A ranar Talata, 'yan Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu su 248 suka jefa kuri'ar amincewa da a rufe ofishi jakadanci, da dakatar da huldar jakadanci da kasar Isra'ila.
'Yan majalisu 91 ne sun jefa kuri'ar kin amincewa da kudurin na yanke hulda tsakanin kasashen biyu.
Afirka ta Kudu ta kasance kan-gaba wajen nuna goyon baya ga al'ummar Falasdinu tun bayan hare-haren da Isra'ila take ta fara kai wa kan Gaza babu kakkautawa.
Karuwar adadin mutanen da suka hallaka
Akalla Falasdinawa 13,300 suka rasa rayukansu sakamakon harin jiragen yakin Isra'ila, tun ranar 7 ga watan Nuwamba.
Tun ranar 16 ga watan Nuwamba ne jam'iyyar Economic Freedom Fighters (EFF), ta bakin shugabanta Julius Malema, ta gabatar da kudurin katse alaka tsakanin Afirka ta Kudu da Isra'ila.
Jami'yya mai mulki, African National Congress (ANC) tana cikin jam'iyyun da suka goyi bayan rufe ofishin jakadancin Isra'ila a Afirka ta Kudu.
Baya ga yin kiran yanke alakar diflomasiyya a kudurin, jam'iyyar EFF ta yi Allah-wadai da abin da ta kira "kisan mata da yara a Gaza, da harin bam kan asibitoci."
'Kowa ya sani'
A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata bayan kuri'ar majalisar, jam'iyyar EFF ta ce, "Isra'ila ta sani cewa, kowace cibiya a Afirka ta Kudu, ko ta kasuwanci ko ta ilimi, dole ta san cewa Afirka ta Kudu ta yanke alakar diflomasiyya da Isra'ila, kuma ya kamata su bi kudurin ceton rayuka."
Afirka ta Kudu tana yawan kwatanta yanayin Faladinawa da irin fafutukar da kasar ta yi karkashin mulkin nuna wariyar launin fata, tsakanin 1948 da 1994.