A yau Litinin ne, matatar mai ta Warri ta koma aiki makonni bayan kamfanin NNPCL ya sake fara aikin tace gangar danyen fetur 60,000 a kowace rana a matatar Port Harcourt. / Hoto: AP

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana matukar farin cikinsa da sake bude matatar man fetur ta Warri da Kamfanin Mai na Ƙasar NNPCL ya yi a ranar Litinin, inda ya bayyana hakan a matsayin wata gagarumar nasara a shekarar 2024 da ta ƙara wa ‘yan Nijeriya samun fatan alheri a gwamnatinsa.

A yau Litinin ne, matatar mai ta Warri ta koma aiki makonni bayan kamfanin NNPCL ya sake fara aikin tace gangar danyen fetur 60,000 a kowace rana a matatar Port Harcourt a watan Nuwamba.

Gwamnatin Nijeriya ta ce a ranar Litinin ta koma wasu ayyuka a matatar mai ta Warri bayan rufe ta na tsawon kusan shekaru goma.

A saƙon da ya fitar bayan sanar da sake bude matatar, Shugaba Tinubu cikin kwarin gwiwa ya ce matatar mai ta Warri wadda yanzu tana aiki da kashi 60% cikin 100, na ba da tabbacin cewa shirin gwamnatinsa na ingancin makamashi da tsaro gaba daya suna kan hanya.

Ya kuma yaba wa mahukuntan NNPC karkashin jagorancin Mele Kyari kan yadda suke aiki tukuru domin dawo da martabar Nijeriya a matsayin babbar kasa mai arzikin man fetur.

"Gyaran matatar mai ta Warri a yau ya sanya ni farin ciki ni da 'yan Nijeriya. Wannan abu zai kara karfafa fata da bai wa 'yan Nijeriya ƙwarin gwiwa na samun makoma mai kyau na alkawuran da muka yi musu.

"Wannan ci gaban wata babbar hanya ce ta rufe wannan shekara bayan wannan aikin da aka yi musamman idan aka hada da gyara tsohuwar matatar Port Harcourt da aka yi duk cikin shekarar nan.

"Na yi farin ciki da cewa kamfanin NNPCL yana aiwatar da umarnina na maido da dukkan matatun manmu guda hudu zuwa kyakkyawan yanayin aiki.

Tun da fari gwamnati ta yi alkawarin farfado da matatun man da suka lalace saboda rashin kulawa.

Mele Kyari, shugaban kamfanin man fetur na kasa NNPC, a lokacin da ya ziyarci cibiyar tare da jami’an gwamnati, da da ‘yan jarida ya ce, “Wannan kamfanin yana aiki a yanzu. Ba mu kammala shi 100 bisa 100 ba.

Matatar man mai tace yawan ganga 125,000 a kowace rana - wacce aka rufe ta a shekarar 2015 bayan da ta lalace - a yanzu kashi 60% nata yana aiki da, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya sanya wa hannu.

TRT Afrika