Shugabannin kasashen Yammacin Afirka za su gana a Abuja, babban birnin Nijeriya don tattaunawa kan juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar.
Za a gudanar da taron ne ranar Lahadi, a cewar shugaban Nijeriya kuma shugaban kungiyar raya tattalin arzikin Yammacin Afirka ECOWAS, Bola Tinubu, a sanarwar da ya fitar ranar Juma'a.
"Ecowas da kasashen duniya za su yi duk abin da ya dace domin kare dimokuradiyya da tabbatar da cewa mulkin dimokuradiyya ya zauna da kafafunsa a wannan yankin," in ji Tinubu.
Sojojin da suka yi juyin mulkin sun yi gargadi cewa za a fuskanci zubar da jini idan kasashen waje suka tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar, kamar yadda suka fada a sanarwar da suka gabatar ta gidan talabijin.
Sanarwar tasu, wadda suka yi kwana biyu bayan sun tsare shugaban kasar Mohamed Bazoum, ta yi gargadi game da "sakamakon da zai biyo baya idan kasashen waje suka sanya baki ta hanyar amfani da karfin soji."
A gefe guda, Tarayyar Turai ta yi barazanar janye tallafin da take bai wa Jamhuriyar Nijar.
"Duk wata karfa-karfa ta karya kundin tsarin mulki za ta yi tasiri game da hadin kai tsakanin Tarayyar Turai da Nijar, ciki har da janye tallafin kudi da muke bayarwa nan take," a cewar sanarwar Tarayyar Turai.