Sabon tsarin CBN ya ce a halin yanzu za a iya hada-hadar kudin da ba su wuce dala dubu goma rana ba. Hoto/Reuters

Shugabannin kasuwar musayar kudade ta WAPA da ke jihar Kano a Nijeriya sun ce sun rufe kasuwar ta tsawon wasu awanni a ranar Laraba sakamakon kiraye-kirayen da hukumomi suka yi musu a kan tashin gwauron zabin da dala ke yi.

A wata kebantacciyar hira da TRT Afrika ta yi da Sakataren Kasuwar Canjin Kudi ta WAPA a Kano, Haruna Musa Halo, a daidai lokacin da farashin sayen dala daya ya kai naira 1,500, ya ce hukumar tsaro ta DSS da kuma hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki Nijeriya zagon kasa, EFCC ne suka yi ta kiransu a waya don son jin me ya jawo wannan yanayi da ake ciki.

Sakataren ya ce karfe 6 na yammacin Laraba daidai agogon Nijeriya dokar rufe kasuwar za ta fara aiki, kuma ba a kasuwar WAPA kawai matakin zai yi aiki ba, zai yi aiki ne a duk wani waje da ake musayar kuɗaɗe a Jihar kano har sai bayan 12 na ranar gobe Alhamis sannan za a buɗe kasuwannin su ga yadda abin zai kasance.

“Ba umarnin rufe kasuwar aka ba mu ba, mu muka ɗau wannan matakin saboda muna ganin kamar zai haifar da ɗa mai ido don muma ba jin daɗin hauhawar muke ba, ba ta da alkhairi kwata-kwata baya take ta mayar da mu,” a cewar Sakataren na WAPA.

“Sun kira mu ne saboada su abin da suke so shi ne idan muna da wata hanya da za mu iya bi a dakatar da hauhawar tata. Amma ita CBN ba su neme mu ba.”

Ya kuma bayyana fatan cewa wani abu zai iya sauyawa daga yau Laraba har zuwa a shiga hutun ƙarshen mako zuwa Litinin.

“Duk da cewa mun samu haɗin kan DSS da EFCC kan matakin rufewar, to dole sai mun rubuta a rubuce mun ba su.”

An wayi garin Laraba farashin dala ɗaya ya kai 1,500 ko ma fiye da haka a kasuwannin musayar kuɗaɗe a cikin ƙasar, har ma da wasu ƙasashen da ƴan Nijeriya ke da yawa a can kamar Amurka da Birtaniya da Turkiyya da China da Saudiyya da sauran su.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta koke-koke kan hauhawar farashin kayayyaki da tashin gwauron zabin da kusan komai ya yi a ƙasar.

‘Yan kasuwar musayar kuɗaɗen ta Kano sun aminta da matakin rufe kasuwannin kamar yadda shugabannin suka tsara, in ji Sakataren WAPA, “matuƙar ba zai cutar da mu da su ba, za su bi doka.”

Me shugabannin WAPA ke son rufe kasuwar ya cimma?

“Abin da muke son cimma da daukar wannan mataki shi ne dala ta daina tsada, ta daina yin gaba. Muna so ko ba a samu wata ƙwaƙƙwarar mafita ba to ta daina yin gaba saboda ci gaba da tsadar wahala ne,” in ji Haruna Musa Halo.

Ya ce da a ce gwamnati za ta tuntube su don neman mafita da suna da tarin shawarwarin da za su bayar wadanda za su taimaka.

“Amma har yanzu cikin ikon Allah ba mu samu hakan daga gwamnati ba tsakani da Allah.” Ya koka kan yadda su kansu tashin dalar yake matukar shafar kasuwancinsu

TRT Afrika