Bankin Ci-gaban Afirka (AfDB) zai bai wa wasu jihohin Nijeriya tallafin dala miliyan 540 domin bunƙasa ayyukan noma.
Bankin zai ware kuɗaɗen ne ga jihohi bakwai domin soma shiri na musamman kan bunƙasa fannin noma na yankin wato ''Agro-Industrial Processing Zones'' (SAPZs) kamar yadda mai magana da yawun bankin na AfDB Banji Oyelaran-Oyeyinka ya bayyana a cikin wata sanarwa.
Oyelaran-Oyeyinka ya ƙara da cewa shirin na SAPZ zai mayar da hankali a kan manoman da ke yankunan karkara.
Kazalika ya bayyana cewa maƙasudin bankin na AfDB shi ne tallafa wa hada-hadar ayyukan noma da ɗorewar masana'antu a Nijeriya.
Oyelaran-Oyeyinka ya yi kari da cewa tallafin zai taimaka wa ƙasar wajen yaƙi da matsalar ƙarancin abinci.
TRT Afrika