Jama’a da dama a Nijeriya sun wayi gari ba zato ba tsammani da karin farashin man fetur inda wasu gidajen mai a Abuja babban birnin kasar suke sayar da fetur din kan naira 617.
Hakan na nufin an samu karin naira 77 kan farashin da ake sayar da shi na 540 a wasu wurare.
Sai dai shugaban kamfanin mai na Nijeriya NNPCL, Mele Kyari, ya dora alhakin karin farashin kan yanayin kasuwa.
Ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai bayan ya gana da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.
Mista Kyari ya jaddada cewa yanayin kasuwa ne ya haifar da tashin farashin ba karancin fetur ba ne.
Tuni wasu gidajen mai da ke kwaryar birnin Abuja suka kara farashin litar mai a jikin injin din sayar da mai da kuma allon da ke dauke da farashi na gidan mai.
Karin farashin na zuwa ne kasa da wata biyu bayan farashin man ya karu daga 195 zuwa 540.
Dama a kwanakin baya an ta rade-radin cewa za a yi karin farashin na fetur, sai dai kungiyar dillalan man fetur din kasar ta fito ta nesantar da kanta daga hakan.
Ga dai yadda wasu ‘yan kasar ke korafi kan kadin kudin man:
@FemiSobodu a shafin Twitter yake cewa mutane da dama za su wahala sakamakon fetur ya koma 617. A cewarsa, motoci za su fi hutawa a gida ba tare da fita ba sai ta kama dole.
Da alama mazaunin birnin Legas ne domin ya bayyana cewa za a samu ragowar cunkoso a titunan Legas sakamakon ba kowa bane zai iya kashe dubu 25 zuwa 35 a mako domin sayen fetur kadai ba.
Shi ma @aojempire a shafin Twitter wata magana ya yi mai kama da barkwanci inda ya ce yanzu sai dai mutum ya je ya sayi keke sakamakon karin farashin.
Sai kuma @iam_doctormayor shi kuma cewa ya yi man fetur ya koma naira 617 kan kowace lita sai dala kuma tana kaiwa 835.
Karin farashin man na zuwa ne a daidai lokacin da farashin dala ke ta hauhawa kan naira tun bayan karya darajar nairar a watan Yuni.
Tashin farashin dalar da kuma karin farashin na man fetur sun kara jawo tsadar rayuwa.
Domin kuwa ko a wannan makon sai da hukumar kididdiga ta Nijeriya ta fitar da sanarwa kan kara samun hauhawar farashi a kasar inda farashin ya karu daga maki 22.41 zuwa zuwa 22.79 inda aka samu karin 0.38.