akwai yiwuwar yajin aikin ma'aikatan ya janyo gagarumin koma baya a harkokin zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa a Kenya.
Ma'aikatan sufurin jiragen sama a Kenya na buƙatar a dakatar da shirin zuba jari da gwamnatin ƙasar ta ke shirin yi da wani kamfani Indiya. /Hoto: Reuters 

Ƙungiyar ma'aikatan sufurin jiragen sama ta Kenya ta faɗa a ranar Litinin cewa ma'aikatan kamfanin sama na Kenya Airways da na hukumar kula da filayen jiragen sama a ƙasar za su fara yajin aiki daga ranar 19 ga watan Agusta.

Ƙungiyar dai na ɓukatar gwamnatin Kenya ta dakatar da shirin zuba jari daga wani kamfanin ƙasar Indiya, mai suna Adani Airport Holdings a babban filin jirgin saman ƙasar.

Akwai yiwuwar yajin aikin ma'aikatan ya janyo gagarumin koma baya a harkokin zirga-zirgar jiragen Kenya Airways da kuma ayyukan tashar jiragen sama ta Jomo Kenyatta da ke Nairobi wadda ke zama babbar cibiyar tafiye-tafiyen Afirka.

"Za mu iya janye shirin zuwa yajin aikin ne kawai idan har aka yi watsi da yarjejeniyar Adani Airport Holdings Limited gaba daya," in ji Moss Ndiema, shugaban kungiyar ma'aikatan sufurin jiragen sama ta Kenya.

A watan da ya gabata, hukumar kula da filayen jiragen sama ta Kenya ta ce shirin saka hannun jari na kamfanin Adani ya hada da hanyar tashin jirgi na biyu a filin jirgin Jomo Kenyatta na ƙasa da ƙasa.

Reuters