Kungiyar Tarayyar Afirka ta umarci sojojin Nijar su "koma bariki kuma su dawo da gwamnatin tsarin mulki" nan da kwana 15 kwanaki kadan bayan sun yi juyin mulki a kasar.
Kwamitin Tsaro da Zaman Lafiya na Tarayyar Afirka ya "bukaci jami'an soji su yi gaggawar komawa bariki ba tare da wani sharadi ba sannan su dawo da gwamnatin tsarin mulki nan da kwana 15", a cewar sanarwar da ya fitar ranar Juma'a.
Sojojin suna tsare da Shugaba Mohamed Bazoum a gidansa da ke fadar shugaban kasa tun ranar Laraba sannan suka bayyana cewa sun kifar da gwamnatinsa.
Kasashen duniya suna ci gaba da matsa lamba ga sojoji don su dawo da tafarkin dimokuradiyya.
Wani labarin mai alaka: Bayanai kan shugaban juyin mulkin Nijar Abdourahamane Tchiani
Sai dai Janar Abdourahamane Tchiani da ya jagoranci juyin mulki a kasar ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa sannan ya yi gargadin cewa za a zubar da jini idan wata kasar waje ta tsoma baki a sha'anin cikin gida na Nijar.
Ranar Asabar Tarayyar Turai ta ce ba za ta amince da sojojin ba sannan ta dakatar da tallafin da take bai wa kasar nan take.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce kasarsa za ta bai wa Mohamed Bazoum taimako "mara iyaka" sannan ya "jaddada muhimmancin ci gaba da mulkinsa" a kasar.
Mr Blinken ya bayyana haka ne a tattaunawar da ya yi ta wayar tarho da Mohamed Bazoum, a cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar ranar Juma'a.
"Ya jinjina wa Bazoum a kan rawar da ya taka wajen tabbatar da tsaro a Nijar da kuma yankin Yammacin Afirka," in ji sanarwar da kakakin ma'aikatar wajen Amurka Matthew Miller ya fitar.