Tinubu ya ce "ba za mu yi kasa a gwiwa ba game da matsayarmu ta kare kundin tsarin dokoki." Hoto: OTHERS

Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya yi Allah-wadai da abin da ya kira yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar tare da kira ga sojoji "maciya amanar kasa" da su dakatar da aniyar ta su ba tare da bata lokaci ba.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ma ta bayyana damuwarta kan yanayin siyasar da ake ciki a Nijar bayan da sojoji suka toshe fadar shugaban kasa a Niamey, babban birnin kasar.

''Shugabancin ECOWAS ba zai lamunci duk wani tarnaki da zai shafi tafiyar da sha'anin mulki cikin doka ba a Nijar ko wani fanni na Afirka ta Yamma," a cewar wata sanarwa da shugaban Nijeriya Bola Tinubu wanda shi ne shugaban ECOWAS, ya fitar.

"Ya kamata masu hannu a wannan lamari a Jamhuriyar Nijar su fahimci cewa shugabancin ECOWAS da duk masu goyon bayan dimokuradiyya a fadin duniya ba za su lamunci duk abin da zai jawo rusa gwamnatin dimokudariyya da aka kafa a kasar ba."

''Ina so na ce muna bin diddigi da sa ido kan duk abin da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar kuma za mu yi duk abin da ya kamata don tabbatar da cewa dimokuradiyya ta kafu ta bunkasa ta kuma yadu a yankin," Tinubu ya kara da cewa.

Matsayarmu

Ya jaddada "matsayar shugabannin yankinmu cewa ba za mu yi kasa a gwiwa ba game da matsayarmu ta kare kundin tsarin dokoki," ya fada.

Tun da fari, fadar shugaban kasar Nijar ta ce wasu sojojin fadar shugaban kasar sun tayar da yamutsi a ranar Laraba, kuma rundunar sojin kasar a shirye take ta kai musu hari idan ba su shiga taitayinsu ba.

Shugaba Mohamed Bazoum da iyalansa na nan lafiya, kamar yadda sanarwar ta kara da cewa. Wannan lamari na zuwa ne bayan da majiyoyin tsaro suka ce sojojin fadar shugaban kasar na tsare da Shugaba Bazoum a cikin fadar shugaban kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Zaben Bazoum da aka yi a shekarar 2021 shi ne na farko da aka mika mulki daga farar hula zuwa wata farar hular, a kasar da sau hudu tana ganin juyin mulki tun bayan samun 'yancin kanta daga Faransa a 1960.

Kwanaki kadan kafin rantsar da Bazoum ma an yi yunkurin juyin mulki a kasar.

TRT Afrika