'Yan Ghana na jiran sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka yi kankankan

'Yan Ghana na jiran sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka yi kankankan

Ana sa ran samun sakamakon farko na zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar zuwa ranar Talata.
Zuwa ranar Talata ake sa ran fara samun sakamakon zaɓen na shugaban ƙasa da aka gudanar ranar Talata. /Hoto:Reuters

'Yan Ghana na zaman jiran sakamakon shugaban ƙasa da aka gudanar ranar Asabar, inda 'yan takara dake kan gaba Mataimakin Shugaban Ƙasa Mahamudu Bawumia da Tsohon Shugaban Ƙasar John Mahama suke kusan kankankan a zaɓen.

An buɗe rumfunan zaɓe da ƙarfe 7 na safiyar ranar Asaba, sannan an rufe su da ƙarfe 5 na yamma, ana sa ran samun sakamakon zaɓen zuwa ranar Talata.

An kuma zaɓi 'yan majalisa a ƙuri'un da aka kaɗa ranar Asabar.

Kimanin mutane miliyan 18.7 suka yi rijista a ƙasar ta Yammmacin Afirka wacce take fama da matsin tattalin arziki, ɗaya daga cikin waɗanda suka fi muni a shekaru da dama.

Batun tattalin arzikin ya zama abin da ya fi mamaye yaƙin neman zaɓe, bayan ƙasar wacce ta yi fice wajen noman cocao da haƙar zinare ta faɗa cikin ƙangin bashi, da mummunan tashin farashin kayayyaki.

Dawowar Mahama?

Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna yiwuwar dawowar Mahama. Wani kamfanin bincike na cikin gida Global InfoAnalytics ya ce yana hasashen Mahama zai samu 52% na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da Bawumia zai biye masa da ƙuri'u 41.4%.

Bayan ya kaɗa ƙuri'a a garin Bale a arewacin ƙasar, Mahama ya yaba kan yadda ake gudanar da zaɓan cikin lumana, sannan ya bayyana ƙwaƙƙwaran fatan samun nasara.

Gwamnatin Ghana ta rufe duka iyakokin shiga ƙasar tun daga ranar Juma'a har zuwa ranar Lahadi, don tabbatar da ingancin zaɓen, a cewar Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida.

TRT Afrika