Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sayar wa bankuna 26 a ƙasar waɗanda suka cika ƙa'idoji da matakai dala miliyan 876 a kan farashin Naira 1495 kan kowace dala a tsarin ''Retail Dutch Action.''
A wata takardar sanarwar da Babban Bankin ya fitar a ranar Laraba ya ce matakin zai taimaka wajen farfado da faduwar darajar Naira a Nijeriya.
Kazalika matakin CBN na zuwa ne a daidai lokacin da Naira ke cigaba da fuskantar matsin lamba sakamakon yadda masu zuwa yawon bude ido da ’yan kasuwa da ke shigo da kayayyaki daga ƙetare zuwa Nijeriya wadda ke yawan dogaro da kayayyakin kasashen waje.
''An samu Jimillar tayin neman dala biliyan 1.18 daga bankuna 32 waɗanda suke da lasisi,'' in ji sanarwar.
''Daga cikin kudaɗen an sayar wa bankuna 26 wadanda suka cancanta dala miliyan 876.26, yayin da aka hana bankuna shida dala miliyan 313.69 saboda gaza cika ka'idoji da suka yi.''
CNB ya bayyana cewa, ''bankuna hudu sun gaza cika ƙa'idojin samun kudin har zuwa lokacin da ya ƙayyade, yayin da sauran bankuna biyun kuma suka gaza bin tsarin da ya kamata a bi wajen samun kuɗin.''
Kazalika, babban bankin ya ce, ya ''soke tayin duk wani banki da ya yi mafani da takardar neman ƙuɗin na Fom Q da A da kuma M.''
CBN ya sayar wa bankunan dala akan farashin Naira 1495 a tsarin ''Retail Dutch Action.''
Haka kuma CBN ya bayyana cewa a ranar Alhamis 8 ga watan Agusta zai wallafa sunayen bankunan da suka cancanta a shafinsa na intanet domin sahihanci.
Nijeriya dai na fama da karancin kudaɗen kasashen waje musamman dala saboda raguwar hako fetur, wanda shi ne abin da kasar ta fi fitarwa zuwa kasashen waje inda take samun kusan kashin 90 cikin 100 na dalar da ke shiga kasar.
Shugaba Bola Tinubu dai ya sha alwashin bunkasa kudaɗen waje da ke shigowa Nijeriya ta hanyar jawo sabbin masu zuba jari, da habaka hako mai da kuma gyara kasuwar canji ƙasar.