Mahmoud na takara don maye gurbin dan aksar Chadi Moussa Faki Mahamat a matsayin Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka na gaba. Hoto: Mahmoud/X

Daga Nuri Aden

Ministan Harkokin Waje mafi daɗewa a kan kujerar a ƙasar Djibouti, Mahmoud Ali Youssouf, na tunkarar muhimman matakai guda biyu a yayin da yake gina rayuwa da aiki masu ƙayatarwa.

Youssouf, ƙwararre a fannin diflomasiyya da shugabanci a tsawon fiye da shekaru 30, ya cika shekaru 60 a duniya a ranar 9 ga Fabrairu, wanda ya zo daidai da lokacin da yake ƙoƙarin maye gurbin ɗan ƙasar Chadi, Moussa Faki Mahamat a matsayin shugaban Hukumar Tarayyar Afirka.

Kyakkyawan aikin diflomasiyya da shugabanci, da ma jajircewa wajen haɓakar Afirka ne suka sanya Youssouf shiga takarar da zai fafata da wasu manyan mutane biyu - Raila Amolo Odinga na Kenya da Richard Randriamndrato na Madagascar. Kuma shi ne mafi ƙanƙantar shekaru a tsakanin 'yan takarar uku.

A yayin da wanda zai maye gurbin Mahamat don yin shugabancin shekaru huɗu ya dogara kan batutuwa daban-daban, zai zama cuɗe-ni-in-cuɗe ka ga Gabashin Afirka a yayin da yake lokacinta ne na karɓar ragamar shugabancin nahiyar.

Ja ya faɗo ja ya ɗauka

Youssouf ya samu ƙwarewa inda yake da kyawawan manufofi da hangen nesa, wanda gamayyarsu za ta ba shi damar kawo ci gaba a nahiyar Afirka a nan gaba.

Wannan gangami ne da ya samu karɓuwa ga dukkan masu amanna cewar Djibouti na da duk abin da ake buƙata domin lashe zaɓen a lokacin da shugabannin Afirka za su taru a babban birnin Ethiopia, Addis Ababa, a wata mai zuwa don zaɓen ɗan takarar da suke so.

Duba da yadda ya sadaukar da rabin rayuwarsa ga ayyukan diflomasiyya da shugabanci, Youssouf na da ƙarfin faɗa a ji a yankinsa da ma duniya baki ɗaya.

Ya shafe shekaru da dama wajen zurfafa alaƙa a nahiyar Afirka, yana haɓaka zaman lafiya da haɗin-kai, tare da gina al'umma da neman mafita.

Mahamoud Ali Youssouf ya yi jawabi ga Zauren Majalisar Dinkin Duniya a 2024. Hoto: UN

A matsayinsa na jami'in diflomasiyya, ƙoƙarin Youssouf da ƙwarewarsa sun fito sosai a yankin da ma ƙasashen duniya.

Ya yi aiki a matsayin shugaban Majalisar Ministocin Ƙasashen Larabawa na tsawon shekaru 10. A shekarar 2012, ya shugabanci Majalisar Ministocin Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmi (OIC).

Jakadan Djibouti a Saudiyya, Dya-Eddine Bamakhrama, na da yaƙinin cewa ƙasashe mambobin OIC za su goyi bayan Youssouf a zaɓen.

A matsayin babban jami'i a Ƙungiyar Ci-gaban Ƙasashe da Haɗin Kan gwamnatoci (IGAD), Youssouf ya nuna zai iya haɗe kan yankin da samar da zaman lafiya.

Ya ci gaba da neman a zauna lafiya da kwantar da hankali a nahiyar, wanda hakan ya sa shi zama daya daga cikin waɗanda aka fi yarda da su a Gabashin Afirka.

"Na yi alƙawarin zan kare buƙatun Afirka a hukumomin ƙasa da ƙasa da ƙarfafa rawar da take takawa a hukumomin. Dole ne Afirka ta daidaita kanta a matsayin mai taka babbar rawa a tattaunawar samar da manufofin juya duniya, tare a haɓaka tattalin arzikinta da buƙatunta"

Mahmoud Ali Youssouf

Ƙwararre da ke jin harsuna da dama

Ɗaya daga cikin ɗabi'un da suke ƙara nuna cancantar Youssouf shi ne ƙoƙarinsa na iya sadarwa da manyan harsunan Afirka.

