Rundunar ƴan sandan jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta ce ta kama wata mata da ake zarginta da kashe wani mutum ɗan Jihar Bauchi.
A sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Juma’a mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta SP Abdullahi Kiyawa, ta ce ta kama matar ne ‘yar shekara 24 mai suna Hafsat Surajo bayan ƙorafin da ƴan’uwan mamacin suka kai mata.
Labarin rasuwar matashin ta karaɗe shafukan sada zumunta a Nijeriya, inda ake ta yaɗa hotonsa da na wacce ake zargi da kashe shi da kuma wani bidiyo na hirar da aka yi da mahaifinsa yana bayyana yadda abin ya faru.
Batun ya ɗauki hankali sosai inda ya jawo ce-ce-ku-ce da Allah wadai daga faɗin ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa wacce ake zargi da kisan ita da mijinta iyayen gidan marigayin ne wanda yake zaune tare da su a Kano.
“A ranar Alhamis 21 ga watan Disamba da misalin ƙarfe 7 na safe ne wani mutumin Bauchi Hafizu Salisu ya kawo mana ƙara cewa wani Dayyabu Abdullahi mazaunin Unguwa Uku a Kano ya kira su ya sanar da su rasuwar ɗan’uwansu Nafi’u Hafiz mai shekara 38.
“Ya kuma ce su je su ɗauki gawarsa don yi masa jana’iza. A lokacin da suka je ne sai suka gano raunuka a sassan jikinsa da ke nuna alamun wuƙa aka caccaka masa,” in ji sanarwar ƴan sandan.
Rundunar ta ce ba tare da ɓata lokaci ba sai Kwamishinan Ƴan sanda Mohammed Usaini Gumel ya ba da izinin aika tawaga zuwa gidan da lamarin ya faru don fara bincike.
“Da zuwan tawagar ƴan sanda wajen sai suka ɗauki gawar suka dangana Asibitin Koyarwa na Aminu Kano inda aka tabbatar da mutuwar.
“Bincike na gaba ne ya sa aka kai ga kama Hafsat Suraji mai shekara 24, wadda matar aure ce da ke gidan da mamacin ke zaune.
Sanarwar ƴan sandan ta ce binciken da aka ci gaba da yi ne ya kai ga Hafsat ta amsa laifin cewa ita kadai ta kashe shi ta hanyar “caccaka masa wuƙa a sassan jikinsa daban-daban” a lokacin da yake ƙoƙarin hana ta yunƙurin kashe kanta da take yi.
Kazalika ƴan sanda sun kama mijinta mai suna Dayyabu Abdullahi mai shekara 38 da shi ma yake zaune a gidan da kuma maigadin gidan Malam Adamu mai shekara 65, "waɗanda su ne suka taimaka wajen haɗa gawar da ɓoye aika-aikar.”
"Binciken ya kuma gano wuƙar da ake zargin da ita aka yi kisan da jini duk a jikinta."
'Yan sanda sun ce za a gurfanar da wacce ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.