Babban bankin Nijeriyya. /Hoto: shafin Twitter na CBN

Babban Bankin Najeriya CBN ya ce ya kashe Naira biliyan 125.3 a kan sha’anin tsaron kasar a bara, adadin da ya kusan ninkawa sau uku idan aka kwatanta da kudaden da ya kashe a shekarun baya-bayan nan.

Jaridar Kasuwanci ta Business Day da ake wallafawa a kasar ta ambato wasu alkaluma da nuna cewa CBN ya kashe Naira biliyan 507 kan harkokin tsaron kasa da bangaren soji da kuma sha’anin tsaron jihohi da dai saurans a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2022.

CBN ya ce kudaden da aka kashe sun hada da wadanda aka yi amfani da su wajen aiwatar da ayyukan shiga tsakani da suka shafi sha'anin tsaron kasa na gwamnatin tarraya da na jihohi, da kuma ayyukan inganta fannin kudin kasar idan bukatar hakan ya taso.

“Dukka kudaden da aka biya na ayyukan shiga tsakani a madadin gwamnatin tarayya da bankin ya yi an kashe su ne kamar yadda aka bukace su. Sai dai an ware su a matsayin rance sai bayan watanni 12 idan ba a kai ga mayar da su gwamnatin tarayyar ba sai su shiga cikin lissafin kudaden da aka kashe,'' a cewar bayanan da jaridar ta tattaro daga CBN.

Karin wasu bayanai sun yi nuni da cewa CBN ya kashe Naira biliyan 45.4 a shekarar 2021 sai kuma Naira biliyan 28.6 a 2020, a 2019 an kashe Naira biliyan 21.4, a 2018 an kashe Naira biliyan 44.9 a shekarar 2017 an kashe Naira biliyan 19.3 sannan a 2016 bankin ya kashe Naira biliyan 38.5 a sha'anin tsaron kasa.

Masana sun bayyana cewa ayyukan ta'addanci da sauran nau'o'in rashin tsaro a Nijeriyya sun ci gaba da karuwa daga shekaru goma zuwa yanzu ba tare da samun wani sauki ba, duk kuwa da biliyoyin kudaden da gwamnatin kasar ke ikirarin kashewa kan lamuran tsaro a duk shekara.

Rahotanni da dama sun nuna cewa Nijeriya na daya daga cikin kasashen da ke ware makudan kudade a bangaren tsaro a nahiyar Afirka, amma tsawon shekaru da dama, hakan bai kai ga samun ingantaccen tsaro ba.

Wani rahoto na shekarar 2019 da Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar mai taken ‘Auna Tasirin Tattalin Arzikin Ta’addanci a Afirka', ya bayyana tasirin ayyukan ta’addanci a kasashen Afirka, inda Najeriya ta kasance a kan gaba wajen asarar rayuka da tattalin arzikinta.

A cewar rahoton, Nijeriya ta yi asarar dala miliyan 40.828, a kan mutanen da suka mutu da kuma wadanda jikkata a hare-haren ta'addanci, sannan an yi kiyasin asarar dala miliyan 598.8 a kadarori da aka barnata.

Kazalika rahoton ya bayyana cewa Nijeriya ce kan gaba wajen kashe makuden kudaden kan tsaro da dala biliyan 78.43 a shekarar 2017, sai Morocco da ke biye da ita inda ta kashe dala biliyan 42.52.

A shekarar 2020 kadai, Nijeriya ta yi asarar dala biliyan 40.6 a bangaren zuba hannayen jarinta sakamakon rashin tsaro, kamar yadda rahoton kungiyar Global Terrorism Index ta bayyana.

Baya ga asarar rayuka da dukiyoyi, tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da fuskantar koma-baya sakamakon yadda tabarbarewar rashin tsaro ke hana masu zuba hannayen-jari zuwa kasar.

TRT Afrika