Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce tana neman Rukayya Saadina Dantata ruwa-a-jallo.
A wata sanarwar da ta fitar ta shafinta na X ranar Alhamis, rundunar ta ce ofishin mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda da ke bincike kan laifuka ne yake neman Rukayya.
Sanarwar ta kara da cewa ana nemanta ne kan zargin hadin baki wajen aikata laifuka da cin-amana da damfara da barazanar kisa.
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa Rukayya, mai shekara 35, ‘yar asalin jihar Kano ce duk da cewa gidan da aka santa da zama yana unuguwar Ikeja ne a jihar Legas.
Ta kara da cewa za a bai wa duk wanda ya samar da bayanai kan yadda za a iya kama ta tukici mai gwabi.
TRT Afrika