Yana jin Turancin Ingilishi, Larabci, Faransanci, Somaliyanci da Afar, kuma an san shi da ƙoƙarin nuna rashin bambanci tsakanin al'adu da harsuna, babbar ƙwarewa da ke kai wa ga ƙulla alaƙa da masu magana da harsunan Faransanci, Turanci da Larabci a nahiyar.

Youssouf ya nuna ƙwarewarsa a matsayin wanda ya iya harsuna da dama a lokacin da aka yi muhawarar "Mjadala Afrika", inda ya fafata da sauran 'yan takara Odinga da Randriamandrato.

Ya kuma haɓaka faɗaɗa harsuna a ma'aikatar Harkokin Wajen Djibouti, inda ya jagoranci ganin an koyar da ma'aikatu harsuna irin su Chinanci, Amharic da Rashanci.

Wannan mayar da hankali ga haɓaka koyon harsuna ya inganta ƙarfin diflomasiyyar Djibouti tare da bayyana yadda amince da ƙarfin sadarwa don ƙarfafa haɗin-kai da aiki tare.

Matakin warware rikice-rikice

An sake ganin ƙarfin ƙwarewar diflomasiyyar Youssouf a yadda ya taka rawa wajen shiryawa da karɓar baƙuncin Taron Cikin Sulhun Gida na Somalia a 2008.

Wannan babban taro mai muhimmanci ya tattara ɓangarori daban-daban na Somalia, wanda ke nuna kaifin basirar jami'in diflomasiyyar kuma minista wajen warware rikice-rikice da kuma ƙudurinsa na warware manyan matsaloli.

A shekarunsa na farko, daga 1997 zuwa 2001, Youssouf ya yi aiki a matsayin jakadan ƙasar a Masar kuma wakilin dindindin a Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa.

Ƙwarewarsa ta kuma isa ga manyan ƙasashe a duniyar Larabawa, inda ya yi aiki a matsayin Jakadan da ba na yankin ba zuwa Sudan, Lebanon, Syria, da Turkiyya.

Waɗannan manyan rawa da ya taka sun faɗaɗa fagen diflomasiyyarsa da ƙara girman amincewa da shi a matsayin jami'in diflomasiyya ƙwararre da ya san aikinsa.

Ƙwarewar da Youssouf ya tattara za su taimaka wajen shirya yadda 'yan Afirka da ke ƙasashen waje sun amfanar da nahiyar sosai.

"'Yan Afirka da ke ƙasashen wajen nahiyar na muhimmancin wajen samun cigaban Afirka. Zan yi aiki tuƙuru don ƙarfafa rawarsu a nahiyar," in ji shi.

Ƙoƙari a cikin gida

A Djibouti, shugabancin Youssouf ya faɗaɗu har zuwa sama da matsayinsa na ministan harkokin waje mamban jam'iyya mai mulki ne, kuma mamban majalisar zartarwa a shekaru 10 da suka gabata.

A 2012, shugaban ƙasar Djibouti, Omar Guellah ya ba shi lambar girma mafi matsayi a ƙasar ta - Babban Kwamandan Babban Tauraron Djbouti.

A matsayin mamban Majalisar Dokoki, ya jagoranci samar da ayyuka irin su ƙauyen Sourat, mai nisan kilomita 5 arewa da Tadjourah. Ƙauyen na bayar da gidaje kyauta, ruwan sha da kayan more rayuwa da dama, ciki har da makaranta da masallaci.

A baya bayan nan ƙauyen ya samar da ɗaliban da suka tafi babbar makaranta a Tadjourah.

Shirya makoma mai kyau

"Matasan Afirka ne makomar nahiyar a nan gaba. Na yi alƙawarin tallafa wa ilimin Afirka, samar da ayyukan yi da ɗabbaƙa manufofin koyon sana'o'i don cim ma muradunsu. Yaƙi da rashin ayyukan yi zai zama a kan gaba, za a samar da ayyukan yi da taimaka wa sana'o'i," in ji Youssouf.

Ya kuma ƙuduri niyyar kare dimokuraɗiyya da tabbatar da shugabanci na gari.

Youssouf ya ƙara da cewa "Girmama tsarin dimokuraɗiyya da kare hakkokin 'yan ƙasa na da muhimmanci ga kwanciyar hankali da halascin gwamnatocin Afirka."

A yayin da ake jiran zuwan watan Fabrairu don jefa ƙuri'a, magoya bayan Youssouf a nahiyar na tallata ɗan takarar da yake son ganin an tabbatar da samun Afirka mai haɗin-kai da ci-gaba.

TRT Afrika